← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 73

Sashe 61

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sa'daf sa'daf ya fito ya hangi wata 'kofa a bu'de, a saba'in yasa kai zai wuce, sai ji yayi anyi pointing bindiga akansa ana fa'din surrender or I'll shoot, ai a tamanin Lawo yayi jifa da mum din Latifa zai arce " daya daga cikin sojojin yana fadin " freeze stop inaaa Lawo yasa kai... ji kake pammm an fasa kan Lawo. Da sauri suka karasa wajen aka dagasa,
"Mum din Latifa kuwa juyi ta soma yi kaman wata guguwa, can ta fadi gefe guda, su kansu sojojin nan saida abun ya razana su, wa'enda suka santa da farko arcewa sukayi niyyan yi dan a ganinsu fatalwa ce ta dawo, a iya saninsu ance masu ta jima da mutuwa sai gashi yau sun ganta da 'kafafunta, babban abun da yafi razanasu shine yanayinta ya canza gaba 'daya, gashin kanta duk ya damfare kaman dada, snn wasu jajayen kaya ne a jikinta, fatan jikinta kuwa duk ya tattare ya jeme.
"Securities suka rikota suka zaunar da ita, da farko ihu ta soma masu can sai ta soma fadin, ina Tanim kunkaini wajen sa na ro'keku.....

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
75

"A hankali komai yake dawowa mum din Latifa sanda suke tafe cikin mota, kuka take kaman ranta zai fita dan agabanta Tanimu ya kashe diyarasu, "Drivern mota gudu kawai yake shararawa dan akwai tazara sosai tsakanin gidan zuwa kotu.

"Barr Barnabas yaci gaba ds fa'din" ya me shari'a da wnn hujjoji da suka gabata a gaban kotu nake ro'kon wnn kotu me alfarma da ta yankewa captain AA irin hukumcin data dace dashi na gode ya me shari'a, daga haka ya koma ya zauna, Admiral kaman ya zuba ruwa a 'kasa yasha dan murna.
"Al'kali ya sunkuya yayi rubutu kafin ya 'dago kai ya soma fa'din" bisa ga hujjoji da suka gabata agaban kotu, da rashin ta'kamemmen hujja wanda zai tabbatar Captain AA bashi ya aikata laifin ba, snn a ranar 21 ga watan January captain AA ya amasa laifinsa cewa shi da kansa ya kashe marigayiya Latifa snn an samu gawanta a cikin gidan Captain Abubakar, dan haka wnn kotu me alfarma ta yanke wa Captain AA hukuncin 'daurin rai da rai ta hanyar rataya kaman yanda yazo a 'kundin tsarin mulki 1999........Admiral baisan sanda ya shiga sarawa barr Barnabas ba " inna lillahimwa inna'laihirra'jiun Sameer cire malfar kansa na lauyoyi kawai yayi Sady da Sumy rungume juna kawai sukayi suna kuka."Al'kali na shirin mikewa kawai sai ji sukayi an bu'de 'kofan kotu......" Jikin Admiral ya 'dauki karkarwa haka su Dad din Aisar da duk wanda yasan mum din Latifa...." jiki na 'bari Admiral ya isa gabanta yana fadin "ke wayace ki fito waya dawo dake wnn duniyan..." Aifa kallo ya koma kansu," mum din Latifa tace" Allah mahallici na mahallicinka wanda ya haramta zalumci shi ya dawo dani wnn rayuwa, Allah bazai barka kaci gaba da aikata zalunci ba yau 'karshen zaluncinka ya zo," ta shiga nuna sa da yatsa tana fa'din ka cuce ni Tanimu ka kashe 'yarka ta cikinka a gabana ka mallakani wa bokanka...." Malikaaaaa me kike cewa "ya me shari'a kark yarda da wnn matan fatalwa ce ta jima da mutuwa wllhi fatalwa ce...
"Al'kali ya buga benchi silence..... kowa ya koma wajen zamansa ya zauna, haba nan fah Admiral zufa ta shiga ysatsafo masa hakama dad din Aisar, Admiral yana 'ko'karin mikewa Chief of defense ya narka masa wata kallo kawai a saba'in ya koma ya zauna. Da yawan mutanen dake cikin kotun sun razana da ganin mahaifiyar latifa gaba daya suffanta ya canza kamar wata hallita.
"Mum din Latifa ta 'karaso gaban Haidar hawaye na bin kuncinta ta soma fa'din ko bansani ba kaine Haidar, kaine mutumin da matarka ta ceco 'diyata daga halaka na wnn azzalumin mutumin, matarka ta fito da latifa daga duhu zuwa haske, snn kaine Tanimu ya la'kaba maka sharrin ka kasheta saboda tsoron kaine zaka fasa abunda yayi shekara da shekaru. Hawayene kawai kebin kumatun Haidar..
"Ta juyo tana kallon me shari'a kafin tace ya me shari'a a yau zan bayyana mummunan aiki na wnn azzalumin bawa, " ta juya tana nuna Admiral da tuni ya soma sakin fitsari a jikinsa kafin tace" Wnn mutumi ya aurani wa bokansa shekara da shekaru, bana cewa um bana cewa um um amma kuma ina sane da duk abunda ke faruwa, wnn mutumi ya mayar da 'diyarsa Latifa tamkar matarsa ya lalata mata rayuwarta wnn mutumi shi ya kashe tsohon kwamandan rundunar sojan ruwa dan ya maye gurbinsa wnn mutumi shi ya kashe mun 'diyata a gabana...... kuka ya kufce mata. " Dan'kari ma'kari, kotu tayi tsit sai sautin kukan mum din Latifa kawai kakeji, da yawan mutane mamakin irin laifukan Admiral da aka zayyano suke, anya wnn mutum ne lallai wnn shime babban shedan.
"Al'kali ya 'dago cike da 'dunbin al'ajabi kafin ya furta " kotu tana bu'katan Naval Chief Of Staff da ya shigo cikin Akulkin tuhuma...." Admiral ya soma 'bari yana fa'din ya me shari'a kar ku yarda da wnn matan ta jima da mutuwa fatalwa ce kawai ta fito... tsawan da aka daka masa yasa yin tsit jiki a mace ya nufi gefen Haidar..." wata mirmushi kawai Haidar ya sakar masa sanda ya tsaya a gefensa.
"Alkali ya soma fa'din" Admiral kaji abubjwan da iyalinka ta zayyano akanka, shin ka yarda ka amsa laifinka kokuwa....
"Admiral kam ganin ta tashi masa yasa duk ya susuce, bai ankaraba ya hango dad din Aisar na 'ko'karin warewa. Da sauri ya nunasa yana fadin ga dayan can zai gudu, Dad din Aisar ya soma fadin" ni kuma me ya hada ni da kai ni babu hannuna cikin mutuwan 'yarka nida ka kamamun mata kasa 'dana bada shaidan 'karya dan kar..... Admiral ya soma fadin karya kake kai ka kawo wnn shawara dan kar asirinka ya tonu abunda kayi shekaru talatin baya kisan Barrister Ridwan Marafa da kayi...... "Ai bai gama rufe baki ba Aisar yayi wata tsalle ya dun'kule hannunsa bai tsaya ko ina ba sai fuskan Dad dinsa ya kai masa wani wawan naushi naushi duk tarin mutanen da suka taru suna ri'ke Aisar ina bai ko sairaresu ba dukan Dad kawai yake da iya 'karfinsa yana fa'din " you blackmail me you monster.... "Dad ya dago kai yana fadin" Aisar kar ka yarda dashi 'karya yake maka... inaaaa Aisar baiji bai gani dukan Dad dinsa kawai yake ya cukume wuyansa yana fa'din am gonna kill you invincible ina ka kai mun mum dina ina mum takeee..." fuskan dad duk jini yake fa'din tana guest house dinshi tana guest house din Admiral..... " A tamanin Aisar ya fice daga kotun..."( jama'a gaba 'daya kotu ta rikice😳) dole Al'kali ya bada hutun rabin lokaci abubuwa su daidaita tare da bada umarnin a tsare Admiral da Dad din Aisar.

