← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 73

Sashe 68

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haka akayi kamu aka gama, duk wanda yaga Haidar yau zai gane tsantsan fari cikin da yake ciki, shi kansa jinsa yake kaman wani sabin ango. Washe gari mamy ta ha'da gagarumun walima, the next day aka daura aure da daddare angwaye suka ha'da Spectacular dinner na gani na fada, biki yayi da'di sai Allah son barka, ranar Sunday aka wuce da amare Lagos by flight, hakan yasa mutane 'kalilan ne suka raka su ciki harda Inna da Anty Hiba.
"Haidar kuwa sallama sukayi da angwaye dan yana nan sai nan da sati biyu ya koma, musamman da Beautiful dinsa da unborn Champ and Princess ya dauki hutu.

"Kulawa sosai suke bawa junansu ita da Haidar, wuni suke suna makale da juna, idan kaga ya fice toh gidan mamy ya taho, a haka suka shafe sati biyun su suna kwasan soyayya. Koda Haidar zai tafi sosai tayi kuka, tun ana washe gari zai tafi ya kusan kwana aikin lallashi, washe gari har airport ta raka sa, kaman kar su rabu da juna. Inna da kanta ta koma gidan Hanifa dan kula da ita....

*************************

"Kwanci tashi babu wuya wajen Allah yau gashi Hanifa ta shiga watan haihuwanta, tana zaune suna drama da Inna sai ta shanye wani ji'ko nasu na tsofi wai maganin za'ki.... sai ture turen baki take ita bazata sha ba" ana haka wayanta ya soma ringing ganin Handsome dinta ne yasa ta saurin daga wayan" cike da shagwa'ba suka gaisa,
"Haidar yace" Beautiful ya jiki haka, akwai wani abu ne.....
"Turo baki ta kuma yi tana hararan inna tace ba Inna ce wai sai nasha wani magani baka gani ba gaba daya ma is not hygienic bansan dame akayi ba....." A zabure Haidar ya mike yana fa'din" What! No way, saka wayan a hands free let me talk to her.... Hanifa tayi yanda yace, Inna kuwa sai sababi take mata, " ki tsaya biyewa namiji shi me yasani kuma shane dole kiyi....
"Muryan Haidar ne ya katse ta, " pls inna all those gargajiya things banso ana bata, it is not good for her and the baby...." Tabe baki Inna tayi tace yo ni nasan me kake fada, kai Zaki bari kaji dole tasha maganin zaki, ta mike tana gyara daurin kwali ta dubi Hanifa tace ku gama iyayinku ki zo ki sameni.
"Handsome kajita ko.. tayi magann cike da shagwa'ba.
"Kar ki damu Beautiful I'll be on my way gobe insha Allah, babu me ta'kura maki idan na dawo kinji. Da haka Haidar yayita lallashinta suka sha soyayyansu kadin sukayi sallama.

"Washe gari kuwa Haidar ya dira a garin Kano, haka sukata ya'ki da Inna a gidan duk wani shirgin maganin za'kin dake gidan Haidar ya zubar dasu Inna kuwa ta saka gaba da sababi. Da yamma lis suka shirya suka tafi akayi scanning aka duba lafiyan baby, nan Dr ya shaida masu babys uku ne a cikin Hanifa, ya'ki fa'da masu ne ya bari ya tabbatar, wai zakaga murna wajen Haidar, saida ya cika Dr Kasim da kyauta. Inna ma sosai tayi murna, Suna tafe a mota Haidae ya dubeta yace" Beautiful kinga Allah ya amshi addu'a ta, kin gado mamy, Allah ya raba lafiya, gaba daya ita da Inna suka amsa da ameen, kai tsaye gidan mamy suka wuce, Haidar ko kunya shi da kansa ya isar da wnn labari ga iyayen nasa wato Abba da Mamy.
"Wayyo Allah zo kaga murna wajen wa'an nan bayin Allah. Addu'ansu 'daya Allah ya sauketa lafiya.

👸🏻Queen Samy😍💄💋..........
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
80

"Satin Haidar guda a Kano, Hanifa kuwa har ta shige edd dinta da sati guda. Haidar ya'ki komawa Lag a cewarsa yafiso sai ta haihu ya koma, wani kulawa na misamman yake bata, kullum sai sumyi drama shida Inna gaba daya ya hana bawa Hanifa ko wanr irin magani sai na asibiti.

