← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 73

Sashe 29

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*Washe gari*
"Misalin 'karfe 9:11am ya gama shirins tsaf cikin kakinsa, ya fito bai ganta a parlor ba, yasan hakan nada la'ka da fushin da tayi jiya. A hankali ya tura 'kofan 'dakin ganimta yayi kwance bisa gado ko wanka batayi ba, tana jinsa ta rufe ido wai ita a dole bacci take.
"Zama yayi gefenta, sassanyan kamshin turarensa ya daki hancinta.
"Nasan ba barci kike ba, so is better idan kika tashi mukayi sallama, who knows ko bazan dawo ba, kinsan yanda yanayin aikin namu yake.
"Last statement dinsa ne yasata mi'kewa ta zauna, kallonta yayi na dan lokaci kafin yace, " meya hanaki tashi kiyi breakfast, baki a ture tace "ba komai, I don't feel like eating. Kallonta yake da muhun mamaki wai dma ta iya fushi haka. Mikewa yayi ya nufi 'kofa ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace, "make sure kin tashi daga bed din nan kinyi brush kafin na dawo. Bai jira cewanta ba ya fice.
"Tabi bayansa da harara wani haushi ta kuma ji, duk ranta ya jagule. Mi'kewa tayi ta wuce bathroom tayi yanda yace.
"Tana fitowa daga bathroom din ya shigo hannunsa dauke da plate da mug, jiuewa yayi bisa bedside, fuskansa babu walwala yace oya zoki zauna, babu musu ta 'karaso ta zauna, sai kallon shara'banta yake 'kasa'kasa,
"Tea da bread ne ta shiga ci kaman bata so, saida ya tabbata taci sosai, ya mi'ke yana kallom agogonsa yace "zan tafi yanzu, Phillips zai kawo maki shopping na gida anjima, wata leda ya mika mata yace ga wnn naki ne. Kaman bazata kar'ba ba sai kuma tasa hannu ta kar'ba, trolley dinsa ya shiga ja har zuwa 'kofa, saida ya kai daidai 'kafa ya juyo yana kallonta, murmushi ya sakar mata yace Allah sadamu da alkhairi.
"Kasa komai tayi sai kallonsa da take, har ya fice tana jin karan footsteps dinsa daga stirs. Da sauri ta karasa window daidai lokacin Phillips na bude masa mota, kaman ya sani ya dago kai yana dubanta, hawaye na zuba a idonta wanda ta ras gane dalilin zubansa nan ta shiga daga wa Haidar hannu, murmushi yayi ya daga mata hannu hadi da wurga mata kiss snn ya shige mota saida taga ficewarsu snn ta dawo ta zauna jiki a mace....

👸🏻Queen Samy😍💄💋....
[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
45

"Wani sabom kukan ta shiga rusawa wanda ta rasa gane dalilin yinsa, tafi 1hour tana zaune a wajen tana aiin abu 'daya, idanunta duk sunyi ja sun kubura haka nan fuskarta ma tayi jajazur.
"Tana zaune a wajen taji ana danna bell, kasa tashi tayi ta bu'de, saida me danna bell din ya gaji ya shiga 'kwan'kwasa 'kofan, a kufule ta mi'ke ta nufi 'kofa, ganin Latifa ce yasata jan dogin tsaki ta koma cikin parlorn tayi zamanta, Latifa dai bata cemata komai ba, ta kar'bi kayan hannun Phillips dan dama tare suke, ta masa sallama ta shige da kayan kitchen, har lokacin Hanifa na zaune tana goge ragowar hawayen idonta.

"Zama Latifa tayi a gefenta, ta soma magana a hankali cikin sigan rarrashi," Sisy pls kiyi ha'kuri ki daina kuka, yayanki ba jimawa zaiyi ba dazaran sun gama abunda sukaje yi zai dawo, ki daina damuwa I'll be here for you,..... wani uwar harara Hanifa ta sakar mata gamida jan dogon tsaki snn tace "dalla malama ina ruwanki dani ce maki akayi kukan rashinsa nake, idan yaga dama ma kar ya kuma dawowa mana as far as zai maida wajen iyayena da 'yan uwana masu 'kaunana, kin wani kwaso 'kafa kinzo dan asara ke ko kunya ma bakyaji kirin'ka bin saurayi har gidansa kuna alfasha..... "Enough! Latifa ta daka mata tsawa, nan kuma ta tuna hu'duban da Haidar yayi mata kan cewa tayi ha'kuri da Hanifa ta ri'ke masa ita amana har yaje ya dawo snn idan son samu ko 'kuda baiso ya ta'ba jikin Hanifa kan ya dawo..... Saita kanta tayi 'ko'karin yi, Hanifa kam tuni ta wuce 'daki ha'di da banko 'kofan.

"Latifa ta sau'ke ajiyan zuciya dan kuwa tasan tabbas zamansu da Hanifa akwai rikici, dole ta shanye duk wani wula'kanci saboda son Haidar da take yi. Mi'kewa tayi ta wuce kitchen ta 'daura masu lunch. Snn tayi sorting out kayan da Phillips ya kawo. Bayan ta dawo parlor ne yanda Hanifa ta tashi taga leda ajiye a wajen, 'dauka tayi tana bin ledan da kallo kafin ta shiga bu'dewa, pads ta gani da magunguna ta 'dauka ta wuce 'dakin Hanifa kai tsaye ta shiga knockn, sanin ko zata kwana wajen tana 'kwankwasawa ne Hanifa bazta bu'de ba yasata murda handle din kofan a hankali snn ta shige.
"Zaune ta sameta gaban dressing mirror tana 'daura dankwali, murmushi Latifa tayi ta 'karasa ta zauna a bakin gado tana kallon yanda Hanifa ke 'daura 'dankwalin, saitaji sha'wan atampa tunda ita kayanta english wears ne akasari, cikanki Hanifa bata ce da ita har ta gama abunda take. Latifa ta 'danyi gyaran murya tace " sisy am sorry regarding what happened earlier, dan Allah kiyi ha'kuri mu zama friends mu rin'ka cin abinci tare muyi ta'di tare pls kinji.
"Wata harara Hanifa ta galla mata kafin tace " wama kike da suna, barin fa'da maki nafi 'karfin zama 'kawar karuwa, ke nifa kin dameni shi wanda yace kizo gidan ki zauna kiyi zaman dan shi mana, amma ni dan Allah ki daina shiga hidimata... daga haka ta juya ta fice ta bar mata 'dakin. Latifa ta ha'diye bakin cikinta dan kuwa kalaman Hanifa sun mata zafi. Ajiye ledan tayi ta fice daga 'dakin ta wuce kitchen ta karasa girkinta. Hanifa kuwa na zaune a parlor ta har'de 'kafafu tana kallo, idan Latifa ta giftata taja dogon tsaki tate da jifa mata harara.
"Koda Latifa ta mata tayin abinci banza da ita tayi kaman batasan da wata halitta a wajen ba. Haka suka shafe kwana kisan biyar a haka. Haidar yayi wayada Latifa ta sanar dashi lafia suke zaune duk dan ta samu soyayyan Haidar.
Chapter 29 · 0% Book details