← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 73

Sashe 48

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" 'Karfe 4:00pm ya gama duk wani abumda zaiyi a Office ya tarkasa ya nufo downstairs, Captain Paul da Admiral ya hanga daga can suna tattaunawa, daga nesa Paul ya dago masa hannu yana sara masa, murmushi Haidar yayi ya jefa masa yarensu na sojoji, ko kallo Admiral bai ishe Haidar ba ya shige motarsa ya bar wajen, Paul ya sheke da wata dariya yace I pity your life navy.... Admiral yayi wata mirmushi kafin yace yanzu zai gane ba'a ja da babba a waje, Paul are you sure kunyi aikin nan da kyau, paul yace haba sir ko ka mance ni na halaka chief of staff balle wani Haidar karamin kwaro, ai kawai yana isa soldiers zasu bi bayansa a bincike sa,.
"Admiral yayi dariya yace" Captain AA this is your end. Paul ya sheke da dariya ya sara ma Admiral, daga na suka wuce paul na binsa a baya kafin cheif security dinsa ya karaso yana sara masa.

"Saida ya biya wani store ya danyi minor shopping dangin su coffee da sauransu kafinnya nufo gida.... " Tun daga Main gate yaga navys kota ina an kewaye, fannin en securities, sosai abun ya basa mamaki kafin kaga haka sai wani gagarumin abu ya faru, bai gama shan mamaki ba saida ya iso cikin building dinsu dan ko ina securities ne ana bincike, yana gama parking ya fito.... " Daga nesa Admiral ya fara nunasa cikin zafin rai ga hawaye na bin kuncinsa yake fadin, there he is, arrest him, arrest him he's a murder, he killed her he killed my only daughter..... gaba daya Haidar be fahimci abunda Admiral ke fada ba, ganin Admiral gadan gadan ya nufosa yasa akayi arresting Haidar " you're under arrest sir..... " da mamaki Haidar ke binsu da kallo kafin yace, what do you mean I'm under arrest, this is ridiculous, out of my way. 'Kin matsawa sukayi saima dada arresting dinsa da sukayi daya daga ciki yace " muna zarginka da kisan 'yar Admiral ta baro hida jiya da daddare ta taho gidanka kwana, " tsaki Haidar ya buga snn yace thus is nonsense, will stop this stupid acquisition, "bindiga ya daura a 'keyar Haidar yace "am sorry Sir, but we need to check in your house..... " securitin ya shiga dagawa sauran hannu yana fadin " let's ho in... Haidar baice komai ba ya hangi Admiral yana tsaye can gefe an daddafesa, girgiza kai yayi yasaka key ya bude gidansa, nan aka shiga bincike ta ko ina, har sun fito suna girgiza kai ba komai, dayan yace " are you sure you search everywhere, no Sir except the bathroom, oya go in and serch.... bathroom din dakin Hanifa suka fara dubawa babu komai, suka duba na daya dakin ma babu, ana shiga na Haidar aka ga gawan Latifa cikin bathtub an cika da ruwa, har ta soma kumbura.... da sauri suka fiyo suna fadin " we found her death body in there...... " A zabure Haidar ya mike ya nufi cikin bathroom din, ji yayi 'kafarsa ta kasa daukarsa, innalillahi wa inna'ilaihirra ji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifli khairan min ha.... abunda Haidar ya iya fadi knn, Admiral kuwa wani 'kara ya sake yana fa'din a barsa yazo ya sha'ke Haidar....
" Handcuffs aka saka wa Haidar wanda ya koma tamkar mutum mutumi, meyake shirin faruwa dashi, meyasa baya kyutawa mutanen da suke kyauta masa, meyasa haka, Allah sarki Latifa wa ya mata wnn kisan gillan, tana da matsayi a raywarsa, ko babu komai ta nuna masa 'kauna, daya sani da ya saurareta a daren jiya.... sisiriyan hawaye ya sauko daga idonsa, ha'kika yaji zafin mutuwan Latifa..... " You have the right to remain silent, duk abunda ka fada zai iya zama hujja a gaban al'kali, cewan daya security din... " Admiral ya shako wuyan Haidar yana fadin " tell me me ta maka me ta maka ka kasheta, koda yake kayi furucin sai ka kasheta a gaban kowa last week, saboda kawai tace ta daina sonka ta daina kwana da kai shine ka za'bi rabani da gudan jini na, you won't escape the law Captain,.... "Haidar kam baisan sanda ya soma fa'din yes " ni na kasheta I killed her I'm a murder..... "Admiral ya juyo yana fadin kunji ko kunajinsa ko shine... take him away... nan aka dauki Haidar aka tafi dashi....

"A gajiye suka iso garin Kaduna, ta rasa dalilin dayasa gabanta keta fa'duwa, koda Ajmal ya dawo daga islamiya ma ba kaman yanda suka saba wasa ta masa ba, haka uncle Faruq, uncle Faruq yafi ala'kanta hakan da matsalolin da take fuskanta, dan haka ya gargadi Anty Hiba kar ta takurata da wani maganganun da zai rinka sata damuwa, haka a ranar dai Hanifa tankwana duk bata jin da'di, ga wani mummunan mafarkin da tayi da yaHaidar, haka tayita farkwa cikin dare, karshe dai mi'kewa tayi ta shiga jero nafilfili...

