← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 73

Sashe 62

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci nan Al'kali ya wanke Haidar tsaf daga zargin da ake masa, Sady da Sumy rungume juna sukayi dan murna, Sameer na murmushi yake girgiza masu kai alamun no more kuka, Haidar tsakiyan 'kannensa yaje ya rungume su baki daya.
"Admiral da Dad din Aisar kuwa sai wulli wulli da ido suke, kotu ta yankewa Dad din Aisar life in prison tareda hore me tsanani bisa laifin samun hannumsa dumu dumu cikin kisan Barr Ridawan Marafa, "hannu Dad ya daura aka lokacin da yaji Sentence dinsa, ya juyo yana duban amininsa yana fa'din ka cuce ni Tanimu ka cuce ni...." Al'kali ya buga bnci Silence...." snn yaci gaba da fadin, Admiral. Tanim Razak, an kama da laifuka kaman haka na farko kisan Tsohon hafsun rundunar sojin Ruwa tareda iyalensa, na biyu tauye rayuwar matarka da 'diyarka ta hanyar humiliating dinsu, na uku kisan 'diyarka Latifa tareda 'durawa Captain Aliyu Abubakar sharri...." wadann sune laifukan ka. Kaman yanda take a 'kundin tsarin mulkin 'kasa a matsayinka na soja hukuncinka yasha banban da civilian" kotu ta yanke maka hukuncin daurin rai da rai ta hanyar rataya..... " These are your sentences" daga haka Al'kali ya mi'ke kotu ta amsa da kooooot. Jama'a suka soma turuwan fita, nan da nan aka ka'da 'keyan Admiral da Dad din Aisar.

"Ana 'ko'karin fiffitowa Cheif of defense ya 'karaso gaba Haidar da sauri Haidar ya sara masa, kan kace me shima ya sara wa Hakdar, ya mika masa hannu sukayi musaba snn yace" Captain AA you did a great a job, I salute to you navy, samun irinku a cikin sojoji ALHERI NE, keep on with it, zan bar lagos jibi, so kafin na tafi ina so akwai meeting da zamuyi."Haidar ya kuma sara masa kafin yace" Thank you very much sir, "The pleasure is mine Captain. Daga haka Chief Of Defense ya wuce securities dinsa sukabi bayansa.
"Chief of staff yasa a dauki mum din latifa a kaita asibiti a bata kulawa daga nan sai su nemi relatives dinta.

