← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 73

Sashe 30

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Tun safe take mur'kusoso a 'daki tana juyi tana kama mararta, shiru Latifa bata ji 'duriyanta ba har rana tayi, gashi ta mata iyaka da shiga dakinta, abun duk yadame Latifa ganin ko breakfast Hanifa bata fito tayi ba, da haka ta yanke shawarin shiga dakin dubota, "a sittin ta 'karasa ganin Hanifa kwance tana juyi tana kuka da 'kyar, 'dagota tayi tana fa'din sisy lafia what's wrong, are you sick. Kasa bata amsa tayi sai juyi take, tana 'dagota taga jini duk ya 'bata mata jiki.
"Taimaka mata tayi ta kaita har bathroom ta duba wnn ledan da ta shigo mata dashi ta ciro pad, ta kaimata snn ta dawo ta gyara 'dakin tsaf.
"Hanifa na fitowa taga har Latifa ta gyra wajen tas dashi, kwanciya tayi bisa gado ta du'kunkune, Latifa ce ta turo kofan ta shigo da ruwan lipton mai ha'din maganin menstruation pain , ta 'dagota tace maza tashi ki sha ga magani na kawo maki, girgiza kai Hanifa tayi alamun a'a.
"Cikin lallashi Latifa tace tashi kisha it will help you. Kinga nima da ciwo na knn tunda wata Dr ta bani shiknn na rabu dashi, kallonta Hanifa ta 'dan yi snn tasa hannu ta kar'ba, ta dan sha da 'dan dama, fita latif ta kuma yi ta shigo mata plate na abinci tasata ta dan ci, nan ta kwanta bacci yayi gaba da ita, ba ita ta farka ba sai wajejen la'asar.
"Sosai taji da'di data farka kaman bata period haka taji, ta tuna irin wula'kancin da tayiwa Latifa da irin tsanar da ta mata, Allah sarki ashe duk munin halin 'dan adam yana da good side dinsa, kawai saitaji duk babu da'di, dukda har yanzu tsnar Latifa na nan a ranta, mikewa tayi ta fa'da bathroom tayi wanka kadin ta fito parlor ta samu Latifa na kallo, murmushi Latifa ta sakar mata kafin tace "knn tashi, kai kawai Hanifa ta gya'da mata snn ta karaso ta zauna 'daya daga cikin kujerun.
"Ga abinci a dinning ko na kawo maki nan ne, cewan Latifa.
"Girgiza kai Hanifa tayi tace na 'koshi saiko anjima, em dama inaso nace maki kiyi ha'kuri bisa abubuwan dana maki a da.
"Murmushi Latifa tayi tace babu komai wllhi, ni yanda nake son Aliyu haka na 'dauke ki tamkar 'kanwa.
"Take annurin fuskan Hanifa ya 'dauke. Ta gyara zama tace, "dan kina sonsa shine kike basa kanki a matsayinki na 'diya mace, shi namiji bazai nuna ajikinsa ba sai ke, snn ko da aure kukayi ai bazai ganki da kima ba dan kuwa kin watsar da karama da mutunci da darajan da addinin islama ta maki.
"Sosai jikin Latifa yayi sanyi da kalaman Hanifa, tayi mamakin 'karamar yarinya da ita tayi wnn zurfin tunani.
"Ganin jikin Latifa yayi sanyi yasa Hanifa ta sami 'kwarin gwiwan yi mata wa'azi sosai harta yanayin suturun da take sakawa saida Hanifa ta mata wa'azi akansu. Ga mamakin Hanifa hawaye ta gani kwance kan fuskan Latifa. Nan taji tausayinta ya rufeta ta mike ta 'karasa kujeran da take ta ri'ke hannayenta tace" is not too late, ki ro'ki Allah ya yafe maki dan shi mai yawan afuwa ne da gafara wa bayinsa matu'kar tuba ta gaskiya sukayi.... " Latifa na kuka tace dole nayi kuka Hanifa, ko kinsan Haidar zina ba halinsa bane ni nayi seducing dinsa na ringa yaudaransa ina kwa'daitar masa kaina, tun yana korata yana hanani ban ta'ba gajiyawa ba har saida she'dan yayi mun jagora na jawo ra'ayinsa ya soma biye mun, amma wllhi ba halinsa bane hasalima baida budurwa baya kula kowa saini dana nace masa ba rana ba dare ba damina ba rani ba sanyi ba zafi, koda yaushe ina ma'kale dashi har na rinjayesa, kinga kuwa dole nayi kuka na cutar dashi, ni duk a ganina hakan soyayya ne..... kuka mai 'karfi ya kuma kufce mata.
"Daurwa Hanifa tayi dukda tausayin yaHaidar dataji lallai ya ha'du da makircin mace ne, ta rungume Latifa tana fadin kiyi shiru ki daina kuka, Allah zai gafarta maki idan kika rokesa gafara. Da kayr kukan Latifa ya tsagaita, Hanifa ta dubeta tace ki tashi kiyi sallah kinji ana kiran sallan la'asar, Latifa tace ai nayi duka tun asuba....
"Zaro ido Hanifa tayi da mugun mamaki tace, sallolin ne kika yisu tun asuba, Larifa tace eh haka nake yi kar commitments su mun yawa nazo ban samu nayi ba.
