← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 73

Sashe 67

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A satin bikin Aisar da Sameer suka iso Kano, Aisar da kansa ya tafi Zariya dauko Queen dinsa, yana isa waya ya mata ya sanar da ita ya iso, aiko su Fadila da Rashida suka sakata gaba da zolaya,
"Fadila tace "Oh ashede ashede shine angon, sojan da aka gama masifewa, Rashida tasa dariya tace ni dama tun a lokacin na gane they both had a crush..... " tsaki Sady tayi tace dan Allah kuzo mu tafi banson King yayi ta zama jira, dariya sukayi suka dauki luggage dinsu suka wuce, dan dukansu ko wacce an barta daga gida taje bikin kasancewar bikin aminiyansu ne, snn sunyi covering yawancin syllables dinsu dashike semester taja, sun kusa soma examz.
"Haka Fadila da Rashida sukata dariyan fa'dan Aisar da Sadiya cikin motan nan, yanzu za'ayi fada kowa ya juyar da kansa anjima kadan kuma sai a shirya yace my Queen tace my King.lol.....

"Gidan ya soma cika da jama'a, su Anty Hiba ma sun samu isowa tareda me gyaran amare, su Sady na isowa Anty Hiba ta wuce da ita yanda ake masu gyara ita da Sumy, already su Fadila sun sauka gidan wata Antyn ta dake nan Kano.
"Shema ta lura da yanayin Hanifa, dan haka saida ta bari babu kowa ya rage saura su biyu a dakin Inna ta soma tambayanta meke faruwa.
"Kuka Hanifa ta soma tana fa'din" Shema I just couldn't help it anymore, I really need someone to talk to..... "jiki sanyaye Shema ta matso ta ri'ke hannayenta tace" I'm here for you Hany, pls tell me what's bordering you.
"Hanifa ta goge hawayen idonta" kafin ta fa'dawa Shema duk abunda ke faruwa tsakaninta da yaHaidar, da mugun mamaki kawai Shema ke binta da kallo....." Hanifa ta katse shirun da fa'din" I luv him Shema, I luv him with all of my heart I don't wanna loose him.... "Shema ta sau'ke ajiyan zuciya kafin tace " What on earth could possibly make you do that Hanifah, haba haba that was crazy, da iliminki da komanki kiyi irin wnn shirme, it just doesn't fit in head.
"Shema pls yanzu ba lokacin dawo da zance bane, I want my husband, I need him.... "Shema tece" alright fine, ina wayarki sake kiransa...
"He won't pick up, na sani ne.
"Karki damu just call. Jiki a sanyaye tayi dialing.....

"Da sauri Haidar ya matsaya baya dan kar suji karan wayarsa. Saida ya fice daga sashen Inna kafin ya soma amsa wayan.

"Hello Beautiful,.....
"Mamaki ne ya kamata jin ya amsa mata... "yaHaidar kawai sai ta soma kuka, Haidar hankali a tashe ya soma fadin" Oh am sorry Beautiful, pls stop, kafin ki fa'da mun laifina I admitted, nayi laifi, all these while we didn't heard from each other, and this is all my fault, Beautiful kiyi ha'kuri aiki ne ya min yawa, pls forgive me I promise that will never happen again kinji Soulmate,..
"Sau'ke ajiyan zuciya tayi wani sanyi na shiga zuciyanta Shema ta kashe mata ido ta dau wayanta ta ci gaba da charting dinta,
"Hanifa tace" yaHaidar ka yafe mun.
"Beautiful na jima da yafe maki, remember I luv you very much.
"Toh yaushe zaka zo.....
"Murmushi yayi kafin yace" Ai nazo tun jiya, na sauka can gidanmu ne tare da amaryanki..... "Ai kaman wacce aka zabura haka ta mi'ke, amaryata kuma.
"Yes Beautiful amaryarki na maki amarya a lag na taho da ita kuga juna, yanzu haka tana nan tana jiran isowarki...... jifa da wayan Hanifa tayi ta sake sabin kuka, Shema ta mike tana tambayanta lafiya inaaa ta fice tayi side din mamy.