"Mislin 'karfe 9:30pm, ta gama duk wani 'dabi'un ta na bacci ta nufi 'dakinsa, zaume ta samesa saman gado laptop ne a gabansa yana duba mail 'dinsa. Yana ganinta ya sakar mata murmushi gamida bu'de mata hannayensa alamun ta 'karaso,
"Murmushin itama tayi kafin ta 'karaso ta zauna da 'kyar gefensa, hannunsa yasa ya tallafo bayanta gamida kissing gashinta yasan 'ko'kari kawai take amma cikin nan nata na mata nauyi.
"Handsome, ta kira sunansa gamida ri'ko yatsunsa.
"Juyowa yayi yana fuskantan ta kafin yace" yes my Beautiful.
"Yakamata ka koma bakin aikinka, kaga gaskiyan ka da ri'kon amanarka ya kaika maysayin da kake a yanzu. Zamanka a nan it will affect your work, you need to go back.
"Matse 'yan yatsunta yayi kafin yace" Beautiful family over everything, I can't leave you a situation din da kike yanzu, bazan ta'ba samun peace of mind ba ko na tafi, na sani sarai dauriya kawai kike but da alama cikin nan na baki wahala, I can't leave Beautiful, kinfi mun komai balle wani so called job. Ya rungumeta cikin jikinsa kafin yaci gaba da fa'din" am here for you Beautiful, together we will go through this, fatana Allah ya sau'keki lafiya.
"Hawayene ya ciko idonta bata san wani irin so yaHaidar ke mata ba, ha'kika tayi DACE samun miji irin yaHaidar sai an darje...... 'dumin hawayenta dayaji ne yasa hankalinsa mugun tashi, da sauri ya dago face dinta yana kallo.
"Oh no, what's wrong Beautiful, why those tears..... "Tell me kin fara jin ciwo ne.... ganin bata amsa sa baba kukan na 'karuwa yasa sa saurin mi'kewa yana shirin zura jallabiya....." Ri'ko hannunsa tayi ta mi'ke tsaye ha'de da rungumesa cikin jikinta tace" am fine yaHaidar, hawayen farin ciki nake, ha'ki'ka inajina tamkar nafi ko wace mace sa'a, you mean the world to me yaHaidar, sunan maraici nake amma ko ka'dan banta'ba experiencing bitterness na maraici ba, na taso cikin so da 'kauna daga wajen mahaifanka wanda ko iyayena iyakacin son da zasu nuna mun knn, snn na samu miji kaman kai me sona me 'kaunata wanda duk burin mace knn, yaHaidar ka ha'da abubuwa da dama, you and your parents means everything to me, Abba da mamy sun ri'ke amanan 'kannensu wanda da suna duniya a yau da sunfi kowa farin ciki, thank you for everything yaHaidar....... bai bari ta gama fa'da ba yasaka bakinsa cikin nata sun jima a haka wanda shima saida ya zubda 'kwalla.... rungumeta yayi cikin jikinsa tausayinta da tsananin 'kaunarta na shigansa. A hankali ya masu masau'ki kan wani resting chair dake can gefe cikin 'dakin,
"Murmushi yake yana duban face dinta ya saka 'dan yatsansa ya mayar mata da kitsonta da ya sakko guda daya kafin yace" Beautiful I should be the one thanking you, in spite of everything I have done to you but you still love me, you give me another chance, the only thing da zan maki shine na mallaka maki kaina completely.... yana murza 'yan yatsunsa cikin nata yake fa'din" Ni Aliyu Haidar *Mijin Haneefah* ne ita ka'danta tol nan duniya...... you're like an Angel to me, you're a great gift to me from our Lord. Ido cikin ido suke kallon juna hannunsu ri'ke dana juna kafim Haidar yaci gaba da fa'din " You are my Inspiration Haneefah, I love you.... "Rungumesa tayi tana cusa kai cikin 'kirjinsa. Ta jima cikin 'kirjinsa ko wannensu farin ciki yakeji maras misaltuwa kafin ta 'dago kai a shagwa'be tace"Handsome pls ka koma bakin aikinka kajifa Dr yace zan iya kaiwa 3weeks ma ban haihu ba... "Haidar ya da'da kwantar da kanta kan kafa'dunsa yana wasa da kitson kanta kafin ya kwaikwayi miryanta yace" kuma yace ai any moment from now labour na iya zuwa maki, ta yaya zan tafu na barki Beautiful, ya wani girgiza kai yana ta'be baki yace" no way I can't possibly do that...."Yanda yayi maganan saida ya bata dariya.
"Ta 'dan shnaye dariyan tana turo baki tace "but am not alone here, akwai Inna snn gasu mamy harma da Abba, idan ka'ki tafiya su Abba zasu ga kaman ka raina efforts dinsu akaina ne, I beg of you pls yaHaidar ka koma bakin aikinka.
"Murmushi Haidar yayi kafin yaja hancinta yace" wai kema har kin iya tsara zance ko, ok fine naji tunda korata kike, but nasan " my Champions da princess suna son na zauna, barin tambayesu idan sun yarda na tafi sai na tafi but idan suka 'ki, toh am not leaving.... "sunkuyowa yayi yana facing cikin yace" Champs princess do you guys want daddy to leave?.... "Yanda ya wani kafse yana maganan sosai ya bawa Hanifa dariya, itakam tana shan dariya idan taga yaHaidar ya dage da gaske yana magana da cikinta. 'Dago kai Haidar yayi yana kallonta yanda yaga sai dariya take " kashe mata ido 'daya yayi yace" kinji sunce basu so na tafi, sunfi so a haifosu daddy na nan..... sosai Hanifa ke dariya harda kwanciya bisa gado, mirginowa shima yayi ya rungumeta ta baya yana sha'kan ni'imtaccen 'kamshinta.

"Waswasa Haidar ya'ki tafiya gashi har ya share wajen sati biyu, saida Hanifa ta ha'dasa da Abba da mamy sukayi da gaske kafin ya koma Lag. Inna ma dama ba son zamansa take ba, dan tunda ya dawo kullum basu da aiki shida matarsa sai cin kayan fulawa a cewarta (pizza hot). Itako tafi son Hanifa taci tuwo yaranta suyi 'kwari.

"Tunda Haidar ya tafi kullum suna ma'kale a waya, cikinta ya kuma girma sosai gashi har yanzu bata haihu ba, gaba 'daya Haidar ya rasa samun kwanciyan hankali, kullum bayan sunyi waya da Hanifa sai sunyi da mamy ma yaji ko akwai wani abu ne, hankalinsa duk ya gaza kwanciya. Ga tafiya Turkey a gabansa duk ya rasa wanne zeyi gashi shine me jahorantar tafiyan. Idan kaga Haidar dole ka lira da raman da yayi. Ana gobe zaiyi tafiyan ya kirs wayan Hanifa. Tana ganin my handsome ne ta dauka cike da murna.
Chapter 68 · 0% Book details