← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 73

Sashe 17

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Koda ya shige gida bebi takan Hanifa daki ya wuce yayi wanka ya canza kaya, abubuwa da yawa yake tunani, ya kasa samun sukuni gameda Latifa da Aisar, duk yanda akayi akwai abunda suka 'boye masa, he needs to find out menene suke 'boye masa da wnn tunani ya 'karsa dinning dan cin abinci. Yana zaune yana cin abinci ta fito daga daki hannunta ri'ke da cup, beji motsin fitowarta ba dan haka cikin nutsuwa yaci gaba da cin abincinsa, kallonsa take yayi kyau sosai cikin 'kanan kaya red shirt da blue jeans farin fatarsa ya fito sosai, ta'be baki tayi tace a ranta kyaun 'dan maciji. Haka kawai yaji kaman kallonsa aikuwa tana nan tsaye ta kafa masa ido, murmushi yayi a ransa dannyaji da'din ganin ta warware tayi kyau sosai sai ta 'kara haske tana sanye cikin doguwar rigar atamfa Holland atampar me duhu ne sai ya fito da farin fatarta kanta babu 'dankwali sai manyan kalaba da bazasu wuce goma ba sun zubo har gadon bayanta. Dukansu kallon juna suke kowa da abinda ke sa'kawa a zuciyansa...... "Keeee! Ya daka mata tsawan da yasata razana, " ke wace irin mayya ce kin tsare mutum da ido salon na 'kware ko. Babu hali kiga namiji sai kin nuna maitar ki a fili.
"To be frank ta gaji da kalaman da yaHaidar ke jifanta dasu, ta 'dan 'daure fuska batare da tace komai tazo zata wuce kitchen, kallon mamaki ya bita dashi a ransa yace "ah lalle yarinya kin girma dole kiyi banza dani ina maki magana. Mi'kewa yayi ya nufota, ta juya da sauri zata sa gudu ya capko ta. Da hannu 'daya kawai ya ri'keta amm ko motsawa ta kasa, ta shiga kiciniyan 'kwace hannunta amma ta kasa.
"Ido ya kafa mata kafin yace " ni sa'anki ne ina maki magana kin min shiru. 'Kwalla ne yaciko idonta tace wllhi banjika bane fa, bakinta ya kama da yatsansa ya mur'da saida ta 'danyi 'kara kafin yace " inaga kin mance waye Haidae gwara na tuna maki.
"YaHaidar dan Allah kayi ha'kur...... bata ankaraba sai jin bakinsa tayi cikin nata, cup 'din dake hannuta ne ya fa'di aikuwa nan ya tarwatse a wajen. Cak Haidar ya 'dagata sama kaman wata baby. Kan sofa ya mata masauki kafin ya soma binta da mugun kallo, kallon 'kasan yanda cup din ya tarwatse yakeyi Nutella da madara da sugar yaga ta ha'da tana sha. Ya maida da dubansa gareta fuska a tamke kafin yace "meye kike sha, shiru tayi ta kasa basa amsa, saida ya kuma tambaya kafin ta soma inn nna.
"Gajeren tsaki yayi ya jawo kunnenta gamida mur'dawa, ta shiga 'kara a hankali tana basa ha'kuri.
"Haidar yaci gaba da fa'din " kina jina idan kika kuskura kika sake mun kukan ciwon ciki a gidan nan sai fasa kanki da bindiga wawuya kawai da'ki'kiya, saboda tsaban toshewan 'kwal'kwalwa irin taki baki ma san meke kawo maki menstruation pen dinba, na sake ganin kina shan kayan za'ki haka sai na karerayi ya sake kunnen yace "Get out of my side stupid kawai. Ta soma tafiya tana share 'kwallan idanunta ta nufi 'daki, har ta kai 'kofa yace " zo nan, babu musu ta juyo baki a cure,
"Tidy this place first, komawa kan dining yayi ya 'dau wayarsa ya dawo parlor yana gani ta gyara wajen tsaf. Ta gama ta nufi hanyan 'daki kiranta ya sake ta dawo ta tsaya yafi minti biyu na neman chanel din kallo kafin yace" kinci abinci girgiza masa kai tayi alaman a'a. Mi'kewa yayi ya kawo ya zubo mata abincin ya sakata gaba dole taci, tana ci tana satan kallonsa idan sukanha'da ido kuwa harara yake watsa mata, tana gama ci ya mi'ko mata magani da glass of water, turo baki tayi tace yaHaidar na warke fah. Wani mugun kallo ya watsa mata wanda yasata kar'ba babu shiri haka dole ta sha maganin. Ta mi'ke zata wuce muryan shi ya daki dodon kunennta. " ki shirya anjima zan kaiki kiba wa budurwata ha'kurin laifin da kika mata jiya kuma saura idan munje kiyi misbehaving kiga yanda zanyi dake a gidan nan.
"Kaman bazata tafi ba haka ta tsaya dan wani mugun ba'kinciki ne ya tokareta, wai mijinta ne ke cewa taje ta bawa karuwa ha'kuri kai gaskiya Allah ya isanta..... "meye kika tsaya mun a nan dalla 'bace mun da gani jor. Ya fa'di yana mata mugun kallo. Da sauri ta wuce kaman zata tashi sama.... shi kuwa Haidar 'kasitaccen murmushi ya sake ko babu komai yasan ya 'kuntata mata, ya shafi ha'barsa yace yarinya bakiga 'kunci bama tukunna sai mun fita......

