← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 73

Sashe 9

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Can dakin Inna ta tafi ta kwanta tunanin rayuwan dake shirin tinkaranta take, yaHaidar ya tsaneta fiye da komai a duniya, itama ta tsanesa bata kaunan koda ganinsa ne amma ya ta iya bazata iya watsawa su Abba kasa a ido ba mutanen da suka zame mata sutura a rayuwa.... tana a haka 'yan uku suka turo kofan daki take ta rufe idonta kaman me barci gaba daya tausayin Hanifa suke sosai dan haka suka fice suka bart tayi bacci, suna fita wani sabon kuka ya kufce mata shiknn yanzu zata rabu da 'yan uwanta, 'yan uwanta da suke tare koda yaushe dare da rana safe da yamma, ta goge hawayen idonta sanda Inna tayi sallama ta shigo.
"Abinci ne a plate Inna ta shiga lalla'bata taci, fir Hanifa ta kasa cin abinci inna tayi tayi haka Anty Hiba ma duk taki saida mamy tazo da kanta snn ta samu ta saka wani abu a cikinta..
"Washe gari Haidar ya iso gari bayan Abba ya masa tuni kan magann su, shi kam gaba daya ya mance da wani aurwn Hanifa a kansa, abu daya yake tunawa yayi murmushi shine zai koya wa Hanifa hankali zai saita tabyanda bazata kuma kodankallon banza bane wa mutane balle har ta kaita ga masu rashin kunya...

"Jere na gani a fada Abba yayima Hanifa a gidanta na Kano, babu yanda su Shema basuyi ba kan Hanifa ta yarda a danyi koda walima ce amma fir taki, gaba daya ba isheshen lafia bane ma da ita, tunda yaHaidar ya iso gari dir taki su hadu.
"Yau tana zaune bayan Anty Hiba ta tilasta mata shan pepper soup, haka ta sha kadan duk jinta take batada appetite yayi sallama ya shigo.
"Take gaban Hanifa ya shiga dukan taratara, Anty Hiba ce ta iya amsa sallaman kana Haidar ya shigo yana sanye da jampa blue da hula zanna bukar, sai kamshin Dolce n Gabbana ne ke tashi ajikinsa.
"Woh wann wani irin angone da bazai bari a kai masa mayarba sai yazo ya dame mutane, cewan Anty Hiba teasingly.
"Murmushi Haidar yayi hannunsa na nade a kirji kana ya saci kallon Hanifa da gaba daya ta kasa daga kanta sai faman bin plate din hanunta take da kallo. Anty Hiba ta mike tace toh maza kasata taci tunda ka shigo, sai snn Hanifa ta dago kanta tana duban shi amma me, wani mugun faduwan gaba taji tayi saurin sunkuyar da kanta. Daga haka Anty hiba kam ta fice abunta.
"Hanifa kam kiris ya rage numfashinta bai daukeba dan tsoro, Haidar yayi taku kadan ya karaso gabanta. Kallonta yake dan rabonshi da ganinta yakai 2yrs.
"Kwanto da kanshi yayi daidai saitin kunnenta take ta soma ja da baya dan kuwa 'bari jikinta ya soma, yayi murmushin cin nasara kana. Ina zakije ko kin mance mijinki ne a gabanki abinda ya fada knn cikin dakewa.
"Bata fasa matsawa ba saida ta isa kuryan gado, kafa yasa ya take kafanta wanda ya hanata karasawa karshen gadon, dukda zafinnda taji hakan baisata uffa komi ba sai hawayen dake kokarin ciko idonta.
" hannu yasa ya cire hijabin dake jikinta, take ta shiga rike hijabin tana fasin "dan Allah yaHaidar kayi hakuri.... Shiii! Ya daura hannu a bakinshi alamun tayi shiru ya karasa cire hijabin ita kam Hanifa rumtse idonta tayi ga kirjinta dake barazanar tarwtsewa, 'yar karamar rigace a jikinta wanda ya nuna komai na jikinta, take yaji bezai iya jure kallonta a haka ba, dan kuwa wani irin yarrr yaji gaba daya illahirin jikinsa, tasa hannunta ta shiga kare kirjinta... tsaki yayi gamida jefa mata hijabin jikinta yace" meye kike boyewa a wajen, kina tunanin kinda abinda ni Haidar zai burge ni ne, never. So nake na fada maki ki shirya zama a gidan yari dan kuwa na tanadar maki rayuwa mafi kunci a gidana, mayya idan banda mayya dasu Abba suka tambayeki ko kinason auren ai ce masu zakiyi baki so, amma dashike ke mayya ce 'yar 'karama dake kina son sanin namiji shine zakice masu kin amince, yayi wani murmushin mugunta kana yace "this is the huge mistake you made, I'll make your life so miserable ta yanda sai kin tsane rayuwarki. Is not too late for you little Brad zaki iya zuwa kice masu baki son auren, am just warning you kar kiyi mistake din zuwa gidan Haidar idan kunne yaji jiki ya tsira. Daga haka ya fice zuciyansa fes...
"Kwanciya tayi bisa pillow din dake gefenta ta shiga rusa kuka me tsuma zuciya....

