← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 53

Sashe 20

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *VOTE me on wattpad @Hajjac* *DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu Page *16* Zaune suke a cikin ajin wanda yawancin su duk matan aure ne da alama makarantar manya ce ta yak'i da jahilci. Gefe guda kuma INdo ce ta duk'ufa tana kallon wani littafi na alifun ba'un sai faman mamul-mamul takeyi da bakinta da alama sotake tasan su ta kuma gane su a haka wata dattijuwar malama ta shigo hannunta rik'e da littattafai idanta sanye da glass fari ta samu guri ta zauna. Bayan ta kammala biya musu littafin ahkdari ta zauna tana kuma yi musu bayani har tazo tana yi musu sharhin isra'i da mu'iraji tana basu labarin ire-iren matan da annabi (s.a.w) ya gani a cikin wuta tace. "Manzon Allah sallallawa'alaihiwa sallam yana cewa aure sunnah tane duk wanda baya son aure baya tare dani, baya da alkairi mutum ya zauna yayi ta kace nace da mutum musamman idan bata fuskar addini ba. Lokacin da ma'aikin Allah (s.a.w) ya dawo daga isra'i Nana Fateema da megidanta sayyadina Aliyu suka je gurinshi suka tarar dashi yana kuka suka tambaye shi menene yasanya shi wannan kukan, sai ma'aiki yace, yaga mata dayawa daga cikin al'umarsa anayi musu nau'i-nau'in azabobi kala-kala. Yace yaga wata mata an d'aureta d'auri irinna azaba da gashin kanta, _itace mace baliga wadda take barin gashin kanta a waje dan wasu sugani_ ya kuma ganin wata an zaro harshenta an nannad'eta dashi, yace _itace wadda take d'aga murya idan tanayiwa mijinta magana duk yadda taga dama, duk abinda zai mata ta kushe, ta dinga ganin be'iya yi mata komai_ wata kuma an tsananta d'aurin nononta, _itace wadda bata kula da shimfid'ar mijinta, bata bashi hakk'insa, ko tayi ta garashi dan taga yana buk'ata, sannan tana bin wasu mazan a waje_ wata kuma aka maida fuskarta ta alade jikinta na jaki. _itace wacce ta kassance munafuka, annamimiya me d'aukar magana takaiwa wannan taje can ta kunsa wata maganar_, ita ake yiwa wannan azabar.." Akwai nau'ika kala-kala daya sanar dasu wanda ya gani, anan gurin kowacce tasan abinda takeyi na rashin dai-dai dan haka sai kowacce taje ta gyara wanda takeyi kafin tilon ganyenta ya bushe ya fad'o ma'ana kafin ta koma ga wanda yayita. Akwai masu iyaye a raye babanki neko Mamanki kiyi musu biyayya akan abinda besa6awa shari'ar musulinci ba domin sa6a musu babban laifine a wajan Allah dama cikin rayuwar mutum gabaki d'aya, Allah yayi mana kyakyawan k'arshe.." Duka ajin suka amsa da amin sannan malamar ta fita, kasan cewar ajin duk matan aure ne mutum uku ne 'yan mata yasa INdo bata irin wannan haukan gashi basa kulasu ita kuma karatun ba wani shigarta yake yi ba saidai tana matuk'ar san tarihi domin jinta takeyi tamkar agabanta akeyi wasu abubuwan. K'arfe shabiyu da rabi aka tashesu gaba d'aya makarantar hijjab suke sawa kuma kala d'aya shine ya zama kamar uniform d'insu. Yau kwanakinta talatin da biyar da kawota makaranta babu abinda za'ace sai hamdala domin ta fara iya yin sallah sai dai sam kwakwalwarta bata d'aukar hadda, a gurin za'a biya tanaji amma kuma ya zauna a cikin kwakwalwar ne wahala. Tana fitowa itada k'awayen da tayi sababbi Zainab da Hadiza suna maganar