← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 73

Sashe 71

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sanda ya dawo asibiti mamy ya samu a tareda Inna ta wuce gida dan kintsawa.
"Beautiful ya fa'di yana riko hannunta, mamy ta mi'ke tana duba yaran dake kwance bisa gadonsu....
"A hankali ta bu'de idonta fuskan Haidar ta gani yana mata murmushi. Murmushin itama ta 'danyi, Haidar ya sunkuyo ya manna mata kiss goshi yace sannu Beautiful 'dina, how you feeling. "A hanakali tace" da sau'ki Handsome, jawo kujera yayi ya zauna gefenta hannunsu cikin na juna.
"Handsome yaushe kazo.
"Kissing hannunta yayi kafin yace" ai na fa'da maki zanzo,
"Toh aikin...... "shiii ya daura hannu bisa lips dinta kafin" yace Dr yace babu yawan surutu, keep calm ok, I luv you...."Murmushi ta 'danyi tare da gya'da kanta a hankali.
"Sosai Haidar da Haneefah suka burge mamy tana jin sonsu har cikin ranta fatanta Allah ya barsu tare. Sun jima a haka yana ri'ke da hannunta har bacci ya kuma yin gaba da ita.
"Namijin ne ya soma kuka yana wutsil wustil, mamy ta mi'ke da sauri ta 'dagosa.... "A hanakli Haidar ya ajiye hannun Hanifa ya nufo mamy. "Mamy me yake so ko yunwa yake ji, yayi magana cike da kulawa.
"Yunwa yakeji daga gani zaiyi tsotso, gashi bata fara basu nono ba. "Mamy ko madara za'a basu,. "Eh toh amma gwara idan ta dawo hayyacinta ta fara basu nono kafin a basu wani madara.... "Haidar ya mi'ka hannu ya kar'besa yana jijjiga sa yana fa'din" it's Okay Champ daddy is here, zaka tashi momy da princess, sai sunbatu yake da jariri, mamy kam har dariya abun ya bata.... "'Karshe Haidar ya'dan saka masa le'ben bakinsa na 'kasa nan da nan kuwa ya kama yana ja.... da haka har yayi shiru ya koma bacci.
"Mamy tayi murmushi tace" Son ka iya raino fah, lallai daughter ta huta, murmushi Haidar yayi cike da kunya....

"Gaba 'daya Haidar ya tare a asibiti idan kaga ya tafi toh darene, a haka har tayu kwana biyar a asibiti kafin aka sallame ta, sosai Inna da mamy ke bata kulawa, Haidar yaso a wuce da ita gidanta amma fir Inna ta'ki tace gwara su tafi can gida, mamy ma ta goyi bayan haka, babu yanda Haidar ya iya dole ya ha'kura. Amma kullum na gidan mamy yana tareda Beautiful dinsa da Champion da kuma princess dinsa.
Su Sumy harma da momma sun samu isowa, kowa sai sha'awan yaran yake, Shema ma kusan kullum sai tazo duba Hany, Su Sady da Mum kuma sun wuce Zariya duba dangin mum kafin zuwa ran suna su zagayo.
"Hanifa ta sami 'karfi sosai, kamarba cs aka mata ba, ta warware sosai tana samun kulawa na mussaman daga masoyanta, bama kaman Haidar baijin kunya agaban kowa yake nuna mata tsantsan soyayyansa.

👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
83

"Gidan cike yake da mutane kai kace biki ake, yara sunci sunan Umar (Farouq) da kuma Khadeejah( Deena). Gata da soyayya kam wa'en nan yara sun ganshi tareda mamansu, tun safe Haidar be sakata a idanunsa ba dan kuwa ta ko ina mutane ne ma'kil a gidan, da yamma misalin 'karfe 5:00pm ya shirya tsaf cikin sky blue jampa da hula dark blue zanna bukar yayi kyau sosai kaman ka sace ka gudu, gidan ya nufa a tunaninsa tunda yamma tayi 'kila an 'dan ragu 'yan suna tinda waliman da rana akayi.

"Kai tsaye cikin gidan ya nufa sashen mamy, su Inna da wasu gwaggwanayen su zaune a parlorn ana ciye ciye an ta'ba hira anga dangi. Aiko yana kutso kai suka soma ga angon 'karni, Haidar gaba daya kunya ya kullu'besa, ya'dan tsuguna yana gaishesu, duk suka amsa masa da sakin fuska tare da masa barka, ya mi'ka yana 'ko'karin juyawa" goggo Rabi tace" tashi abinka ka shiga kaga yaranka. Inna ta ya'be baki tace" wa yace maki yaran yazo kallo, shi yasan wacce yazo gani uwar yaran yazo gani, ni mero ban ta'ba ganin soyyaya irin na Zaki da Hanifa ba, wai kunsan basa kiran juna da sunansu sede kiji yace mata bintiful(Beautiful) itakuma kiji tace Haso( Handsome)..... "Gaba daya suka sa dariya, Inna larai tace yo ai gaskiyansu haka muke so gwara suso junansu, kode kishi kike ne yaya mero. Dariya Inna tayi tace wa ni ai na sallama wa Hanifa suje can suci soyayyansu ita da taga zata iya rayuwan saman ruwa, ni mero ina zan iya salon kifi ta cinyeni... aka kuma saka dariya gaba 'daya..." Haidar ya mi'ke yana sunne kai..." caraf Inna tace" meye kake 'ko'karin juyawa mun san wajenta kazo, maza 'karasa nasan itama yau seta kusa zazza'bi tinda ta yini bata ganka ba.." kallon zamu ha'du Haidar ya mata kafin ya haye sama.

