← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 73

Sashe 38

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Misalin karfe 1:15 pm, momma na rungume da Amal dake faman kuka tana daga wa daddynta da Hanifa hannu a babban filin jirgin saman Murtala Muhammed international airport. Saida suka bace masu kafin suka juya suka shige mota, har suka shiga jirgi Hanifa na matsan hawaye, Barrister ya mi'ko mata hanki, ta dagi tana dubansa kafin ta sakar masa murmushi ta kar'ba, daidai lokacin aka soma announcing jirgi zata tashi, cikin mintoci jirginsu ta daga zuwa jhar kano.....

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
54

"Bayan la'asar Haidar ya 'dan samu strength ya tashi, waya yayi wa Saif yaji ina yake, Saif yace ya fita ba jimawa zaiyi ba amma, Haidar yace ok shiknn ni zan 'karasa gida, Saif yace just wait bit longer ganin nan zuwa Haidar. Fajeren tsaki Haidar yadan yi yace " kana ina ne yanzu, nan Saif ya fada masa street din da yake, Ok zan sameka a wajen, fine sai ka iso.

"Gefen wani shagon aski me kyaun gaske Haidar yayi parking, ya jingina kansa jikin seat yana jiran Saif, kaman ance daga kanka, a daidai traffic ya hango wata bayan taxi kaman Hanifa, zabjra yayi ya kuma goge idonsa dan tabbatrwa, daidadi lokacin Saif ya iso yana fadin mu 'karasa soldier..... Nuna masa motan Haidar ya shiga yi yana fadin " Saif look at that car... Hanifa ce ciki, ka shigo mu bi bayansu za'a basu green light... Saif yace Ok barin shiga motata.... bude mota Haidar yayi ya jawo Saif ya danna sa ciki ya shiga falfala gudu, haka ya rin'ka rough driving dasu kar motar ta 'bace masu, ganin sun 'dau street din unguwarsu yasa Haidar sassauta gudun da yake.
"Taxi din tayi parking daidai gate din gidan Abba, Haidar ma parking yayi a gefe, Sameer ne ya fito daga gaban motan yana murmushi ya zagayo ya bude wa Hanifa, fitowa tayi fuskanta dauke da murmushi, aiko Haidar ya zabura zai nufe su, Saif yayi saurin ri'kosa.
"Taxi driver din ya fito ya bude trunk ya ciro luggage dinsu Sameer ya kar'ba, snn ya wuce, sai snn Hanifa ta lura da motar yaHaidar dake parke a gefe, nan ta kuma jin wani mugun tsanar sa na taso mata, murmushi ta sakar ma Sameer ta soma masa labari suna dariya suka nufi cikin gidan kaman wasu masoya,
"Kan su shige suka ji an finciko Sameer, ya dawo baya, wata naushi Haidar ya sakar masa a hanci saida yayi ha'bo, Ya cukume wuyan Sameer yana fadin munafukin Allah me ya hadaka da matata, " Saif ya shiga jan Haidar yana fa'din pls Haidar behave yor self meye haka kake yi.
"Cikin ki'dima Hanifa take kallon Sameer cike da damuwa, tayi saurin ciro hanki ta mi'ka masa, oh Allah you're bleeding ko asibiti zamu, it hurts ko, kayi ha'kuri mahaukaci ne ba me lafiya bane, mu 'karasa ciki kafin haukan nasa yayi tsamari..... Da mugun mamaki Haidar ke kallon Hanifa, gani yake kaman ba ita ke maganar ba,.... muryan Sameer ya dawo dashi daga duniyan tunanin da ya tafi.... " no no kar ki damu basai munje asibiti ba, amma ko ai bai kamata ake barin iri wadnn mahaukatan ba sai su illata mutane, kamata yayi a killacesa a asibiti cewan Sameer, Hanifa ta ta'be baki tace ai ya jima a asibitin mahaukata inaga ya gudo ne, mu 'karasa ciki pls..... suka nufi cikin gida tana faman masa sannu.

"Kaman gunki haka Haidar ya tsaya yake binsu da kallo har suka 'bace masa, Saif ya dafa sa yace mu 'karasa ciki... Haidar ya juyo da dubansa ga Saif snn yace " didn't you hear what they said, wato mahaukaci ma suka dauke ni, yes am going crazy about you Haneefah, Saif yace duk ba wnn ba yanzu mu 'karasa ciki, Haidar jiki a mace yace "Saif matata nake gani da wani har tana fifitasa akaina, Saif yace pls Haidar let's get going.

"Tarba me kyau Abba da Mamy suka ma Sameer, sai haba haba suke dashi harma da Inna wacce take ji kaman ta dau zani ta goya Sameer, Hanifa na ma'kale jikin mamy sai zuba mata shagwa'ba take, Mamy inasu Sumy ne ban gansu ba, mamy tace Sumy tana faman registration a nan BUK, Sady kuma jiya muka kaita ABU, amma anjima kadan Sumayya zata dawo.... daidai nan Saif da Haidar suka yi Sallama.
"Gaisuwan Saif kawai Abba da mamy suka amsa inna ma harda basar da Haidar kaman bata san ya shigo ba. Sameer ya mike yana fadin toh Abba ni zan wuce masauki, Abba yace aff ko abinci baka ci ba a'a haba dai, ka saki jikinka Barrister nan gidanku ne, a ina ne masau'kin naka.
"A'a dama hotel zan wuce Abba, Sameer ya fadi,
"Haba Barrister dan Allah ka dauke mu tamkar iyaye, a nan zaka sauka babu batun zuwa Hotel, cewan Abba. "Haidar sai satan kallon Hanifa yake, itama ta saci kallom nasa yanda taga yayi rama kaman me cuta.
"Abba ya dubi Saif yace "Saifullah ga key din guest room a can maza 'dauka ka raka sa, Saif ya mi'ke yana fadin toh Abba ya karasa ya dau key din Sameer ya mike yana godiya, su Abba suka ce " haba ai mune da godiya ka isa ka huta yanzu za'a kawo maka abinci.

"Mamy ta mi'ke tana fa'din barin ha'da masa abincin, Hanifa ta mike tana fadin I'll ho with you mamy. Abba yace zauna daughter zamuyi magana. Zama tayi tana fadin toh Abba, Abba ya dubi mamy yace jeki dawo Mariya magana zamuyi. Mamy tace toh I won't take long kafin ta wuce cikin sauri.
"Haidar da har lokacin yake durkushe yana satan kallon Haneefah, ya hango dan sauran bandage a goshinta take yaji gabansa ya fadi "Oh Allah me ya sameta. Inna ce tace meye kake wani satan kallonta hankalinka yanzu sai ya kwanta tunda ta dawo, shafa kansa yayi ya mi'ke yana shirin fita muryan Abba ya dakatar dasi, "ina zaka je, dawo ka zauna. Ba musu ya dawo ya zauna.

"Mamy ce ta shigo tana fadin daughter ko zakici abinci yanzu ne, no mamy sai nayi wanka. Mamy ta karaso gamida jawo Hanifa jikinta.
Chapter 38 · 0% Book details