"Anty Hiba da mamy na zaune na tattaunawa Hanifa ta shigo tana kuka ta fa'da kan mamy tana kuka, gaba dayansu hankali a tashe suke tambayanta lafiya.... "cikin kuka take fadin "mamy wai yaHaidar amarya ya min, mamy wllhi ina sonsa dan Allah kice danyi duk abunda yake so mamy...... "mamy ta soma rarrashinta tana fadin " wasa yake maki Hanifa, Haidar babu wata amaryan da yayi..... mamy wllhi da gaske ne tana can gidansa haka yace mun...."Anty Hiba me zatyi inbanda dariya tana kallon Haidar dake tsaye bayansu shima dariyan yake...." kallonsu mamy tayi shida Anty Hiba yanda suke dariya..."wani mugun kallo mamy ta watsa wa Haidar kafin tace" tashi abinki daughter idan baki son amarya ai sai ya sakar min ke yaje can ya 'karata da amaryarsa... " A zabure ta dago tana duban mamy tace " mamy wllhi ni ina son shi bazan iya rayuwa babu shi ba saidai ya saki amaryar...." Caraf Haidar yace" Nima ina sonki Beautiful dina bazan iya rayuwa babu ke ba, ya 'karaso yana 'kunshe dariyar sa yace taso abunki yau zamu tafi gidanmu 'yan biki duk zasu ta'kura ki a nan, tinda baki son amaryar zan saketa idan muka isa gidanmu kinji..." wani kunya ne ya lullu'be Hanifa jin yanda ya wani 'dagota ya rungume gaban su mamy, Anty Hiba kuwa sai dariya take tana fa'din " kai 'dan gidana dama haka ake sonka lallai ka cire tuta. Mamy kuwa harara ta narka wa Haidar tace" zaka zo ka sameni ne kukan da ka daughter na tayi sai na rama mata. Anty Hiba tace mamy zane shi za'ayi, mamy tace shima ya sani idan ta kama a zanesan tsaf za'a zanesa akan daughter...... gaba daya suka sa dariya, mamy da Anty Hiba suka wuce sama suka barsu nan tsaye.
"Dago kai tayi baki a ture zata masa magana ya saka bakinsa cikin nata sun jima a haka kafin ya saketa, a ranar mamy ta Anty Hiba suka shirya mata komai nata Anty Hiba dasu Shema suka rakata can sabon gidanta, da farko mamy taki aminta ta tafi can saida Haidar yata magiya ya shaida mata sati biyu zaiyi kafin ya koma, karshe saida Abba yasa baki mamy ta yarda Hanifa ta koma.

"Da daddare misalin 'karfe tara ta gama shirinta na bacci tana zaune tana shafa turarruka na jiki da Anty Hiba ta bata wayanta ya soma ringing" My Handsome ne ya bayyana jikin screen din" tana murmushi ta 'daga wayan " Hello Handsome,
"Hello Beautiful shima ya fadi, ina fata yau kin shirya tarban mijinki dan yau musabaha sosai nake so muyi da Champ and Princess.
"Murmushi Hanifa tayi tace "kai Handsome, wai ina ka tsaya ne,
"Murmushi shima yayi yace aw kin dauka wasa nake, am serious nasan suma sunyi missing dina suna son jin 'dumin daddynsu, dariya tayi sosai kafin ta dan turo baki tace" Handsome nifa ban son kana kaiwa this hours a waje.
"Haidar yayi daeiya ya juyo yana duban su Sameer da suke can gefe yace yace" am sorry Beautiful wllhi su Aisar ne suka ri'ke ni kan shirye shiryen dinner dinsu, but am on my way now, wai suna gaida maman en 4.
"Hanifa ta zaro ido tace wai dama gabansu kake wnn maganganun... sai ka iso kawai tace gamida katse kiran.
"Dariya Haidar yayi ya 'karasa yanda su Sameer suke ya masu sallama, sai zolayansa suke ya wuce ya barsu.

