← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 53

Sashe 33

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

gidan ba, gidan yayi matuk'ar yin kyau domin yasha tile's bangon da k'asan ta ko'ina sai dai bekai girma da tsaruwar na marigayi Abubakar ba amma hakan be damu INdo ba domin na iyayanta sam be kama k'afar su ba. Kallon agogo Hawwah tayi tare dajan tsaki tace. "Wallahi Yaya Sadeeq d'an wulak'anci ne, yasan fa muna jiransa amma bazai zo ba ga mijina can sai waya yake yomin." "Kinga yayya Hawwah kiyi tafiyarki mu zamu jirashi." Haleema ta fad'a tana gyara kwanciya akan kujera hannunta rik'e da waya wanda hakan yake nuni da cewar chatting takeyi. "Ba haka mukayi da Abba ba, cewa yayi karna bar gidan nan sai na tabbatar mai da shigowar Yaya Sadeeq." "Toh saiki zauna gyara wani auran ke kuma ki 6allo naki ba." Waya ta zaro zata k'ira Abba sukajiyo sallamarsa a k'asan makoshinsa. Tashi kowanne yayi yana sanya mayafinsa ya zauna a kan kujera. "Toh Yaya Allah ya bada zaman lafiya." Yayi shiru yana canza channel Hawwah tace. "Yaya ina muku addu'a kayi shiru." "Ke malama ku wuce kutafi gida bana son sa ido." "Amin yayya Hawwah mun gode a gaida gida da abban siyama sai munzo." Suka jiyo muryar INdo tana fitowa daga bedroom, hatta shi kansa saida ya kalleta ta gyatsina mai hanci tabi bayansu danyi musu rakiya. "Amarya kamar karmu barki wallahi." "Allah sarki Aminatu idan Allah ya kaimu basai ku dawo ba." "Zamu zo amma da yamma kinga gobe monday akwai makaranta." Cewar Haleema INdo tace. "Toh koma dai yaushe ne sai kunzo a gaida Mama." "Zataji." Suka fad'a tare da juyawa su shiga mota da driver na jiransu itama ta juya ta shiga ba tare da ta kulle gidan ba. Zama tayi a falon tana wak'ar Nas ya shareta yana kallonsa itama bata kulasa ba domin ba so takeyi ba daman. "Ke jeki kwanta dare yayi." Yayi maganar yana gyara kwanciya akan kujera. Itama ta gyara zama tare da d'aukar remote tana murmushi tace. "Wallahi malam Sadeeq banajin bacci." Had'e rai yayi domin yana son yin waya da Fateema ya rage mata dare yayi mata alk'awari gashi wannan yarinyar zata samai ido. "Ke bakya jin magana ko? Kin tashi kosai ranki ya 6aci.?!" Tashi tayi cike dajin haushi ta shiga bedroom, kan gadon Abubakar datake so shi aka sanya mata a d'aki d'ayan kuma dayake matsayin nata aka sashi a d'ayan d'akin da ake nufin na sadeeq ne. Tana kwance kwai ya fad'o mata ta zura hannu k'ark'ashin filo wayam babu sweet d'insa da yake ajiyewa ta kalli agogo da yanzu suna tare kawai ta mik'e ta koma falon tana k'ik'ifta ido. "Idan Zan iya zama ni d'aya a d'akin Allah ya tsinen..!" Sadeeq dake manne da waya a kunnensa yaji da fad'a. A hankali yace. "Babyna wait zan sake kiranki." Kashewa yayi tare da juyawa ya kalleta sai kuma ya juya ganinta sanye cikin riga da wando pink and white na bacci sun kuma zauna a jikinta d'as duk da basu kamata ba yace. "Toh kina son nazo mu kwanta tare ne." "Malam Sadeeq ko bakazo badai toh kabarni anan." "No baki isaba ko kuma ki kwanta anan d'in ni saina shiga ciki." Zama tayi kan kujerar tare da cewa,. "Tunda waya kakeyi toh ka k'arasa anan idan ka gama sai ka tafi nasan sannan nayi bacci bazanji tsoro ba." Mtwww yaja tsaki ta kwanta suna kallo duk sunyi jigum har wajan 1:45am duk ya gaji ita kuma sai a lokacin tad'an fara lumshe ido ya zaro wayarsa ya lalibi Fateema amma abin mamaki switch off ya cillar da wayar gefensa yasan haushi taji be kiraba yanzu kila tana can tayi mai fassara kala-kala. A takaice duk anan falo suka kwana, haka har yayi kwanaki biyu a gidanta washe gari Sadeeq da Fateema suka wuce kwara state cike da farin cikin su ita kuma INdo aka turo mata Aminatu ta taya ta zama.. _M fan's kuyi hakuri gobe zakujini shiru zanyi 'yar tafiya insha Allahu dana dawo zamu d'ora I need ur prayers please._ *HAJJA CE* [7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: * MUSAYAR ZUCIYA...
Chapter 33 · 0% Book details