littafin k'awa'idi sai ga me mashin d'inta wanda Abubakar ya samar mata yazo d'aukarta, shine yake kawota ya kuma dawo ya d'auketa duk sati Abubakar yake bashi kud'insa sukayi sallama ta hau suka tafi. Zama tayi a cikin d'aki suna hira da Inna ita kuma tafito da littattafan tana kallonsu taja tsaki tare da fad'in. "Wallahi Inna karatun nan badai wahala ba, ni wallahi duk makarantar ta iheni dacta Habubakar ya takura min." Ta k'arasa maganar tana turo baki tare da yatsina fuska, Inna tayi dariya tace. "Haba 'yar nan ki dubafa kigani zuwanki makarantar nan yanzu sallah bata wuce ki, sannan kina zaune a gida kina k'ok'arin yin alifun ba'un d'inki aini kam naji dad'i wallahi." "Ta6 lallai Inna, nifa ma wallahi inajin film zan higa dan wallahi dana fara Inna zaki ganni da narkekiyar mota wadda tafima ta dacta." Tafad'a cikin nuna son yin abinda tace, Inna tace, "Ahir d'inki da wannan sana'ar, yanzu keko cewa akayi kihiga ai bakyaje ba sabida ma tsarinku ba d'aya bane su sunfiki kud'i da karatu." "Toh Inna bakiga 'yar autah ba me sa bakin janbaki, yanzu kina nufin kice min itama tafini kud'i ko iya film d'in...?!" "Oh ni maryama nace bana son kiyi amma kuna dagewa." "Toh kiyi hakuri Inna dan yau anyi mana magana akan yiwa iyaye abinda basa so,malam Hansa'u tace me sa6awa iyaye idan ya mutu Allah ze k'onashi na denayi miki na fasa higa film d'in." Daga nan suka cigaba da hira duk ranar asabar, lahadi da litinin INdo na makaranta kuma alhamdulillahi duk sanda taje ta dawo akwai abinda zata d'an tuna musamman idan anayi musu k'arin haske akan littattafan. Shi kuma Abubakar idan yazo zai kuma sanar da ita abinda shima ya sani da haka INdo ta fara gane fari da bak'i sannan gashi Abubakar yana iya k'okarinsa wajan ganin yayi mata abubuwan zamani wayace kawai yak'i siya mata sabida yasan ba k'aramin d'auke mata hankali zatayi ba shi kuma yana son yaga ta samu wani abun a Cikin addininta. *Bayan shekara d'aya DA rabi* Waya ce kare ajikin kunnansa yana ta faman cike-ciken files sai faman murmushi yake yi sannan yace. "M twinnie na riga na gaya maka bazan samu damar zuwa gidan su wata Fateema ba gobe sabida akwai inda zani, nifa Fateema ma ta rainani wallahi ko ta d'auka kaine babba dan cewa tayi min wai wasan k'anin miji ta farayi dani." Sadeeq yayi dariya tare da cewa. "My sweet heart kenan ai tayi min dai-dai kasan wayayyen mutum gashi dama ta shiga college abin ya kuma k'aruwar mata Ina son Zarah M twinnie." Abubakar ya ta6e baki tare da cewa "Yh I see. Yanzu dai sai goben idan ka dawo ma had'u nima idan naje wajan babyna zan baka ku gaisa da ita." "Okey no problem Allah ya kaimu." Daga haka sukayi sallama kowa ya ajiye wayar yana kewar d'an uwansa, har tsawon shekarar nan Sadeeq besan Abubakar yana tare da INdo ba domin duk iya hutun da zaiyi a gida baya ta6a gigin nuna mishi dan ko wayarshi gallery d'insa password d'in a jiki bazaka ta6a tunanin ma cewa yana ajiye hoton mace a cikin wayarsa ko laptop ko wani gurin ba sabida iya taku da d'auke kai irin nasa. Washe gari Sadeeq ya dawo ranar raba dare sukayi suna hira. Da gari ya waye su Mama da sauran yaran gidan anata shirye-shiryan zuwan budurwar Yaya Habu domin a ranar yake son kawo INdo gidan su ganta itama taga 'yan gidansu. Sam