← Book details Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 53

Sashe 53

Musayar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

ransa. Sun dad'e suna faranta ran juna duk sun manta da rigimar su ta baya Sadeeq ya kawar da rayuwarta ta baya a cikin ransa yana ganin tamkar dama a hakanta ya santa. Watan Ayman takwas kenan har gidan Fateema ake kaisa ya d'an jima kafin a dawo dashi tana son yaron har cikin ranta domin tana masifar son mahaifinsa. ***** K'arfe takwas ya shiga gida, zaune ya ganta tana gyarawa Ayman kwanciya a falo, dariya yayi har yana rik'e ciki ganin yau kuma da salon da za'a siyeshi can ta tsuke cikin riga da wando nan kuma tayi mai shigarta daya santa a real INdon ta zamanin tana kauyan sani. "Kai malam Sadeeq he wani kallona kakeyi he kace baka sanni ba." Wayyo dariya Sadeeq ya tsugunna agurin ya dinga yi dan gani yake tazo mai da wani sabon salon soyayya. Ta dashare mai baki tare da k'arasawa wajan sa tasa hannu ta rik'osa da nufin ya tashi aikuwa ya janyo ta itama ta fad'a kansa suka dinga dariya cikin shauk'i. "Cutie I love you so much." "I love you too Abu Ayman." "Allah yajik'an M tiwwine yasa rahama ta baibayesa yasa yana cikin farin ciki kamar yadda muke a yanzu." "Amin ya Allah." Ta fad'a tana wasa da ma6ullayen rigarsa nan suka dinga hirar baya suna dariya. Shirye-shiryen bikin Haleematu suka farayi Sadeeq yayi k'ok'ari sosai dan da su biyu suke had'uwa suyi komai shi yayi kayan d'akin hawwa Abubakar kuma yayi na falo amma yanzu baya nan daga shi sai Abba suka dinga yin komai. Duk matan sa kuma sun zage anyi komai dasu cikin farin ciki dajin dad'i, suna nan kuma har yanzu a tare mijin su yana sansu iya gwargwado yana bawa kowacce hakkinta. ALHAMDULILLAH. Allah na gode maka daka nuna min farkon labarin nan da kuma k'arshensa, Allah kaine abin godiya kuma abin alfahari alhamdulillah. Allah kajik'an marigayi kasa aljanna ce makomarsa da aiyukan alkairinsa. Duk wad'anda suka rigamu gidan gaskiya a cikin musulmai Allah ka yafe musu mu kuma kasa mu cika da kyakkyawan aiki. Dole na godewa masoya masu kaunar Hajja ce da kuma rubutunta, hakika wannan novel d'in ya sadani da mutane masu d'in bin yawa wad'anda baki baxai iya fad'ar yawansu ba, haka kuma hannu bazai iya k'ididdige yawanku ba sai dai nace Allah yabar soyayya da kauna tsakaninmu yasa sakon ciki ya amfanar daku. Nasan na 6atawa wasu rai toh dan Allah kuyi hakuri, nasan na farantawa wasu rai toh kuma kun faranta min, nasan na nishad'antar da wasu nima kun sani nishad'i kusani reader's kune jigon saka duk wata writer cikin farin ciki haka kuma kune kuke saka writer cikin damuwa domin idan bakwa karantawa bazataji dad'in yin rubutun ba duk kuwa dason yin rubutunta nidai na gode muku masoya na fili dana 6oye na kusa dana nesa bazan iya lissafoku ba domin hakan ya janyo min fitina harma wasu daga cikin wad'anda nake alfahari dasu suka gujeni sabida ban yi musu dedication ba amma still suma idan sun karanta karshen page dinnan suyi hakuri ni 'yar Adam ce me laifuka kala-kala a doran k'asa suyi hakuri but bazan manta dasu ba a cikin zuciya ta ba. *K'ANWATA STYLISH.*:-Dake aka shirya za'ayi rubutun nan kika gudu kika barni, but ba komai nasan dama ke lazy writer ce (smile) nayi na gama kuma na gode miki da sake zakulo min muhimman abubuwan cikin labarin Allah ya barki da mijinki Lafiya keda k'anwarki Abler. *MISS XOXO:-* Bazan iya kammala rubutu na ba ban sakoki ba koda kuwa wasu zasuji haushina, kin taka muhimmiyar rawa a cikin rubutuna ta yadda nake hanaki bacci nake hanaki jin dad'i har sai kin bada taki gudun mawar hakan kuma yasa labarin ya tafi cikin tsari da jin dad'in karanta shi, Allah yayi miki albarka ya nuna min lokacin auranki autarees Ina alfahari dake ked'in masoyayyar Hajja ce wanda babu algus. Ina alfahari da duk me bin labarina grps d'in da nake ciki da wanda bana ciki Ina alfahari daku. 'Yan wattpad ina alfahari daku Ina sanku har cikin kalbina kud'in na daban ne. My co-writer's da suka bi labarin nan ku sani naji dad'i sosai duk da wasu na sansu wasu kuma ban sani ba amma sun karanta Ina fatan duk wacce taga gyara ko kuskure zata yi min domin Ina son hakan Allah ya k'ara baseera da kwarin ido. Olo my one &only Ina alfahari dake ked'in aminiya ce ta kwarai.Tare da aunty na Maijidda musa da yayata barrister Fateen Bch. *HAJJA CE NOVELS GRP* *HASKE WRITER'S:-* kungiya ta Ina alfahari daku Allah ya k'ara baseera ya k'ara had'e kawunan mu amin. *HAJJA CE* *HAJJA CE* Times New Roman Times New Roman Calibri Calibri !%),.:;>?]} $([{ SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office 6baa432ee75244788a065aab42bc1b69
Chapter 53 · 0% Book details