"Hanifa ta girgiza kai tace " babu abunda yake gaba da sallah, duk tarin commitments din da suke gaban mutum dole ne wajibi ne farillah ne na asali ba wanda wani zai iya 'dauke wa wani ba, Sallah itace ginshi'kin aikin mutum, Sallah itace za'a fara tambayan mutum akanta da zaran ya mutu, idan tayi kyau tofah dukkan ayyuka sunyi kyau idan batayi kyau ba tofah sauran ayyuka sun rushe, sallah dolene ko me kike yi da zaran lokacinta yayi ki daina kiyi sallah, babu aikin da ubangijinmu yake so kaman yin sallah akan lokacinta fa'din manzon mu S.A.W.
"Latifa tayi shiru tana kallon Hanifa yanda take kwararo mata bayani, snn tace toh knn sallolin da nayi kafin lokutansu su shiga basuyi ba knn. Hanifa ta gyada mata kai tace 'kwarai kuwa ba'ayin sallah alhalin lokacinta bai shiga ba, 'karamin yaro wanda shari'a bata hau kansa ba, mai bacci mace me jinin bi'ki ko al'ada da mahaukaci sune sallah ta sauka akansu, snn shi me bacci da zaran ya tashi koda lokacin sallahn ta fita to zai rama wnn sallahn kafin yayi wacce lokacinta ya shiga, misali mutum na bacci lokacin azahar ya wucesa bai farka ba sai lokacin da ake sallan la'asar, toh ba la'asar zaiyi ba azahar zai fara yi kafin yayi la'asar din.
"Latifa ta jinjina kai tace na fahimta, yanzu barin tashi na biya sallahn azahar snn nayi la'sar, kuma insha Allah bazan sake yin haka ba. Na gode sisy na Allah ya saka maki da alkhair. Murmushi Hanifa tayi tace ai babu komai Anty Latifa yima wani ai yima kaine. Shgewa latifa tayi tayi sallolinta ta fito ta samu Hanifa tace sisy idan bazaki damu ba muje kasuwa mu sayo littafan addini ki rin'ka koya mun don na gyara ibada na.
"Hanifa ta zaro ido waje tace "kuji Anty latifa dai kin 'dauka ni 'din malama ce, Latifa tace 'kwarai kuwa saidai bazaki koya mun ba, ki taimaka mun pls kinga ni'din marainiya ce babu uwa na tashi snn mahaifina bai bani lilmin addini ba sai na boko, tun a primary da ake mana IRK na tsnci wasu abubuwa snn kinga yanayin environment din dana tashi pls ki taimaka mun kema Allah zai taimake ki.
"Sosai Hanifa taji tausayin Latifa sai yanzu ta gane ashe harda rashin sanin addini ne yasa Latifa shiga wani yanayi na rayuwa, amma ko babu komai tanada good heart snn insha Allah zata taimaka mata da iya 'dan abunda ta sani..... "kinyi shiru sisy "are we good to go, pls don't say no. Murmushi Hanifa tayi tace na yarda zan koya maki dukda nima 'daliba ce, yanzu ki kira yaHaidar kice masa zamu fita.
"Rungumeta Latifa tayi tace na gode sisy barin kirasa, ta kira numbern Haidar yafi abunda yafi amma baya shiga, ta dubi Hanifa tace 'kila suna wajen da babu network. Hanifa tace is possible yanzu dai muje kafin dare yayi idan yaso koda mun dawo sai ki masa waya ki fada masa. Haka suka fice Latifa taja su a motanta kirar 4matic E350, gwanin sha'awa suna tafe suna hira, Hanifa tayita mata hiran su mamy dasu Inna... a haka suka isa kasuwan suka sayo litattafai irinsu Akhadar, tauhidi hadisi da sauransu. Har karatun 'kur'ani Hanifa saida ta koyawa Latifa, kan sati ya zagayo Latifa ta soma picking, kama daga wankan tsarki hada baki alola da sallah duk saida Hanifa ta nuna wa Latifa yanda ake yinsu.
"Sai yanzu ne wani wasan mahaifinta yake da'da tasiri a ranta, hakika ya cuci rayuwarta Allah ne kawai zai mata sakayya. Ya kirata yafi sau nawa bata dagawa wani mugun tsanarsa take ji, batajin zata iya ci gaba da rayuwa dashi
"Yau suna zaune bayan sun gama karatu suka kunna kallo, Latifa tace inga fa cikin satin nan su Aliyu zasu dawo.Saida gaban Hanifa ya fa'di wanda ta rasa dalilin hakan, tayi murmushi on the contrary taji da'din zancen. Tana son ganinsa.... aiko suna cikin zancen wayan Latifa yayi 'kara... ta 'dago da murmushi tana duban Hanifa tace kinga 'dan halak muna zancensa ya kira. Nan Latifa ta 'daga suka gaisa ya shida mata gobe zasu iso lagos insha Allah, Hanifa kam wani 'katutun ba'kin cikine ya tokare mata ma'koshi, ta rasa gane kishi ne ko me.
"Ta mi'ke kawai zata wuce daki, sai jiyo muryan latifa tayi tana fadin gata nan barin bata, alamun YaHaidar ya tambayeta knn, da sauri tace "no pls ki gaishesa I want to use the bathroom, Latifa ta gyada mata kai snn tace da Haidar ta tashi bata kusa saidai ka kira later, jikim Haidar ya basa haushi Hanifa taji dan yasan halinta sosai by now.
Chapter 30 · 0% Book details