← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 73

Sashe 4

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tare suka fito har bakin parking lot, sale dreba na ganinsu ya taso da sauri yana fa'din hajiya ina kwana. Mamy ta amsa snn sale suka gaisa da Haidar ya kar'bi luggage 'dinsa gamida sawa cikin boot.
"Har ya shige mota mamy ta juyo tace karfa ka mance kubi asibitin ka duba Hanifa snn kayi sllama da Inna.
"A ta'kaice yace toh mamy insha Allah.... sann malam habu ya hangame masu gate suka fice...

"Tun shigowan Haidar cikin asibitin mata nurses ke binsa da kallo kakin nan ba 'karamin kar'bansa tayi kaman dominsa aka 'kera. Shi kuwa gogan yasan suna kallonsa dan haka ya 'daure fuskan nan tamau kaman baisan kalman dariya ba, hakan sai ya zame masa fashion, yana tafiya kana jin sautin tafiyan nasa irin ta mazaje cikakkun sojoji takalmin 'kafarsa ya 'kara ma tafiyan nasa sauti mai da'di da kuma kyau. Wani hanya Captain AA ya nufa ba mata kawai ba harta maza sai sunbi shi da kallo dan kuwa kwarjininsa da kyaunsa ya zarce bayani....

"Tana zaune tana shan lipton ya turo 'kofan gamida shigowa, bata 'dago kai ba dan azatonta nurse ne ko Dr. 'Kamshin turarensa ya tabbatar mata shine dan kuwa wann kamshin shine tamau a wardrobe dinsa jiya da take gyarawa, da sauri ta 'dago dan tabbatr ma idonta shi'dinne kuwa yana tsaye ya ha'de rai kaman baisn kalman dariya ba.
"Baki a cure tace inakwana yaHaidar sanda yake shigowa cikin 'dakin.
"Kaman bazai amsa sai kuma ya amsa a ta'kaice, gaban gadon da take kai ya 'karaso 'kirjinta sai dukan uku uku yake, a ranta take addu'an Allah sa ba kasheta yazo yi.
"Hannu yasa ya 'dago ha'banta yana mata mugun kallo. Ita kam kasa kallonsa tayi dan kuwa sosai yayan nata ke mata 'kwarjini snann ta tsane koda ganin fuskansa ne.
"Jin yanda jikinta ke karkarwa ya tabbatarwa Haidar Hanifa ta shiga makarantar ta nutsu, yayi wani murmushin mugunta kana yace" next time don't try to mess with me, wann ka'dan ne daga cikin irin horon dana tanadar wa marassa kunya irinki useless kawai me kamada mayu. Ta 'dago ido tana kallonsa ya daka mata tsawa "bar kallona da ido kaman na mujiya.
"A ranta tace ai naga da kai da Abba muke kama kaima kana kama da mayun kenan...

"Inna ce ta turo 'kofan bayin tana fa'din likitan ne ya shigo.... murmushi Haidar ya sakar mata sanda take goge fuska yana fa'din tsohuwa ko nazo na ri'keki ne kinsan jikinki babu laka yanzu kin tafi.
"Kaci gidanku Ali wannan 'kafa tawa da kake gani ras take gudun da zanyi ma bazakayi ba... Haidar sai dariya yake.. Hanifa kuwa cewa tayi a ranta mugu kawai ji kaman ba shi bane ya gama 'daure fuska yanzu...
" Inna taga yanda jikan nata yasha kyau cikin uniform dinsa ta wage baki tana fa'din "A a a kaga soji marmari daga nesa ta fa'di sanda take zama bisa sofa.
"Murmushi Haidar yayi ya 'karaso gamida gaida Inna.
"Badai yau zaka tafi ba dan nasan kana saka wannan inifom 'din naka toh tafiya ne zakayi ko zaka wani taro....
"Ya 'dan dara kana yace tshohuwa kenan kice baki son tafiyan nawa..
"Toh ai kaine idan ka tafi sai ka shafe rabin shekara mutum kullum a saman ruwa kaman kifi....
"Ya 'karaso gaamida ri'ke hannayen Inna yace ba jimawa zanyi ba tsohuwa wata shida kawai zanyi..
"Hanifa a ranta tace Allah sama karka dawo kayi zaman ka a can mugu kawai...