"Washi gari idanun Hanifa duk sun kumbura saboda kuka, Anty Hiba ta gama hada mata kayanta da wasu turarruka da ta hada mata, dan jirgin karfe 12:00pm zasu bi,
"Tana zaune gefen Abba a kasa bayan ya gama mata nasiha da fatan alkhairi tare da saka mata Albarka, Haidar yayi sallama ya shigo parlorn, saida zuciyanta ya tsinke da jin sallaman yaHaidar shiknn da gaske ne zata tafi ta bar su mamynta.
"Haidar ya karasa ya gaida Abba, Abba ya masa nasiha sosai shima kana ya hadasu baki daya ya masu nasiha mai tsuma zuciya. Haidar ya saci kallon Hanifa data sunkuya tana hawaye, murmushin side yayi na mugunta a ranshi yace yarinya bakima yi kuka ba tukunna.
"Haidar ne ya fara mikewa yayi sallama da Abba kana ya fice ya nufi sashen mamy, nasiha mamy ma ta masa sann tace sun mallaka masa amanan Hanifa, Hanifa amana ce a garesu dan haka sun dauki wnn amana sun mallaka masa. Har airport suka raka su gaba daya mutanen gidan idan ka dauke Abba, sosai Hanifa tasha kuka ta rungumesu Shema gwanin ban tausayi, ana fara kiran garuruwa mamy ta rungume Hanifa sanda aka kira garin Lagos Haidar yayi sallama dasu mamy kana Hanifa tabi bayansa tana sanye cikin bakar abaya ta yane kanta da mayadin kayan, haka sukata waving wa junansu har ta shige.....

👸🏻Queen Samy😍💄💋......🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
18 and 19

"Suna shiga cikin jirgi bayan sun zazzauna kowa bisa seat dinsa aka soma announcing su 'daura belt, Hanifa sai kiciniyan 'daura nata take amma ta kasa. Haidar ya kalleta ta wutsiyan ido takaici ya kuma kama shi even seat belt ma bata iya 'daurawa ba, yayi gajeren tsaki kana ya sunkuyo kansa na gogan fuskanta hannunsu na shafa na juna ya rike belt din, gaba daya saida shock ya ziyarci jikkunansu, kirjinta kuwa yaci gaba da lugude kaman ana daka dan bugu. A daidai saitin kunnenta ya ra'da mata " So dama all this rashin kunya da tsaurin ido naki even seat belt you don't know how to tie it, what a surprise. Yayi wani murmushin mugunta kana ya daura mata seat belt din sann ya gyara zamansa.
"Hanifa kam babu bakin maga dan this is her first time da ta ta'ba shiga jirgi, kuma sarai yaHaidar ya sani kawai dai salon wulakancin sa ne. Lumshe ido tayi kaman me bacci sanda jirgi take shirin tashi kuwa a razane ta hantsila jikin Haidar gamida 'kan'kanme sa ta tura kanta cikin jikinsa, sosai yaji a jikinsa da irin rikon data masa dan kuwa sakwanni ne da dama suka jiyarci illahirin jikinsa.
"Kallonta yake ganin yanda ta wani razana, be ce mata komai ba har lokacin tana nan makale cikin jikinsa wanda ita kanta batasan tayi hakan ba, saida ya bari jirgi ta daidaita a sama kana ya matse 'kugunta cikin jikinsa snn ya kai bakinsa saitin kunnenta a hankali yake ra'da mata " Saurin me kike ne Witch, saboda tsaban son maza irin naki shine bazaki iya bari mu isa ba saikin gwada wa kowa in public you're in need of namiji ko. A razane ta dago tana dubansa nan fa ta tuna ashe a jikinsa take, take ta shiga kiciniyan kwace kanta... matseta ya kuma yi cikin jikinsa kana yace" Saidai kash burinki na kwadayin namiji bazai cika ba dan ni Haidar kam na maki wuya I don't feel anything for you, to me you're nothing but a piece of trash, taba jikina ma da kika yi yanzu ji nake kaman na ganni a gida na samu na wanke jikina dan kar alargy ya feso mun, daga haka ya saketa ya komar da kansa bisa seeat kana ya lumshe idonsa.
" Shiru tayi sai zuciyanta dake mata mugun 'kuna wai shi meye ya 'dauketa da yaketa jifanta da wnn muggan kalamai, hawayene taji na kokarin ciko idanunta take ta shiga karanto duk addu'an da yazo bakinta....

_Lagos_
"Suna fitowa daga Arrival driver din shi ya karaso gamida sara masa yana fadin "welcome sir, gaisawa sukayi kana ya karbi jakan kayansu ya karasa dashi yanda yayi parking mota, bayan ya zuba kayan a boot ya budewa Haidar front sea ya shige dan dama shi baison zama baya kullum a gaba yake zama koda driver ne ke jansa.
"Philips ya budewa Haneefa back seat gamida sara mata snn ya koma mazaunin dreba yajasu zuwa Maritime.
Chapter 9 · 0% Book details