"Sallama yayi a 'kofan 'dakin kafin ya shigo, tana zaune saman stool gaban dressing mirror Anty Hiba na shiryata da alama wanka ta fito, su Sady suna zube saman gado ana zuba surutu. Gaba daya suka soma gaishesa yana satan kallon Hanee yake amsa gaisuwansu. Nan suka soma gaisawa da Anty Hiba sai tsiya take masa, wayan Anty Hiba ne ya soma ringing ta 'dauka ta nufi downstairs dan mamy ce ke kiranta.
" kai tsaye gadon babys ya wuce ya shiga masu wasa sai wutsil wutsil suke... Su Shema kuwa mi'kewa sukayi da niyyan fita Hany ta tsaresu da ido ina zaku, Sady ta 'karaso kusa da ita ta ra'da mata" Romeo is here you guys need some space nasani, harara Hanifa ta watsa mata, dariya Sady tace a hankali" King yana hanya, any moment from now zai iya isowa, so I need to go and check if his abinci is ready, Hanifata dubi su Shema da har sun isa 'kofa tace " and you ina zaku, Sumy tace zamuje gidan Hajiya dauko Amal da Ajmal... daga haka suka fice gaba 'dayansu.
"Haidar se kallonta yake yanda tayi kaman bata san yana 'dakin ba, har ta gama saka sar'kanta, 'karasowa yayi yanda take ya rungumota ta baya yana fa'din" Beautiful why the long face, you know this face doesn't fit you at all, ya 'karashe maganan yana sunbatan wuyanta, "'kala bata ce masa ba ta shiga saka enkunnaye, hannu yasa ya kar'bi 'yan kunnen yana sa mata yake fa'din" Beautiful you look Spectacular I luv you, ya 'karasa saka mata 'yan kunnen ha'de da manna mata kiss a wuya..... jin ya fara wuce gina da iri yasata saurin turesa tana fa'din" ni babu ruwana da kai baki a ture. Mi'kar da ita tsaye yayi yana ri'ke da kunkuminta yace" I admit nayi laifi banzo ba tun safe, am sorry Beautiful..... "Zatayi magana ya saka bakinsa cikin nata ya shiga kissing nata, sun jima a haka saida sukaji kukan Deena kafin ya saketa nan suka nufeta dukansu, Haidar ya 'dauketa yana jijjigata amma kaman cewa ake ta 'kara, da sauri ya mi'kata ma Hanifa yana fa'din" what's wrong with her, maybe she's hungry, oya feed her.... "Kallonsa kawai Hanifa keyi yanda duk ya daburce, aiko kaman ha'din baki nan Farouq ma ya soma, Hanifa na bawa Deena nono dole Haidar yayita jijjiga sa, ana haka mamy ta shigo da sauri tana fa'din lafiya de ko... "Ai da sauri Haidar ya mi'ka mata Farouq yana fa'din mamy at the same time suke jin yunwa, kinga Deena ta fara first gashi shima yanzu yana yi. Mamy ta kar'besa ta shiga basa madara.
"Kallon abincin da aka shigo ma Hanifa dashi tayu da alamu bata ci ba, ta gama bawa Farouq madara ta mi'ke ta shiga duba abincin, aiko ko ta'bawa ba'ayi ba.. "Tunkan mamy tayi magana gaban Hanifa ya shiga fa'di tasan bazasu wanye da mamy lafiya ba dole ta sata cin na dole.Haidar na ri'ke da Champion dinsa bayan mamy ta gama basa madara.
"Mamy bata ce 'kala ba ta shiga zubawa Hanifa tuwon dawa miyan kuka da yaji man shanu da pepper soup din kayan ciki, ta 'karasa ta kar'bi Deena kafin ta saka mata abincin a gabanta tace "oya eat up..... "Marairaice fuska Hanifa tayi tana fa'din mamy am not hungry, pls mamy... " Com on maza ki cinye abincin nan ban son wani magana, you haven't eaten anything since morning, and yet kina cewa baki jin yunwa... "Haidar ya 'karaso ya saka mata pillow a kan rug kaman yanda yaga ana mata ya ri'ko hannunta ya sau'kota 'kasa yana fa'din "is okay Beautiful zo na tayaki ci..."Muryansa ne ya sar'ke sanda yaga ba'kin tuwon, ya 'dago kai yana kallon mamy kafin yace" mamy what's this, haba haba mamy she can't eat this for heaven sake. This is irritating mamy.... Harara mamy ta galla masa kafin tace" zaka min shiru kokuwa, idan bataci tuwo taji 'karfi ba ina ruwan nono zaizo kana gani yaran tsosto garesu... "jinhaka yasa Haidar fa'din aah toh barun tayaki Beautiful, ya 'dauki spoon yana ci yana bata ashe tuwin da da'di, mamy ta shimfida Farouq dan yayi barci, daidai nan Anty Hiba ta shigo tana fa'din" Mezan gani Admiral da cin tuwo.... dariya Haidar yayi kafin yace" ba dolena na ci ba tunda Beautiful zataci. Dariya Anyy Hiba tayi tace lallai soyayya be bar komai ba snn zai iya canza kowa tunda ya canza *Mijin Haneefah* harta mamy saida ta dara. Anty Hiba tace yawwa idan kun gama Abba naso ayi family pics gaba 'daya a parlonsa,.
"Haka akayita yin pics gaba daya, iri da kala, iayayen yara kakkani da kuma su inna tatta'ba kunne lol.

"Zuwa washe gari gidan ya watse, sati 'daya Haidar ya 'kara ya koma bakin aiki, tinda ya tafi saidai waya kawai suke dan gaba 'daya aiki ya ri'kesa, baya samun zama at all.
"Hanifa kuwa wata biyi tayi ta koma gidanta, Mamy ta sama mata wata 'yar uwa daga 'kauye tana tayata rainon twins.
Chapter 71 · 0% Book details