← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 73

Sashe 56

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*Court of supreme Lagos*
"Kotun ta cika ma'kil da jama'a yanda kowa ya kasa kunnensa dan sauraren shari'an da za'a gabatar,
"Al'kali ne ya shigo kowa ya mike saida Al'kali ya zauna kafin kowa ya zauna a wajen zamansa, maga takarda ya mi'ke ya karanto shari'an da za'a gudanar tare da laifin wanda ake tuhuma.
"Al'kali ya 'dago kai kana yace kotu tana bu'katan ganin wanda ake kara agaban kotu. Take wani sajen ya tafi dan shigo da Haidar,.... " kwalla ne ya ciko idandunansu ganinsa 'daure cikin handcuffs, haka har aka wuce dashi cikin akurkin tuhuma. 'Addu'a kawai Hanifa keyi cikin zuciyanta "Oh Allah give me some strength to go through this, haka mamy ma.
"Lawyoyi ne daga 'bangare biyu suka mi'ke suka gabatar da kawunansu, lawyern me 'kara da lawyern wanda ake 'kara.
"Al'kali ya dubi Haidar yace kaine Captain Aliyu.
"Eh ya mai shari'a
"Kaji tuhuman da ake maka
"Eh naji ya me shari'a.
"Ka yarda ka amsa laifinka.
"Shiru Haidar yayi na 'dan lokaci..... "kowa addu'a yake cikin ransa Allah sa kar ya amsa.... Ido hu'du sukayi da Admiral wanda keta faman murmushi.
"A'a ya mai shari'a ban amsa laifin ba.
"Al'kali ya sunkuya yayi wasu 'yan rubuce rubuce kafin ya dago yace, ko kwai wanda ke da tambayan da zaiyi ma wanda ake zargi ya fadi yana kallon lawuers din.
"Eh akwai ya me shari'a, Barrister Badamasi Barnabas ya mike snn yace na gode ya me shari'a " Suna na Barrister Badamasi Barnabas nine Lawyern wanda yake 'kara, kafin ya 'karasa gaban Haidar yace, "Captain AA a ranar ishirin da 'daya ga watan January kayi furuci na cewa sai kaga bayan Latifa anyi haka ko ba'a yi ba.
"Haidar ya gya'da kansa yace kwarai na furta haka amma bani na kasheta.
"Barr Barnabas yayi murmushi kafin yace " Captain, kowa ya sani cewa Latifa tsohuwar budurwarka ce wacce take kwana a gidanka, kun samu sa'bani dan ta bijirewa bu'katarka ta daina kwanan gidanka, shine kayi yanda kayi ka tilasata mata zuwa har gidanka snn kayi amfani da wnn daman ka kasheta...... "Objection your Honor, Sameer ya fadi," Barr Barnabas ya daina 'daura wa client dina laifi kai tsaye dan zarginsa kawai ake ba a kamasa dumu dumu yana aikata laifin ba.
"'Korafi ya kar'bu Barr Barnabas ka gyara kalamanka.
"Thank you your Honor, Cewan Barr Barnabas kafin yaci gaba da fa'din" Captain AA a ranar 27 ga watan January an samu gawan Latifa a cikin gidan ka anyi haka ko ba'ayi.
"Haidar ya gyda kansa yace anyi haka,
"Toh knn ba kai ka kasheta ba kake so kace wa kotu, idan ba kai ka kasheta ba waye ya kasheta, snn kowa ya sani Latifa bata tarayya da kowa sai kai.
"Barr Barnabas ya juyo da dubansa ga Al'kali snn yace" Ya me sha'ria, Captain Aliyu Abubakar ya masa laifinsa a ganan jami'an tsaro a ranar 21 ga watan January bayan an sami gawan late Latifa Tanim a cikin gidansa, da wnn 'kw'k'kwaran hujja nake ro'kon wnn kotu me alfarma data dubi irin rashin adalcin da Captain AA yayi wa shugabansa Naval Chief of Staff Admiral. Tanim Razak ta hanyar kashe masa tilon 'yarsa da ya mallaka a fa'din duniya, ta yanke wa captain AA irin hukuncin da ta dace dashi. Na gode ya me shari'a.... Barr Barnabas ya tafi ya zauna, "Haidar kuwa gaba 'daya ji yake tamkar jijiyoyin jikinsa su daina aiki, yana 'dago ido sukayi ido hudu da Hanifa idonta yayi jajazur, through kawayan idon juna suke aika wa juna sakwanni, take yaji wani strength yazo masa. Zuciyansa tana da'da kara masa 'karfin gwiwa." Admiral kuwa wani da'di ne ya ziyarci zuciyansa, ji yake ya eiga yayi winning case din nan an gama.

