← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 73

Sashe 58

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
72

*This chapter naku ne masoya littafin mijin haneefah, ina matukar jin da'din yanda kuke biye dani a wann littafi nawa ILYSM❤*

" Aisar ya tattaro nutsuwarsa ya fuskanci mahaifinsa yana sauraren me yake cewa.
"Son, tun tasowarka we never spend much time together, I haven't been a good father to you and I treated you badly, muryan dad ya soma rawa, until now I still can't forgive my sef..... "da sauri Aisar ya matso kusa dashi jiki a sanyaye ya rungume mahaifinsa yana fa'din" please dad stoo saying all this, besides yanzu muna tare gana daya ni kai and mum, and we're living a happy family, this is our dream, gashi Allah ya cika mana burinmu, mum is happy now, you are still my only Dad no matter what, and I love you dad, I'll do everything to pleased you.
"Dad ya dago kai yana kallon Aisar kafin yace" shiyasa nake ga ya kamata mu tafi hutu koda na sati biyu ne, mu mance da wani stress na aiki da saurnsu, let's spend time together and know each other well. Ko yaya ka gani Son, please don't reject my offer, kar ka mance ban ta'ba tambayan ka mun wani abu kaman haka ba, please son.....
"Girgiza kai Aisar ya soma kafin yace" Dad ba wai ban son tafiyan bane this is not the right time, am busy now, besides kasan yanayin aikina it will affect my job idan nayi tafiyan...
"Ka bar zancen aiki Son, idan kaso ko yanzu zaka iyayin ritaya ni na tara maka abunda zaka bu'kata na cash har 'karshen rayuwanka dama zuriyan da zaka haifa, please son let's leave this place for a while..
"Dad try to understand me, bazan iya tafiya na bar Haidar ba a wann situation din, snn maganar aiki kuma sai yanzu nake da'da jin son aiki na, am proud to be Navy Dad, am sorry but I can't leave right now, why not ka bari some other time sai muje, zan dauki hutu sai muje where ever you want us to go...
"Haba nan fah hankalin Dad ya soma tashi, dan gaba daya ya kasa samun goyon bayan Aisar..... " A fusace ya mi'ke yana nunasa da yatsa" kai bakayi girman da zan saka abu ka 'kiyi ba, dan haka dole ka bini mu tafi ko kana so ko baka so, ni bazan tsaya a 'kasan nan ba, abubuwa suna neman kwa'bewa, Aisar saboda kai nake son mu tafi muyi nisa daga nan, na hanaka sa kanka cikin shari'an yaron nan ka 'kiji ka 'ki gani, toh wllhi dole ka bini mu tafi, I don't care about your so called job, na riga na tara maka ma'kudan ku'di you are my only son bazan iya zama inaji ina gani na rasa ka ba...... " Haba Dad meyasa kake fadan irin wadan nan kalaman, kai da bakinka kace mun ka canza, gashi yanu ina ganin akasin haka....." Ran Aisar yayi matu'kar 'baci, jijiyoyin jikinsa suka yi ra'da ra'da idanunsa sukayi jazur, ya matso kusa d Dad yana girgiza kai yake fad'in" no no I can't do that, bazan iya tafiya na bar Haidar ba, mutumin da ya zamar dani mutum, mutumin da yayi sanadiyan rabuwata da shan giya, mutumin da yayi sanadiyan rabuwana da bin mata, mutumin da ya rescuing live dina lokacin da kayi abandoning dina, and last kar ka mance he's the reason why am here with you today, yanzu yana gidan yari akan laiffin da be aikata ba and you're asking me to leave him all alone, no Dad think of..... " Enough Aisaaar, Dad ya daka masa tsawan da yasa mum ta fito babu shiri, " Barin fa'da maka like it or not dole mu bar kasan nan har sai al'amura sun daidaita, dan haka tun kan ranka ya 'baci ka kawo mun passport dinka...... " Cikin tsan tsan 'bacin rai Aisar ya soma fa'din" don't tell me you have something to do gameda abunda ya samu Haidar Dad, ka fada mun dad are you behind this..... wani wawan marin da dad ya kifa masa ne yasa yin shiru hade da dafe kuncinsa..... mum ta karaso tana fa'din haba haba Alhaji wai yaushene kai da Aisar zaku zauna 'karkashin inuwa guda, haba haba.... " Ranar da 'danki ya gane cewa I'm his father and I've every right for him, na baku kwana biyu rak keda 'danki ku shirya mu bar 'kasan nan daga haka ya wuce ya barsu tsaye a wajen.
"Mum ta rungume Aisar tana lallashinsa, zama sukayi bisa sofa mum na duba fuskan 'danta yanda aka sharara masa mari, saida yatsun dad suka fito. Da sauri ta dauko iceblog tazo tana danna mas wajen, "Son kayi hakiri pls kasan halin dad dinka ka ringa binsa a sannu.... " Haba mum yaushene dad zai gyara halinsa, tunda naga yana acting strangely nasan wani abun yake shiryawa, kuma wllhi babu yanda zanje bincike yanzu na soma, idan da hanunsa akan abunda ya samu Haidar he must pay for it...." Enough ya isheka haka, mahaifin naka kake fadan abubuwa akansa, ni na gaji da wnn hali naku Aisar, dole mu tattara mu tafi idan hakan zai zame mana sau'ki daga haka itama ta mi'ke ta bar parlorn, kallo kawai Aisar ya bita dashi har ta haye sama....