"Tana jin 'karan bu'de gate gabanta ya wani fa'di, ta sake duban kanta a mirror rigar baccin dake jikinta yayi matu'kar mata kyau dukda cikinta da ya 'dan turo, ja ne rigar me kaman shimi, komai na jikinta kana iya gani dan very transparent haka rigar take. Ta dau na saman ta dan rufa kafin ta nufo downstairs. Shigiwansa knn yana kokarin rufe 'kofa ya hangota tsaye jikin staircase......"God have Mercy" abinda ya iya fadi knn, bude hannayensa yayi ta 'karaso ta shige cike, take 'kanshin turarrrukanta suka soma tafiya da Haidar wata duniya, a hankali ya masu sau'ki kan kujera yana shinshin wuyanta, kankace me ya soma kissing dinta ta ko ina, " a kunnenta yake ra'da mata I luv you beautiful. Ya ri'ko hannunta yace oya tashi muje kiga amaryarki kar ta gaji da jira....." A zabure ta mi'ke tana dubansa kafin tace" joke aside yaHaidar, peck ya manna mata a kumatu yace " kar ki damu Beautiful nafi sonki fiye da amaryar... kaman ra'kumi da akala haka ta bisa waje tana addu'an samu sau'ki cikin zuciyanta.
"Suna isowa waje juye juye ta soma ta ina zata hangi amarya..... " mayafin dake rufe da wata mita ya bu'de mata, kafin yace here is your amarya Beautiful, I hope you will like her.....
"Gana daya she's speechless, kallon motan take 'kirar Benz fara kal me shegen kyau.... Tsalle tayi ko nauyin cikinjikinta bataji ba ta ru gumesa tana fadin" I lobe you yaHaidar, I luv you soo much, Hanidar kaman a mafarki haka yaji zancen, shima ya dada matseta cikin jikinsa yace" I luv you too Haneefah. Hawayenta yaji a 'kirjinsa, ya dagota yana fadin" Beautiful me ya faru, ko baki son mota ne ko bata maki bane...." Girgiza kai ta soma kafin tace" yayi min sosai na gode yaHaidar, share mata hawayen yayi ya sureta suka shige cikin gida.

"A daren ranan sosai suka tausayawa juna, tausayinsa take sosai tasan yayi kewanta yayi 'ko'kari, shiko Haidar tausayinta yake yasan tayi 'ko'karin faranta masa a wnn dare dukda lalurar dake jikinta, wani kulawa na musamman yake bata, motsi ba motsi ba sai ya tambayi me take so ayi. A wnn dare Hanifa taga gata da soyayya wajen mijinta maras misaltuwa, har saida taji haushin kanta na hanasa kanta da tayi tuntuni. Haidar ya tabbatar mata shi'din me 'kaunarta ne.
"Washi gari ake kamun su Sumy, ji yake kaman kar ta fita su zauna a gida suci soyayyarsu, sai wani shagwa'ba yake zuba mata shi bai son ta fita wajen bikin nan, yana zaune yana kallonta tana shiryawa, kayan ya mata kyau sai tafiti das da ita.
"Mi'kewa yayi ya rungumeta ta baya suna fuskantan fuskokinsu a madubi yace" Beautiful kinyi kyau, nifa banson aje ana kalle mun ke, murmushi tayi tace " Kai Handsome wazai tsaya kallon mata me 'katon ciki kkwa yasan ni matar aurece, Haidar ya turo kansa cikin wuyanta yace" whatever nasan matata tafi kowa kyau a wajen dole na damu, ya danja hancinta yace 'karasa shirin mu tafi, I'll be waiting for you downstairs, kallo ta bisa dashi har ya fice, wani sonsa da 'kaunarsa ne zalla ke azalzalnta.
Chapter 67 · 0% Book details