← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 73

Sashe 8

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Su mamy kam shiryeshirye suke kan yi Anty Hiba kuw abun ba'a cewa komi, bata sama bata 'kasa tuni ta iso kano kullum tana kasuwa ana sayayya.
"Yau suna zaune ita da mamy hira suke wanda ya shafi bikin.
"Nifa sai inaga kaman bamuyi ma Hanifa adalci ba ya kamata mujira muji ta bakinta dan ballaline wannan hukunci ya mata, sannan ko kadan dama jinin Hanifa da Haidar kwatakwata bai jutuwa, beside sai inaga tayi karama ma aure gaba daya tausayinta nake.... mamy ta fadi sanda take duban Hiba.
"Anty Hiba tayi shiru kana tace "mamy ki rika kyautata zato inshaAllah wann aure zai jure zai zame mana abin alfahari nan gaba, dama wuyanta na miji ya amince ne mace kam nata mai sauki ne, sannan a hankali sai kiga sunso junansu.. mudai fatanmu Allah ya tabbatar da alkhairinsa.... ameen sukace gaba dayansu....

"Duk wann bidiri da ake Hanifa na can sch suna rubuta jarabawa babban burinta kiwa bai wuce ta fita da sakamako mai kyau ba dan farantawa iyayenta....

_Friday 5th June_
Yayi daidai da ranan da aka daura auren Haneefah da Aliyu Haidar a babban masallacin central mosque bayan saukowa daga sallan juma'a, hakan kuma yayi daidai da rananr su ta 'karshe na rubuta jarabawan kammala sakandari... mamy kam tasha kuka wanda ta rasa kukan na farin ciki ne kona akasin haka.

👸🏻Queen Samy😍💄💋.........
[5/9, 6:18 AM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
15

Tun kafin su iso gida take murna yau zataga mamynta duk ta ishesu a motan banda zumu'di bata komai.
"Sumy tayi gyaran murya tace Hany are you sure BUK kike so, kai nikam gaskiya I preferred ATBU shinema first choice dina.
"Wa nifa kinsan bazan kuma yin nesa da mamy ba, from now on nothing will tear us apart. We will always be together.
"Shema daketa duba slumbook dinta sai lokacin tayi magana " lallaima kid sis and does that mean zaki zauna da mamy for the rest of your Life, what about if you get married, are you going to live together with her and the husband....
"Gajeren tsaki Hanifa tayi kana tace " Com'on sis Shema there you go again, da zaran anyi magana saiki kawo maganan aure wa mutum, and who told you ni auren nake sonyi....
"Eh mana she's right baby sis Sady ta fadi.... yatsina fuska Hanifa tayi snn tace" whatever!....

"Tarba na mussaman mamy tayiwa girls din nata, murna a wajensu ranan ba'a bayani, Inna kam baki ya kasa rufuwa ranan gaba daya jikokin nata sun girma sun zama 'yan mata sosai.
"Suna can sashen Inna suna zuba surutu Abba ya dawo wai zo kaga murna wajen girls din mamy haka sukaje suka ri'ka zuba masa shagwaban da suka saba shi kuwa sai biyesu yake dama yayi missing hakan. Mamy kam gaba daya batada walwala wani mugun tausayin Hanifa takeji. Walima maiji da lafiya Abba da mamy suka shirya masu, omo com see pretty ladies😍. Abun sai wanda ya gani....

"Babu yanda Abba beyiba a sanar da Hanifa maganan aurenta amma fir mamy ta'ki haka tayita rokon Abba ya dakata tukunna, a cewan ta ya dan kara lokaci bata gama shiryawa ba...