"Hanifa tana farkawa sunan yaHaidar kawai take kira, mamy da Inna suka nufota bata tsaya sajrarensu ba dan kuwa komai ya dawo mata, fincike drip din hanunta tayi mamy ta fito a guje ta samu Dr da Abba suna magana.... ai suna ganinta a haka suka nufo ta babu shiri, da kyar mamy ta iya furta ta tashi she's out of control..... a sittin suka koma 'dakin gana 'daya, suka tarar Hanifa sai 'karamin ya'ki take da inna ita fa a barta taje taga mijinta, zasu kashesa, Abba ya ri'keta sosai yana fa'din" calm down Hanifa, ki nutsu nace, baki da 'koshin kafiya..." Abba yaHaidar dan Allah Abba kankaini ni wllhi lafiyata lou, ku kaini kafin nima na mutu dan Allah Abba, Abba wallhi bazan iya tsayuwa a nan ba ba tareds sanin halin da yake ciki ba, Abba ku taimaka mun...."Abba ya dago ya kalli Dr, girgiza kai Dr yayi yace ku kaita ta ganshi ko zata samu sau'kin ra'da'din da takeji.

"Aisar na fita Cheif of defense yasa wasu securities su bi bayansa don taimaka masa suka nufi guests house din Admiral.

"Captain Paul ne ke tsaron mum din Aisar, daya daga cikin yaran Admiral da yaga abunda ya faru a kotu wanda yake tamkar film ai tuni ya shiga neman layin paul, paul na dauka iskil ya labarta masa komai yace gwara yasan nayi ta tashi masu. A a tamin paul ya katse kiran, ya juyo ya kalli mum din Aisar da suka 'daureta matsowa kusa da ita yayi yana raywa a ransa da yayi biyu babu shiba da samun ku'di ba shi da shan wahalan banza ai gwara ya huta da matan nan.
"Matsowa yayi ya shiga shafa fuskanta, "mum ta tsatta masa yawu cike da tsana, kifa maya mari yayi ya shiga cire kayan jikinsa.... da jajayen idanuns Paul ke kallonta kafin yace zaki yabawa aya za'ki zaki san wa kika tsatta ma yawu.
"Mum na kuka take fadin Allah shi zai fitta dani daga sharrinka, shi zai 'kwace ni a hannunka... " Paul ya fizga 'dankwalinta kokawa suka shiga yi d mum yana 'ko'karin jan rigarta kawai sai jin an daki 'kofa sukayi......" Kan uban can..... wani kukan kura Aisar yayi ya haye kan Paul, dukan filin ya'ki kawai yakewa Paul, Mum me zatayi banda murna, ta dauki mayafinta ta rufa, har lokacin Aisar bayaji baya gani dukan paul kawai yake kaman an aikosa, Securities suka 'karaso suna fadin let us handle over captain...." suna jan Aisar Aisar be fasa dukan ba yana fa'din" let me kill this Animal let me finish him, he is not getting away with this......" Haka Paul ya koma tamkar baya numfashi, Aisar ya masa lilis.... " 'Dagowa yayi yana kallon mum dinsa rungume juna sukayi suna kuka me tsuma zuciya, nan securities suka tasa ke'yan paul aka wuce dashi....

👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
76
Chapter 61 · 0% Book details