Sadeeq besan lokacin da Abubakar ya fita ba, sai shiga d'akin yayi ya tarar k'amshin turarensa, wanka yayi ya kwanta tare da janyo waya ya k'ara Fateema lokacin sun fito daga lecture around 2:45pm. Abubakar kuwa yana shiga kauyan Sani yayi parking a k'ofar gidan su INdo,malam Hamza ya fito suka gaisa sannan yace. "Ai uwar tawa tace idan kazo kajirasu su dawo taje gidan kwalliya, nace yanzu ita kwalliyar ce bazata yi ba sai anje har cikin garin sumaila. Wai ai waccan tafi kyau nace toh Allah ya kyauta." Murmushi Abubakar yayi yana shafa k'eya tare da rissinawa yace. "Ai babu komai baba zanjira." Fita malam Hamza yayi yana ta shiwa Abubakar albarka yana jin aransa zai iya bashi duk abinda yake so indai yana dashi burinsa ma a yanzu kawai yaji Abubakar d'in yace yana son INdo amma yayi likimo ko ita 6eta6a furtawa kalmar ba sai 'yan gidan su daya dama da zancen Aisha budurwarsa. A 6angaran INdo kuwa tunda ta fara gane kyautatawar Abubakar da karamcinsa a gareta da irin yadda yake nuna kulawarsa gareta yasa ta mallaka masa zuciyarta gabaki d'aya, ta sallami salele jira kawai takeyi taji Abubakar yace yana sonta amma hakan ya gagara, gashi zuciyarta ta riga ta mutu akan sa dan ji takeyi tamkar ta fad'a mishi sai dai yanzu tana da kunya dan a makaranta ana gaya musu cewar kunya adon macene duk macen da batada kunyar gayawa namiji abu toh k'imarta zubewa take yi kuma bazai sota ba hakan yasa ko abu take so yanzu bata iya gaya mai saidai ta hak'ura. Abubakar na zaune cikin mota ya ziro k'afarsa waje yana danna waya kamar ance ya kalli gabansa yaga su INdo da Nafeesah suna tahowa cike da nutsuwa tamkar basu ba. "Masha Allah." Yafurta a hankali yana yana me binsu da ido. Har k'asa suka tsuguna suna gaida ya kasa amsawa INdo sai kallonta da yakeyi. Sanye take cikin les Orange da ratsin green ajiki ta yafa mayafi green tamkar ranar da ake sanyata a alalle, wuyanta yasha sark'a tasa d'ankunne yatsanta da zo6e sai k'amshin turare sukeyi yace cikin fara'a. "Aishatul humairah da my sweet sis Nafeesatu kunyi kyau." Nafeesat tace, "Kai Yaya Abubakar ai kafimu nidai bari na shiga na sake takalmi." Tayi maganar tana mik'ewa daga tsugunnan INdo tayi saurin riko hannunta tare da mik'ewa suka shige gida ya bita da kallon mamaki ganin yanzu kunyar da take nuna Mai tayi yawa ya kad'a kai yanajin wani mugun dad in yanayi yana ratsa shi. Suna shiga ba dad'ewa suka fito domin sunsan su yake zaman jira, Inna tayi musu fatan alkhairi da addu'ar Allah ya dawo dasu lafia. Yana jingine jikin mota suka fito a hankali ya juya yana kallon INdo suka yi four eye's ta sakar mishi murmushi da fararan hak'oranta daya kaita asibiti aka gyara mata su le6anta yashi red janbaki ta bud'e gidan gaba ta zauna tare da kawar dakai tana kallon k'ofar gidan su. Shima shiga yayi yana cewa Nafeesah, "Zamu tafi mubarki fa." Tayi saurin fisge hannunta daga rik'on da shehu yayi mata yana bata sallahun abinda zata siyo mai idan sun shiga cikin kano. A hankali ya dinga tafiya har suka fita daga sumaila sannan ya fara gudu dan ayau zai dawo dasu, suna ta hira wanda yawanci akan makaranta ne data ke zuwa lesson sai dai abin ayi addu'a kawai amma INdo kam bata fahimtar turancin da akeyi sai 'yan
Chapter 20 · 0% Book details