Sashe 12
Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta." Mtwww "inajin baka ganeta bane shi yasa kake sakar mata fuska, toh bari na tuna maka kowa cece INdo malam Hamza, wannan me satar amsar ce me cizon maza nasan yanzu ka harbo ta." "Really my twinnie? Abubakar ya fad'a yana sake maida kallonsa fuskar INdo, kwakwalwarsa kuma tana sake hasaso mai lakacin daya kamata ta duk'ufa tana kwafar note dan sam koda ta kwafo ma bagurin da aka tambaya bane, ya kuma kallon Sadeeq cikin mamaki yace "Gaskiya m twinnie kayi k'ok'ari indai haka ne. Ashe k'azan tace duk ta maidasu mahaukata Gaskia I'm sure nan gaba za'a sha mamaki indai suka d'ore da haka za'aji dad'i sosai." K'afarsa yaji ana jijijigawa hakan yasa shi saurin kallon k'afar kawai yaga INdo ce take mai alamar magiya tana nuna mai ya samo mata kyauta kota meye Sadeeq dake fito da kayan zai bawa wad'anda suka ci ya kalli Abubakar dake kallon INdo kawai yaja tsaki sabida takaici. INdo kam sai nunawa Abubakar malam Sadeeq takeyi alamar be zabo mataba zasu k'are yayi dariya cikin zuciyar sa ya kalli sauran masu kuskuran yace. "Kuzo nan muyi photo daku." Suna jin haka suka ruga bayansa suka jeru amma sam INdo batayi gigin zuwa ba hankalin ta yana wajan malam Saseeq dayake ta rabo zuciyar ta tamkar ta fito tsabar fargaban karsu k'are. "Humaira zo mana ayi dake." Abubakar ya fad'a yana kallon Indo , ita kuwa bata masan da ita yake ba tana ji tana gani har malam Sadeeq ya kammala bada kyautukan taji wata muguwar tsanarsa tundaga k'asan zuciyar ta ya game da ilahirin jinin jikinta tayi ta zagba mai harara bemasan tanayi ba yana can yana sake yiwa wad'anda sukaci kyautar nasiha da kuma muhimmancin tsabta da Ilimi. Kuje kuma ku zauna kowa yaje gida yayi karatu ranar Monday zanyi muku test duk wanda ya fad'i ni nasan irin hukuncin dazan d'auka akansa kunajina ko?!" Malam Sadeeq ya fad'a bayan yaga yau twinnie d'in nasa da mutunci ya shigo, duk 'yan ajin suka ce "OK uncle." Dayake yana k'ara d'an wayar dasu, amma INdo data tashi sai da ta d'auki ledar littafinta ta faki idonsu duk da cewar Abubakar nason yayi mata photo da kwalliyar ta yana can yana tambayar Sadeeq mezai iya bata koda ba babba bane ba sukaji tana cewa. "Baza'ayo karatun tess (test) d'in ba, kai idanma kun sake ganina a makarantar nan dan Allah ku soya ni. Wallahi malam Sadeeq yayi karya kuma ance babba me karya d'an wuta ne gobe k'iyama yana kusa da fir'auna, Allah ya sakamin sabida na kashe kud'ina garin yin kunhi da gyara kambas d'ina sai Allah ya saka min. Yo dan baka bani atamfar ba seme, nima Inna ta zata sai min ai sallah ta kusa." Tana gama fad'a ta murgud'a baki ta juya da gudu zata arce taji an rik'eta gam cikin tsananin tsoro da tashin hankali tayi k'ok'arin juyawa taga waye sai taga malama Murja ce ta cafketa tare da tura ta cikin ajin, tana zuwa ne da yake period d'inta ya shiga sai taji irin rashin kunyar da takewa malamin hakan yasa tayi shiru sai data kai k'arshe zata gudu tayi saurin kamata. Tsananin mamakinta suka kama Abubakar, sai yanzu ya kuma tabbatar da cewa itace ya tashi a fusace yayi kanta jin yadda take gayawa twinnie d'in nasa magana. Sadeeq ne yayi saurin taresa yana kad'a mai kai alamar karya