_Two weeks later_
"Kwanakin nan duk haka mamy keyin su cikin zullumi, ko kadan Hanifa kam bata kawo komi ba, su Shema kam suna son gano wani abu dan rannan sunji Inna da mamy suna maga kaman kuma akan Hanifa ne, Inna tana cewa gwara a sanar da yarinya tanada aure yanzu, mamy kuma na rokon Inna a dan kara mata lokaci dan bata son Hanifa tasan cewa ba itace ta haifeta ba....
"Toh tambayan a nan shine SU WAYE IYAYEN HANIFA SANN AURE AKAYI MATA? toh idan kuwa hakane SHIN WANENE *MIJIN HANEEFAH* wannan tambaya shine ya tsaya a ransu...

"Mamy da Anty Hiba zaune can kuryan dakin mamy, mamy tayi jigum abun duniya duk ya isheta. Anty Hiba ta rike hannun mamy tace pls mamy ki bari a fadawa Haneefa kafin Haidar ya iso gari... Girgiza kai mamy ta soma hawaye na bin kuncinta tace no Hiba noo... banyi shirin ganin irin wann rana ba, ban shirya cewa Hanifa am not her real biological mother ba. She's my daughter she's my child. ?. Kuka sosai ya kufce mata, Anty Hiba ta share kwallan daya zubo mata snn tace " you will always be her mother mamy, you're her mother pls lets end up this'boye 'boye sooner or later she will learn the truth. Snn akwai auren Haidar a kanta so dole a sanar da ita..... daidai nan suka bude kofa suka shigo su ukun "Shema'u Sadiya da kuma Sumayya... kallon kallon suka shig yiwa Anty Hiba da Mamy. Tabbas sunji komai take idanunsu ya ciko da kwalla.
"Shema ce tayi karfin halin cewa "Mamy wacece Haneefah sann YaHaidar shine *Mijin Haneefah*? Anty Hiba ta mike ta riko hannayensu kana ta tura kofan dakin ta rufe, zaunar dasu tayi bisa carpet gaba daya suna fiskantan mamy da Anty Hiba...
"Mamy ta goge hawayen idonta kana tace a yau zan fayyace maku sirrin daya jima a binne sirrin dabuku san dashi ba... gaba daya suka zubawa mamy ido suna saurarenta......

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/9, 6:18 AM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
16 and 17