"Al'kali ya su kuya yayi wasu rubutu kafin ya dago ya dubi Sameer yace Barr Ridwan ko kanada abunda zaka tambaya daga wanda ake 'kara.
"Eh ya me shari'a Barr Ridwan ya fadi kafin ya fito zuwa gaban kotu.
"Ya dubi Al'kali yace " ya me shari'a ina bu'katan kotu ta bani dama na bu'kci Captain Aliyu ya fa'dawa kotu asalin ala'karsa da marigayiya Latifa.
"Kotu ta baka dama Barr Ridwan go ahead,
"Thank you your honor, Barr Ridwan ya fa'di kafin ya dubi Haidar yace " Captain AA kotu tana son sanin asalin alakarka da latifa... nan Haidar ya fadi komai, cewa shi ba son Latifa yake ba hasalima ita tayi seducing dinsa har suka soma aikata mummunan laifi, snn yayi taking wnn advantage dinne dan ya cimma burinsa na binciken da yake akan mahaifinta.
"Barr Ridwan yayi murmushi kafin yace" Captain ko menene kake zargin Mahaifin nata dashi har ya kasa ha'kura ya la'ka maka sharri...... " Objection my lord, Barr Barnabas yayi interrupting kafin yace" ya mai shari'a ya kamata lawyern wanda ake zargi ya daina shigo da wani shari'a cikin wani shari'a... "Korafi bata kar'bu ba, Barr Ridwan ci gaba da tambayoyinka. "Murmushi Sameer yayi kafin yace na gode ya me shari'a.
"Nan fah idon Admiral ya soma kadawa cikinsa ya shiga kugi, Barr Barnabas ya girgiza masa kai alamun kar ya razana.

"Barr Ridwan yaci gaba da fa'din, ko menene kake zargin shugaban naka dashi Captain AA,
"Haidar yace, ina zarginsa da almundahana da dukiyan 'kasa snn ina zarginsa da hannu a kisa tsohon kwamandan rundunar sojin ruwa.
"Barr Ridwan yayi murmushi kafin yace, knn Latifa tana tayaka binkice akan mahaifinta,
"Kwarai tana tayani, tare da ita muke binkice, hasalima ana gobe za a samu gawarta a gidana munyi waya cikin dare take ce mun na taimaka mata kar ya kasheta, ni kuma ban dauki hakan serious ba dan kwanakin baya tayi mun haka daga baya tace mun wasa take.
"Barr Ridwan ya juyo yana duban Al'kali kafin yace ya me shari'a, Captain AA ya kasance me gaskiya akan aikinsa wanda duk mutanen da suke tare dashi sun san wnn, sann 'ko'kari da yake yi na tono gaskiya shi yasa Admiral yayi 'ko'karin kashe 'diyarsa dan ya daurawa Captain sharri da bazai iya fita daga ciki ba.
"Ya me shari'a ina son gabatar da takardun da Haidar ya samesu ta hanya Latifa daga wajen Admiral.
"Alkali yace kotu ta baka dama Barr Ridwan.
"Na gode ya me shari'a, snn ya miko takardu maga takarda ya kar'ba ya mi'kasu ga me shari'a.
"Al'kali ya kalli takardun sosai kafin ya soma magana" Bisa ga hujjiji da suka gabata a gaban kotu, kotu tana son yin binciken wa'dan nan takardu, dan haka kotu ta 'dage wnn shari'a har zuwa ranar biyu ga watan may. Snn za'a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma har zuwa ranar da shari'a zai zagayo. Daga haka Al'kali ya mike ya fice, nan mutane suka soma fitowa.
"Aka zo za'a wuce da Haidar kuka sosai su mamy sukeyi, shima kwallan ne yaji ya ciko idonsa ganin mamy ta rungume Hanifa tana kuka......

👸🏻Queen Samy😍💋💄.......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
71

"Banda safa da marwa babu abunda yake cikin tapkeken parlornsa wanda yasha furniture na alfarma, dun'kule hanunsa yayi ya daki garu yana furta" Damnn it Damnn everything.... that little Brad really wants to die just like the way his invincible father does, you really don't know who you messing with 'karamanin 'dan iska. Tsaki Admiral ya buga jin waya landline dake ma'kale a parlorn na ringing..... " A hasale ya 'daga yana fa'din" what's this again, didn't I tell you, I don't wanna seee anybody..... "Am sorry sir " NNPC chairman really wants see you, he said you have an appointment.
"A sittin Admiral yace " let him in...
Chapter 56 · 0% Book details