doketa, yana wani irin numfashi ya ture hannun Sadeeq d'in daga kafad'arsa yana cewa. "Ka rabu dani Sadeeq bakaji yadda take had'aka zama da fir'auna ba, barni naci uban shegiyar yarinyar nan da har ina tausaya mata ashe batada mutunci har yanzu." "A'a twinnie barni da ita, kayi hakuri ka kwantar da ranka. Malama na gode da gudun mawarki, ke kuma zonan..." Sadeeq ya fad'a yana damk'o hannunta Abubakar kuwa jiyake tamkar ya ham6areta sabida 6acin rai. Fita yayi da ita sai ihu take musu har suka k'arasa cikin staff room ya kalleta yace. "Kama kunnanki." "Dan Allah malam kuyi hakuri." Babu wanda ya kulata sai dai duk malam cikin staff room d'in saida suka bada shedar rashin kunyar INdo, ganin babu mebada hakuri ne yasa ta sunkuya ta zura hannunta tana nishi tana cewa "malam wallahi hannuna baya kaiwa abakacin sa kace nayi nibdom (kneel down) kaji." Jiyosu ma tayi suna hira babu wanda ya kulata dan yau takaisu bango, tun tana magiya har tayi shiru. Ta dad'e tana kamun kunnen kawai suka ganta ta fad'i k'asa Abubakar dake kusa da gefenta besan lokacin daya kai hannu zai tarota ba amma saida tayi k'asan, ashe baccine ya kamata, kuma duk da fad'uwar da tayi hakan besa ta tashi ba saima zarcewa da tayi tafara sauke munshari. "Twinnie mu wuce tunda ka gama." Beh jira cewar sa baya k'arasa inda INdo take kwance sai uban munshari takeyi tamkar wata babbar mata a hankali ya dinga k'iran sunanta amma inah ko motsawa batayi ba, hannu yasa dai-dai kafad'arta yana jijjigata nan ma still bata motsaba. Ganin yadda yake bin ta a hankaline yasa Sadeeq mik'ewa ya d'auki dorina yana zuwa ya tsula mata a baya. A razane ta mik'e ta rarumi Abubakar dake tsaye kusa da ita tana cewa. "Wayo Allah atamfata ce." Sak'e tsula mata yayi tayi saurin sakin Abubakar tayi k'ark'ashin tebur d'in malam yahaya tana kuka tana sosa gurin cikin kuka take bashi hakuri yayin da shi kuma Abubakar ya fita daga cikin staff room d'in. Sai da wasu malam suka bawa malam Sadeeq hakuri sannan aka ce taje ta tsugunna ta bashi hakuri tayi sannan ya hakuri yace kuma duk sanda ta kuma yin fashin zuwa makaranta sai yasa ankamota yayi mata duka tace toh. Fitowa yayi amma bega Abubakar d'inba har ya fita gate babu bare alamun motarsa, sosai Sadeeq yayi mamaki sai ya nufi gidan shima amma abin mamaki bako motarsa a gurin hakan yasa shi kiran wayarsa aka sanar mai cewar a rufe take, mamaki ya kuma sark'e Sadeeq. Yana tsaye a gurin har su INdo suka wuce suna gulmarsa be kulasu ba. Shi kuwa Abubakar yana fita motarsa ya hau yakama hanyar gida, haka kawai yau yaji baya son jin kukan INdo zuciyarsa har zafi take mai duk kuwa da cewar yasan itace batada kunya amma ya rasa dalili, tunda ya taho tunaninta yakeyi yayi-yayi ya halasto qibd'iya ya kasa sai dai INdo da kamanninta ya buga sitiyarin motarsa yafi sau ashirin harya k'arasa gida. Yana shiga yaji Maman su na cewa. "Kajishi can najiyo tsayuwar motarsa da alama ya dawo. Toh shikenan 'biyu kyautar Allah kaima Allah yayi maka albarka." Sai da ya bari ta kashe dan yasan da Sadeeq takeyin wayar sannan ya shiga cikin gidan nasu bakinsa d'auke da sallama.... _Kuyi hakuri da wannan, kunsan bawa duk yadda yaso yayi abu idan Allah bebashi dama DA iko ba toh