"hira sosai suka sha da Inna 'karfe 10:35 ya mike yana fadin to tsohuwa zan wuce kada na makara.
"Inna ta mike tana fadin toh bazaka ci wani abu ba... girgiza kai yayi yace "noo bazan iya cin abinci a nan ba it will irritate me beside am Ok ma...
"Baki inna ta hangame tana dubansa kana tace kaji dashi muje ni na raka ka.
"Ya murmusa yana wani ksahe ido yace "baki so wata ta kwace maki nine gashi tun shigowana 'yan matan ke bina da kallo.
"Dariya Inna tayita jawoshi jikinta tasan zatayi kewan jikan nata sosai da sosai.

"Suna ficewa Hanifa taja tsaki a hankali sann tace " harda wani wai bazai iya cin abincin asibiti ba hmm mtsw, ta kwai kwayi yamda yayi magana "no its irritating. Taja dogon tsaki kana tace Allah raka taki gona azzalumi kawai...

"Fitan Haidar da 'kadan su Shema suka shigo da uniform dinsu a jikinsu daga sch suke dashike friday ne...
"Gaba daya sukayi kanta suka ru gume Inna tace dan Allah kad ku 'karasata mana.
"Sumy baki a ture tace kai kakus we missed her a lot nefa.
"Sady ta riko hanunta tace baby sis how feeling now.
"Am fine now, Dr muke jira ya iso yayi discharging namu...., 'Danmasani ne y shigo yana 'ko'karin maida dariyansa ciki. Nan fahh Hanifa ta 'kule.
" kunnenta ya 'karaso yana ra'da mata "wayace miki a raina soja, gashi kinji a jikinki..
"A kufule ta ture shi tana fa'din eh 'din ina ruwanka.....
"Yana dariya yake fa'din um um yanzu zanyi waya na gayawa ya Haidardan yace komawa kikayi tsaurin ido a fa'da masa, jirginsu batayi landing ba yanzu zai juyo...
"Karki kula shi baby sis cewan Shema dake zaune gefenta....

"Sai bayan juma'a aka sallameta, suna zaune gaba 'daya a parlor Saif yayi sallama ya shigo...
"Wani 'katutun ba'kin ciki Hanifa tayi dn ba yaHaidar kawai ba harta abokansa ta tsanesu... bayan sun gaisa mamy take ce masa 'dazu Haidar ya wuce.
"Eh mamy munyi waya dashi dama naje asibiti duba jikn Hanifa ne akace mun anyi discharging nata...
"Ayya sannu da 'ko'kari Saif Allah bar zumunci....
"Hira suke ta'bawa da mamy dan Saif akwai surutu ba kaman abokinsa Haidar ba shiyasa ma suka saba da mamy sosai, gaba 'daya hankalinsa naga Hanifa daketa cin abinci kaman mai tausayin abincin.....

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/9, 6:10 AM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
09

"Tun bayan sallaman Hanifa a asibiti Saif kullum sai yazo gidan, sabo ne sosai ya shiga tsakaninsu dasu Shema amma Hanifa kam ko ka'dan ta'ki sakin jiki dashi tana ganin yazo ko suna zaune a parlor zata shige ciki abinta, har ranta ta tsane me tarraya da yaHaidar idan ka 'dauke 'yan gidansu.