"Sameer zama yayi dirshan a bakin kotun yana kuka shar shar da hawaye, ha'ki'ka yau mutuwan Dad dinsa ya dawo masa sabo, ashe dad din Aisar da Admiral su suka kashe masa mahaifinsa....." Haidar ne ya 'karaso ya dafa sa, yana 'dago kai suka rungume juna take Haidar ma yaji hawaye na bin 'kuncinsa.
"Haidar ya soma fa'din" Sameer ka kasance 'da na gari, ha'ki'ka yau da mahaifinka na da rai zai yi tin'kaho da kai, Allah ya ji'kansa ya gafarta masa, your Dad is in better place Sameer, yau wa'danda sukayi sanadin mutuwar ga tasu tazo, snn zasu girbe abunda suka shuka.
"Sameer ya share hawayen idonsa kafin yace haka ne Haidar, na gode da kalamanka.
"Haba Barrister ni yafi cancanta na mi'ka godiyata a gareka, dukda kalamai kawai bazasu isa nuna maka irin godiyan da nake maka ba, na hantareka na ci zarafinka na wula'kanta ka, dukda haka baka fasa kyakkyawan 'kudirinka akaina ba, Sameer thank you once again....." pls Haidar ka daina mun irin wnn godiya haka ni da kai 'yan uwa ne....." muryan momma suka ji tana fa'din wnn haka ne 'ya'ya na, a tare Sameer da Haidar suka juyo, Momma na tsakiyan Sady da Sumy ta 'karaso ta ri'ke hannu Sameer da Haidar tace "Alhamdulillah yau Allah ya kawo mana 'karshen wnn shari'a, Allah bazai bar zalunci ta tabbata a doron 'kasa ba, yau azzalumai zasu fara girbe abunda suka shuka tun daga nan duniya har su isa masaukinsu a lahira, Allah ya da'da 'daukaka gaskiua a duk yanda take, snn ya kawar da 'karya a duk yanda take, gaba 'daya suka amsa da ameen.
"Haidar ya dan dube su yace momma Hanee I need go and see her, I can't stay here any long..... gana daya suka sa dariya ganin tsayuwar motar su Hanifah, Haidar ya dan harari Sameer yace " this is not funny Barrister may I've car keys, if you can give me a ride kuma fine, muje ka kaini na gant..... bai gama rufe baki ba ya hangota a guje ta nufo sa.... ai shima a tamanin ya nufeta, a tsakiya suka hade ya kuwa rungumeta tareda 'daga ta sama yana juyi.... Su momma dasu mamy su Inna harma dasu Sumy me zasuyi banda dariya, harta Abba saida ya dara,...
"Sun jima suna rungume da juna kafin ya dago face dinta yana kallo, kallomsa take itama babu ko 'kyafta ido, " yaHajdar what did the judge said, hancinta ya 'danja kafin yace " ba kinji sentences dina ba, yanzu haka an barni na miki sallama ne before a tafi dani....." no no that can't be... ganin ta soma wuri wuri yasa sa saurin rungumeta cikin jikinsa kafin yace" easy Beautiful kar ki mun asara biyu keda unborn dinmu, bakinsa dazu da kika fainting cikin court ba kadan da na zune nima..." yaHaidar ka fada mum pls me ake ciki...." shiru yayi kaman bazaice komai ba sai kuma ya daga ta sama yana fadin " I'm a free maaaaan, wani 'kan'kamesa tayi cikin jikinta hawaye na 'ko'karin fito mata tace" Oh Allah Alhamdulillah, sauran fa ina suke.... sai snn ya juya yamda ake shigedasu Admiral bayan ambulance itama kallonsu tayi. Suna gani aka tasa keyarsu, Har lokacin Haidar na rungume da Hanifah a hankali ya saketa ya nufi gabansu Admiral, kaman bazaice komai ba ya kuwa kai masa wata wawan naushi a fiska saida ya dur'kusa a wajen, "Haidar ya 'dagosa kafin yace " this is for Hanifa, Latifa and Aisar.... " didn't I told you " eventually you'll get what you deserves, now the time has come sir, you'll pay for each and single crime you had committed, ka sani Allah baya mulki da zalunci ya zaka tarar da abunda ka shuka miserable coward, "Admiral be iya cewa komai ba aka tasa 'keyarsa cikin ambulance, Hanifa ta 'karaso ta sakala yatsunta cikin nasa murmushi yayi sanda ya juyo da dubansa gareta...... kaman bazasu bar kallon juna ba haka suka yi " Inna ta ya'be baki tace " oh Mero naga duniya zaku zo mu tafi ne kokuma zaku cinye juna da kallo ne kamar tauraren cikin pilm(film)..... ko kuma kotun ne baku gajimda zamansa bangaba daya aka sa dariya.
"Haidar ya 'dan dubeta ya ta'be baki kafin yace 'karar ki zan shigar dan kina 'ko'karin raba auren soyayya, kuma nasan duk kishi ne ke damunki.
"Ta'be baki inna tayi ta jawo kennensa kafin tace ka gama nacinka sai ka sakar mun jikata..... Haidar ya ri'ke kunnensa yana 'dan 'kara Inna tace ashe sojann'karya ne..... gaba 'daya aka sa dariya Inna harda ranga'da gu'da ta shige tsakiyansu ta rungumesu tana fa'din Alhamdulillah Allah ka cika mun burina ko yau na bar duniya burina ya cika, Aliyu Haidar ya zama *Mijin Haneefah* ba Haidar da Hanifa kawai ba duk sauran mutanen dake wajen saida sukayi dariya.

"Phillips Drivern Haidar ne ya 'karaso da sauri dan murna baisan sanda ya rungume Haidar ba..... Haidar ya dago yana dubansa da mamaki, ai a sittin phillips ya soma shafa kai ya sarawa Haidar yana fa'din " Sorry Sir na kasa 'boye farin cikinane.... Murmushin 'kasaita kawai Haidar yayi ya bubbugi kafa'dan phillips yace is Okay Phillips I understand you, and thank you very much.... haka sojoji 'yan uwansa sukayita congratulating 'dinsa gameda nasaran da ya samu.
"Da kyar Haidar ya samu ya zille bayan yace wa phllips ya matsar da motan daga wajen mutane, Su Abba kam tuni sun wuce, Haidar da Hanifa ne suka rage, yana rungume da ita kaman mai tsoron kar wani abu ya gifta tsakaninsu, gaba daya sai suka koma tamkar celebrities ,haka suka shige bayan mota phillips yajasu, nan Haidar ya cewa phllips gidansu Aisar suka nufa.

"Suna isowa mamaki ne ya cika Haidar ganin motocin su Sameer pake a haraban gidan, Phillips ya fito ya bude masu hade da sara masu, hannun Hanifa Haidar ya sakale cikin nasa suka soma tafiya,
"YaHaidar cikin mutane fah zamu shiga ka sake mun hannuna kaga da alama su Abba na cikin gidan nan, ta fa'di tana kiciniyar kwace hannunta.
"Da'da matse hannun Haidar yayi kafin yace" So, matata ce fa, kikayi wasa 'daukan ki zanyi a hannu kaman baby..... dariya kawai Hanifa tayi ta sunne kanta sanda suke sallama a 'kofan parlorn.
Chapter 62 · 0% Book details