babu abinda zai iya yi a rayuwarsa. Nagode luv you all._ Gaisuwa da fatan alkairi zuwa ga aunty Sdy jegal, Ina miki fatan alkairi a duk inda kike, Allah ya raya mana baby boy d'inmu cikin addinin musulinci. *HAJJA CE* [7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA... A true life story *K.A.S Precious Hajja ce* *HASKE WRITER'S ASSOCIATION* (Home of expert & perfect writer's) *DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu. _Shafin yau na kune 'yan grp d'ina wato *HAJJA CE NOVELS GRP* da *ZAURAN BIEBIE ISAH* tare da * HERTY NOVELS* da *MUSHA KARATU N YBK2* gara nayi muku jam'u domin idan na tsaya lissafoku sai kunji haushina kunce dama typing nayi muku da wannan lissafin. Hak'ik'i ina jin dad'in yadda kuke tare dani, comments d'inku nasani dariya da kuma nishad'i uwa uba kwarin gwaiwa. Nagode sosai #ana tare da INdo malama Hamza._ Page *10* Amsawa Maman tayi tana had'a musu zo6o. k'arasawa yayi ya zauna akan kujera 'yar tsugunno sai faman shafa sajen fuskarsa yakeyi. Umma Dijeh ce ta fito daga parlor kasan cewar muhad'u a parlo ne ta kallesa tana murmushi cikin wasa tace mai. "Likita bokan turai, daga sallar juma'a kuma sai ina? Ko yauma za'a lek'a mak'ota ne..?!" Wayarsa ya zaro zai kunna domin tunda ya baro makarantar ya kasheta sabida yasan dole Sadeeq ya nemeshi, shikuwa beshirya abinda zai gaya masa ba. Kallan Umma Dije yayi sannan yayi murmushi yace. "Haba Umma jiya fa naje, kuma yauma bata nan." Dariya suka yi itada Maman sannan ya tashi ya fito yashiga d'akinsu, kayan jikinsa ya rage ya zauna daga shi sai vest da boxer shorts sannan ya kuma d'aukar wayarsa dai-dai lokacin kuma Sadeeq ya kuma kiransa. Babu yadda zaiyi dole ya d'aga kodan ya kare kansa daga wajan abokin haihuwar tasa, cikin basarwa ya kara a jikin kunnansa tare da fad'in, "My twinnie sai kaga na taho ko?!" Sadeeq dake zaune a k'ofar gida ya ta6e baki sannan yace. "Ba gani nayi ba nemanka nayi na rasa wanda kuma ni bansan dalilin yin hakan ba, twinnie kasan irin tashin hankalin daka sakani? Da police station zanje nakai report sai kuma muka yi waya da Mother take cemin gakanan ka k'arasa why did you do this to me ah?!" Duk sai Abubakar d'in yaji babu dad'i ganin yadda duk ya tayarwa da d'an uwan nasa hankali, da kyar ya samu mafitar da zai wanke kansa ya numfasa tare da cewa. "Kayi hakuri nima saida na taho naga rashin dacewar hakan tunda bamuyi sallama ba, abinda ya faru shine ina fitowa Dr Inuwa yake sanar dani ana nemana a cikin asibitin da gaggawa shi yasa duk na rud'e na kashe wayana dan karsu dunga damuna sorry twinnie kaji kayi min afuwa.." "Okk bakomai yanzu tunda naji kana gida sai anjima." Kamar ya tambayesa INdo sai kuma yayi shiru suka ajiye wayar shi kansa besan yadda zai fad'i abinda yakeji ba har mamaki yake yi ya ajiye wayar yashiga toilet. Wanka yayi lokacin har an kawo mai abincinsa an ajiye amma ko kallansa beyi ba sai wayar ya sake d'auka ya shiga gallery, hotunan dayayi mata ba tare da kowa ya sani ba. Yana gani yana duba na e so yake yagano meke damunsa amma inah..ya kasa tantancewa sai faman k'aryata zuciyarsa yake yi da abinda take shaida mai. INdo kuwa tana zuwa gida ta fara cire kayan jikinta tana killarwa ta sanya wata