*Lagos*......
_Maritime_.......
"Misalin karfe 5:30pm Haidar ne zaune a parlor dinshi bisa sofa, gabanshi laptop ne yana reserch gefe kuma kwalban wine 'dinshi ne yana danna laptop din yana sipping wine dinshi, a hankali ta turo 'kofan parlon ta shigo tana sanye cikin doguwar riga datake kamar a jikinta aka 'dinka dan yanda ya matseta, gashin kanta a bu'de as usual sai handbag dinta dake makale a hannunta na dama.
"Da mugun mamaki ya 'dago yana kallon Lateefa dake tsaye tana binsa da mayen kallon data saba, Sai sannan Haidar ya tuna ashe singlet da gajeren wando ne a jikinsa.... wani dogon tsaki yaja gamida mikewa ya nufi bedroom, idan da sabo Lateefa ta saba da halin Haidar na disgi dukda disgin da yake mata ko ka'dan bata jin sonshi na raguwa azuciyarta saima 'karuwa da yake yi after each and every second, tun ba yau ba ta sani Haidar is not womanizer ko ka'dan mata basa gabansa, dan kuwa tasha mi'ka masa kanta kyauta amma baya kulata saida ma suyi fa'da. Shi dai barshi da shan ruwan kwalba kawai, shima shan giya tafiyanshi navy ne ya soma sha dan acikin ko wani jirgin ruwa sunada bar dinsu mussaman na shan giya, wani 'kasar idan sukaje akwai sanyi sosai bararsar takan taimaka masu wajen warming temperature a cewarsu. tun bayaso har ya fara korawa daga haka ta zame masa jiki(Allah ka tsaremu ameen).

"Mintuna 'kadan Haidar ya fito cikin jallabiya fara kal sai ya koma tamkar balarabe, ya nemi waje ya zauna ba tare da yace da ita komai ba. Murmushi ta sakar masa gamida matsowa kusa dashi, dakatar da ita yayi ta hanya narka mata mugun kallo. Nan fa Latifa tasha jinin jikinta ta soma fa'din "haba Aliyu what have I done kuma, tun dawowanka fa bamu ha'duba nayi tafiya sai yau na dawo, and thi is how you welcome me. Haba Aliyu this is not fair fah...
"Cikin ko in kula yace "how many times do I have to tell you bana son ana zuwa mun gida without informing me, wama yace miki ki shigo min gida babu ko knocking in the first place hum.
"Ha'kuri Latifa ta shiga bashi gamida shagwa'be fuska, abun har yaso bawa Haidar dariya ganin yanda Latifa da suke kusan age mates amma sai wani masa shagwa'ba take _the thing no fit her at all 😕😂_.
" Da kyar Latifa ta samu ta lalla'ba Haidar bai koreta ba nan ta sanar dashi Dad dinta nason ganin shi... ya dago yana dubanta kana yace shi ya gaya maki na son ganina, ta gya'da kai alamaun eh... shiru Haidar yayi yana tunanin toh meye Naval chief of staff yake nemansa, tun dawowansa ya'ki su ha'du dukda shine musabbabin dawowansa hutunsa bai 'kare ba...
"A ina yace na same shi ya jeho mata tambayan?
"Yace a gida zaka sameshi by 8:pm..
"Nodding kansa Haidar yayi gamida tunanin wann secret meeting da Naval chief of staff yake so suyi....

"Karfe 8 daidai Haidar da Latifa suka nufo gidansu Latifa, tun daga gate sojoji ke sarawa su Haidar har suka 'karasa ciki.
"A parlorn ba'ki ta masa mazauni kana ta wuce ciki sanar da Dad 'dinta Aliyu ya iso.
"Latifa ita da mahaifinta kawai suke rayuwa cikin gidansu saiko ma'aikata, dan kuwa tunda mahaifiyarta ta mutu dad dinta bai sake aure ba ya 'dauki son duniya ya 'dora ma 'diyarsa wanda soyayyan nasu ni kaina Samy ina zarginsa dan kuwa kaman ya zarce na 'diya da uba kawai....
Chapter 4 · 0% Book details