"Mamy taci gaba da fadin, shekaru goma sha takwas da suka wuce Allah yayima iyayenmu rasuwa nida 'yan uwana guda biyu tak Deena da kuma Hiba. Tun bayan rasuwan mahaifanmu rikon deena da hiba kannena ya dawo hannuna a lokacin ni kadai keda aure cikinsu dan nice babbarsu dama.
"Mahaifinku yanada 'kani guda daya tak a duniya me suna Umar, Umar na yawan zama a gidan wansa wani sa'in yana gidan Inna toh a haka ne har Allah yasa suka fahimci juna shida deena har ta kaisu da aure, lokacin da akayi auren kuwa Umar ya samu aikin banki a meduguri dan dama ya kammala karatunsa. Haka akayi biki aka kai amarya dakinta can meduguri. Shekara guda da aurensu deena ta haifo yarinyarta kyakywa wacce ta shiga ran jama'a da dama aka sanya mata suna Haneefah. Haneefah ta kasance 'yar lele wajen iyayenta da dangi baki daya. Lokacin da takai shekara daya da rabi deena da umar suka yanke shawarin kawo nan kano wajena dan in yayeta. Hakan kuwa akayi, tunda suka kawo mun Haneefa na hadata da ku soyayyanta ya shiga raina har inajin sonta fiye da 'ya'yan da na haifa hakan ne ta kasance a wajen Abbanku ma. A wann lokaci kunada shekaru biyu a duniya yayinda 'Danmasani yake dan shekara uku yayanku Haidar kuma yanada shekaru gomasha daya a duniya, snn cikinku shi kadai ne yasan wnn labari da nake fada maku a yanzu dan kuwa shine yayi girman da zai sani.
"Rana da Hanifa ta cika sati biyu a wajena a ranan sukayi shiri cikinnzumudin zuwa 'daukan 'diyarsu..... kuka ya kuma kufce wa mamy saida tayi mai isanta kafin ta tsagaita kana ta ci gaba.... " zuwan da basuyi ba knn ganin 'diyarsu da basuyiba knn dan kuwa a hanya suka hadu da mummunan ha'darin mota wanda yayi sanadiyan rasa rayukansu....... kuka ya kuma kufce wa mamy yayinda Anty Hiba dasu Shema suke tayata....
"Tundaga wann lokaci mukayi alkawarin rike Hanifa tamkar mu muka haifeta tinda dama abinda yayita shi yayimu baki daya saidai yanzu ya zama dole tasan labarin asalinta dan kuwa a halin yanzu Haidar yayanku shine mijinta, shi kadai ne zai iya rike mana amanrta shida Hanifa duka abu daya ne.... ta rungumo hannayensu snn taci gaba da fadin Hanifa kanwarku ce, First Cousin dinku ce nida mahaifiyarta uwanmu daya ubanmu daya haka nan mahaifinta da mahaifinku iyayensu daya. Har a yanzu babu abunda zai canza tsakaninku.... Sosai su Shema ke kuka dan kuwa ko kadan basu taba kawo hakan a ransu ba... a hankali Sadiya ta mike tana share kwallan idanunta dan kuwa mugun tausayin Hanifa ne ya dira mata, ta sani ko kadan yaHaidar da Hanifa basa jituwa balle ace an masu ure zasu zauna gida guda matsayin miji da mata, tana bude kofa tayi tozali da Hanifa wacce ta durkushe a wajen tana kuka maras sauti alamun taji komai... da sauri su Shema suka karaso basu iya cewa komi ba sai rungumeta da sukayi suna kuka mai tsuma rai, Anty Hiba da mamy ma kukan suke... kusan minti babu wanda ya iya bawa dan uwansa hakuri gameda kukan da suke yi.
"A hankali ta goge hawayen idanunta ta karaso kan carpet yanda mamy ke zaune, zama tayi kan gwiwoyinta ta riko hannu mamy gam cikin hanunta, mamy kam kasa hada ido tayi da ita saima kallon gefe da take yi, a hankali ta soma furta.
"Mamy mamy na dan Allah ki kalleni mamy na, kice mun kece mamyna kinji mamy I love you mamy..... gaba daya kuka ya kufce masu Hanifa rungume mamy tayi tana kuka me tsuma rai mamy ma kukan take.
"Da kyar mamy ta iya saita kanta kana ta soma fadin "we're so sorry daughter ki yafe mana nida Abbanki na boye maki wann sirri har na stawon lokaci, it was never our intention to hurt you, we did this because we do love you dear. And maganan aurenki da Haidar idan baki so dole a warware shi kinji swthrt.... girgiza kai Haneefa ta soma yi kana tasa tafin hanunta ta rufe bakin mamy snn tace "mamy dan Allah ki dena bani hakuri ni kun gama min komai keda Abba banida abinda zan saka maku dashi nan gidan duniya sai addu'a, mamy ban ta'ba kukan maraici ba hasalima ba santa ba, kun nuna mun so fiye da 'ya'yan da kuka haifa kun rikeni bisa gaskiya da amana Allah ubangiji ya saka maku da mafificin alkhairi..... ta 'danja fasali kana taci gaba da fadin "aurena da yaHaidar kuma.. sai ta danyi shiru kana tace "mamy ku kuka fi cancanta ku za'ba mun miji na gari, Allah yasa hakan shine mana alkhairi..... kuka take sanda ta kifa kanta bisa cinyan mamy..
"Allah ya maki Albarka daughter Allah baki zaman lafia me daurewa a gidan aurenki Allah kema ya baki yaran da zasu maki biyayya yanda kika mana, mamy ta fadi sanda murmushin farin ciki ya mamaye fuskanta...
Chapter 8 · 0% Book details