"Fitowansa knn daga wanka yana shiryawa wayarsa ta shiga ringing, gajeran ysaki yayi kafin ya 'karasa ya daga wayan, yana fadin navy ya akayi.. daga daya bangaren me maganan yace " sir kaji abumda ya faru da friend dinka kuwa, Aisar yace which of my friends, Captain AA mana he was arrested yesterday, an kamasa da laifin kisan 'yar Admiral..... " Aisar bai gama jin abunda yake cewa ba dan ji yayi kaman wasan yara, wait navy are you sure of what you saying,
"Am very sure sir, ka kalli news anjima ko ka saya news paper zaka gani.... salati kawai Aisar yake baisan sanda yayi jifa da wayan ba ya shiga 'kwala kirawa mum dinsa..

"Mum na zaune a parlor Aisar ya diro mata ka daga shi sai towel, gaba daya mum ta razana ta mike tana fadin lafiya kai kuma Aisar what's all this, yaushe zaka girma ka daina yawi da towel cikin gida.... " hanunta Aisar ya rike yana girgiza kai yake fadin mum " we need to leave, we need to go back to lag.... " har hutun naka ya kare I thought 1 week ka dauka, noo mum mu tafi babu lafiya... wai meke fatuwa ne Aisar, Mum sunyi sharri wa abokina sun kulla masa... Aisar will you put your self together and spell it out, Mum wai Haidar ya kashe Latifa, amma nasan wnn 'karya ne, Aliyu will never do that, kawai anaso ayi Framing dinsa ne.
"Salati mum ta hauyi tana fadin " ko ni nan bazan ta'ba yarda ba wnn yari mai hankali wanda yayi sanadiyan shirya tsakanin ka da dad dinka, kai wnn sharri ne aka 'kulla masa, maza saka kaya ka tafi ka sayo mana tickets. Aisar yace yeah mum right the way.... a sittin Aisar ya gama komai ya fice daga gudan...

"Misalin 9:am, Sumy ta shigo parlorn Abba nan ta tarae da iyayen nata suna breakfast kaman yanda suka saba snn ta gaishesu, Abba na murmushi yace my princess come and have some, murmushi tayi irin yanzu an girman nan an daina shagwa 'ba wa Abba, ta dan lagabe kai tace yanzu na gama ci Abba, sch zani inda 10 to 12, Abba yace toh my princess Harunan yazo, daga masa kai tayi tace eh Abba, Abba yace you sound sad my princess, akwai wani abu ne, " ta langabe kai tace no Abba, Abba yace tell me idan akwai kinsan yanzu dole na baki spcl kulawa dan hidan an watse an barmun ke, murmushi tayi tace Abba is just that am missing Hany so much, murmushi Abba yayi yace that's natural dear ai ba jimawa zagayi ba, just two weeks kawai zatayi.... mamy dai sai murmushi kawai take.... " News din da aka soma ne na labarun karfe taran safiya a AIT yasa gaba daya suka maida hankali can.... innalillahi wa inna lilaihirraji'un... mene wnn ake fada, wani kara Sumy ta sake ta zube kasa, mamy kam sumewa itama tayi a wajen.... Abba ne kawai me kardin hali ya shiga neman ruwa yana yayyafa masu, ihun da Sumy tayi yasa Inna fitowa babu shiri.... har lokacin ba'a daina nuno news din ba, ganin Haidar an daure hanunsa yasa Inna ta soma fahimtan meke faruwa dan ba turanci take fahimta ba....
"Habubakar meke faruwa, menene wnn suke fada, me ya kawo Ali cikin tv... Abba ya share kwallan da ya zubo masa ya rike Inna ya zaunar da ita saman kujera, yayinda Sumy ta rungume mamy tana ci gaba da kuka take fadin, " mamy wllhi wnn karya ne, Abba karya suke wllhi, yaHaidar bazai iya kashe muyum haka ba da zalunci, Abba kar kabari su kashesa.... nan fah inna ta fahimce komai.... haba basai ta mike ta hau zagagye parlorn tana salati tana kuka, hankalin Abba ya kuma tashi shi ka'dai ysakanin mata uku, haka aka wuni a hidan jigum jigum kaman gidan makoki, wasu daga cikin relatives dinsu da sukaji abunda ya auku a news nan fa aka soma yururwan zuwa jaje wasu suna waya, mamy kam ko iya daga waya batayi...

" Tunda wuri sukaji labarin amma suka kasa sanar da ita, gaba daya Hanifa ta rasa gane Anty Hiba da uncle faruq, wata zuciya taxe 'kila tausayinki suke, haka suka wuni basu bari taji labarin ba, koda Anty Hiba tayi waya da mamy, mamyn ma cewa tayi karta fa'dawa Hanifa tukunna

👸🏻Queen Samy😍💄💋........
[5/21, 5:49 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
63

"Isowarsu garin Apapa knn kai tsaye ya wuce ofishinsu, koda ya bu'kaci ganin Haidar sai ce masa akayi an tafi dashi prison sakamakon amsa laifinsa da yayi, Alkali ya yanke masa watanni uku a gidan yari kafin a shiga kotu a gabatar da shari'a, sosai hankalin Aisar ya tashi, yana fita bai zarce ko ina ba sai prison, nan aka shiga aka sanarwa Haidar yana da visitor....
Chapter 48 · 0% Book details