👸🏻Queen Samy😍💄💋........
🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
30

"Wani farin 'kyalle ya 'daura a kunkuminsa jikinsa babu komai sai wnn farin kyallen, kai tsaye ke'be'b'ben 'dakinda da babu mahalu'kin da yasan dashi a gidan ya shiga. Wata mata da bazata haura shekaru 45 bane zaune da jan kaya kamar gunki, gashin kanta duk ya damfare sabida datti, fatar jikinta duk ya yamutse ya tattare, kai tsaye Naval Chief of Staff ya nufi wajen matan "wani surkulle ya soma ambata nan da nan matan nan ta shiga juyi kaman fanka, kannkace me saiga wani mutumi ya fito, tsugunawa Dad yayi ya shiga mi'ka gaisuwa wa mutumin, nan suka soma magana cikin yare.
"Bokan yace Tanim! Da sauri Dad ya 'dago yana kallonsa kafin yace kariyan arziki na daf da kamaka kuma kana daf da rasa wnn mu'kami da kake kai. Zaro ido waje Dad yayi yace ban gane ba lawo, meyasa hakan ke faruwa. Wani dariya lawo ya kwashe dashi kafin yace " nasha fa'da maka wnn yaro dake 'kar'kashinka shine silan rugujewanka idan kayi wasa.
"Wani yaro kake nufi Lawo?
"Wann yaro Aliyu baka da babban matsalan da ya wuce shi.
"Na fa'da maka Lawo a kawar dashi tun ba yau ba.
"Hahaha da'dina dakai bakada imani, gaka soja amma sai rashin imani.
"Dad yayi 'kasaiteccen murmushi kafin yace " who ever tried to get in my way dole na kashesa.
"Wani dariya Lawo ya sake yi kadin yace kashe wnn yaro yana daidai ka kashe 'yarka abin 'kaunarka Latifa. Kar kayi gaggawan hala'kasa idan lokaci yayi zan sanar da kai. Amma a halin yanzu kar ka kuskura ka sake 'yarka ta aure shi, snn ka rage kusantar 'yarka shiyasa take 'ko'karin juya maka baya, kayi 'ko'kari ka rin'ka kusantar ta a 'kalla sau biyu a rana zaka yi haka na sati guda kafin ka 'daga mata 'kafa.... daga haka Guguwa ta kwace a cikin 'dakin nan Lawo ya 'bace bat wnn matar ta dawo ta zauna yanda take zaune.
"Kanta Dad ya shafa yace " Malika matata na fa'dawa 'yarki kin mutu tsawon shekarun nan snn na maida gurbinki da ita...... ya fashe da wata dariya kafin ya fice daga 'dakin da baya da baya yana surkulle.

5:33pm
"Haidar ya gama shirinsa cikin armless shirt kaki kalan green wato asalin kakin land army snn ya saka wando ba'ka three quatre, yayi kyau sosai kaman wani _Safari brother_😍. Fitowa yayi sai 'kanshi turare yake. Yankusan mintuna uku yana jiran Hanifa ta gama shiryawa ta fito su tafi amma shiru bata fito ba, a hasale ya wuce dakinta ya shiga... Tana tsaye jikin dressing mirror tana shafa mai towel ne daidai cinya 'daure a 'kirjinta, Haidar kam mutuwan tsaye yayi yana 'kare ma cinyoyinta kallo.... ihu tasa ta wuce bathroom da sauri harda kullo 'kofan. Tsaki yayi ya 'karasa jinkin 'kofan ya shiga fa'din " Monster kika gani ko me? idan kinga dama karki fito ki bari na 'kara five seconds ina jiranki sai kinga abinda zan miki, daga haka yayi ficewarsa waje amma me cinyoyin Hanifa sun kasa 'bace masa daga 'kwa'kwalwansa. Gajeren tsaki yayi yace" Oooh Haidar what's wrong with you, kanme ma zan tsaya tuno wnn yarinyar...
"Tana fitowa taja dogon tsaki tace "aima kafi monster a gurguje ta shirya cikin ba'kar abaya tayi kyau sosai kai kace dominta akayi kayan.

"Tun kan ta 'karaso yake binta da kallo tayi masa kyau sosai, tana isowa ya ta'be baki yace bakiyi kyau ba. A ranta tace oho dai kaima haka ko kyau bakayi ba.
"Wayan shi ya 'dauka ya shiga neman layin Latifa har ta yanke ba'a 'daga ba. Dakewa yayi kaman an dau wayan snn ya soma magana "hello darling are you at home, Ok barin kawo ta yanzu tazo ta baki ha'kuri, yawwa sai na iso....
"Hanifa ta gama 'kuluwa tana jinsa har ya gama wayansa. Shi kiwa Haidar babu wayan da yayi kawai dai ya 'kuntata mata ne. Bu'de mazaunin driver yayi ya shiga, kaman bazata shiga ba sai kuma ta bude back seat, wani uwar harara ya sakar mata kadin yace "who's your driver, common wuce ki dawo nan ki zauna kafin nayi 'kwallo dake. Ta dawo front seat ta zauna a zuciyanta tana me mamaki irin tsanar da yaHaidar ya mata... Suna tafe cikin motarsa Mercedes GMK. Wayan Latifa yagani tana kira, rejecting yayi ba tare da ya 'daga ba. Hanifa kam sai kallo take mussamanda suka fita daga cikin maritime dan kuwa tun zuwa bata ta'ba fita ba sai yau, ko wani gate suka wuce sai gaba daya sojojin sun mike sun sarawa Haidar. Yana hankalce da ita sai kalle kalle take
"Ke local champ, ki rage kallon naki mana kar idon ya fado, ooh na manta this is yor first time a city kaman nan ashe. Bata ce komai ba sai sau'ke idonta 'kasa da tayi.
"Wayan shi ya 'dauka ya turawa Latifa tex.
_" let's meet at the beach"_
"Yana gama turawa kaman jira take ai kuwa cikin zumu'di ta mayar masa da reply
_"Ok luv I'll be there right the way"_
Chapter 17 · 0% Book details