"Ana gobe su mamy zasu tafi Hanifa tayi bleeding sosai sida ak kaita asibiti, Dr yace dole ya riketa a asibiti na ysawon sati guda dan tana bu'katan hutu damuwa ya mata yawa, snn tana risk na rasa babyn dake cikinta, wai karkaso kaga tashin hanakli wajen su mamy, gaba daya hankalinsu y tashi dukda Abba yaso su tafi tare amma wann matsala da ya auku yasa dole su barta da Inna anan, sosai Abba ya lallasheta yace ta daina sa damuwa a ranta, hakan kuwa akayi da kyar mamy dasu Sumy suka rabu da Hanifa, Sameer ne ya kaisu airport suka daga zuwa jihar kano.

"Sosai ake bata kulawa a asibiti, haka Inna da momma suna bata kulawa sosai, satin ta guda aka sallameta ta dawo gida, ko ka'dan basu barinta ita kadai bale ta shiga wani tunani, mamy kuwa kullum sai sunyi waya.

"A 'bangaren su Aisar kuwa abu ya 'kara damewa, baga mum ba ga dad dinsa ba, shide Aisar ya kafe yace babu yanda zaije, ga Admiral yasa Dad din Aisar a gaba idan beyi wani kata'bus ba tofa asirinsa shima na iya tonuwa.
"Karshe dad dai lalla'ba Aisar yayi ya nuna masa komai ya wuce, he's willing to give him his unconditional support akan shari'n da suke, abun har ya bawa mum mamaki, shi dai Aisar yaji mahaifin nasa ne kawai amma yana taka tsan tsan dashi dan kuwa haka kawai yake jin be yarda dashi ba.

"Ana sauran kwana uku a koma kotu, yau Aisar ya dawo gida ya samu Dad dinsa zaune a parlor ga securities dinsa sai kai komo suke a gidan, Dad na ganin Aisar ya mike da sauri ya 'karasa ya rungumesa yana kuka shar shar da hawaye, abune me kaman wuya kai shi tun tasowansa bai ta'ba ganin hakan daga mahaifinsa ba, dan haka jikim sa yayi sanyi sosai, ya kira chief security din Dad dinsa yana tambayansa lafiya me ya faru, shima kasa basa amsa yayi ya sulale ya gudu, mikewa yayi ya nufi sama yana kiran mum....

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
73
Chapter 58 · 0% Book details