← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 73

Sashe 12

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......[5/9, 6:18 AM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
24

"Hanifa tayi saurin saita kanta kana tace a'a mamy lafia lou muke zaune yasu Abba dasu Inna,. Mamy ta sau'ke ajiyan zuciya snn tace good that's what I want to hear. Ki kwantar da hankalinki kinji daughter dukda nasan ba son Haidar kike ba a hankali nasani eventually zaki soshi ne.... "Haidar dake ha'da takardu yana jinsu a ranshi yace "lalle ma mamy wato har lallashin yarinyar nan take tayi ha'kurin zama dashi dukda ba sonsa take ba, toh shi'din yana sonta ne, as a matter of fact he hates her like hell. Gajeren tsaki yayi ya mi'ke da takardun ya shige 'daki.
"Hanifa tana ganin ya tashi ta sau'ke ajiyan zuciya suja ci gaba da hira da maminta sai snn take tambayan su Shema. Mamy tace sun fita da Inna sunje dubo jikar 'kawarta ta haihu. Dariya Hanifa tayi tace "Oh Inna da fitina a daren nan bazata bari gari ya waye ba, mamy tace tab aiko kinsan halin Inna da 'daukan 'dumi... sukayi dariya duka biyun.... hira suka sha sosai da mamy karfe 8:30pm daidai sukayi sallama.
"Sosai Hanifa taji da'din yin waya da mamy ko babu komai taga mamynta kuma sunyi magana. Tana nan zaune parlor har lokacin Haidar be fito ba kan screen din computer din tabi da kallo hoton mutanen da aka nuna mata a matsayin mahaifanta su ta gani jikin screen din saidai harda wani 'dan matashin yaro da bazai wuce shekaru goma sha daya ba hannunsa ri'ke da baby ko ba'a fa'da mata yaHaidar ne baby da ya ri'ke ne de batasan waye ba, sunyi kyau sosai matar tana tsananin kama da mamy haka mutumin kuwa kaman kakin yaHaidar har yafi Abba kama da yaHaidar tana zaune tana nazarin pic din kaman daga sama taji knocking. Saida gabanta ya fa'di wani katutun ba'kin ciki ya taso mata "shikenan karuwarsa ta dawo ji tayi kaman kada ta bude kofan, wata zuciya tace ki bu'de kawai ki fa'da mata ta kyale maki mijinki. "Ta zaro ido waje tana fadin no no badai mijina ba Allah ya sawake ni kuwa na zama matarsa, bari kawai na bu'de mata suje can su 'karara. Da haka ta isa 'kofa ta bude.
"To her greatest surprised ba Latifa ta gani ba wann mutumin data gansa 'dazu da yaHaidar shi ta gani. Aisar kam mutuwan tsaye yayi yana kallon Hanifa sai yanzu ya da'da ganin asalin kyaunta, a ranshi yace na samu matar aure.
"Ganin ya tsaya yana kallonta shi be shigo ba shi be juya ba shi beyi magana ba yasata cewa "shigo mana. "Oh gosh her voice kills! Ya fadi a zuciyansa. Murmushi ya sakar mata snn yace yayan naki na ciki...... "kaman daga sama Haidar yake jin magann namiji a gidansa fitowansa kenan daga bathroom yayi wanka yana 'daure da towel a 'kugu baisan sanda ya nufo parlor babu shiri ba.
"Hanifa tace eh yana nan bisimillah shigo mana..... muryanta ne ya sar'ke sanda taji Haidar ya daka mata wani uban tsawa.
"Da uban wa kike magana a wajen...... Aisar ya karasa shigowa yana fadin take it esay navy ba wani bane nine. Hanifa kam gaba 'daya kunyan ganin yaHaidar tayi a haka farin fatarsa se she'ki take ga ruwa kwance luf a kirjinsa da sajensa.... gaba daya saita ru'de. Ba tare da ya kuma cewa komi ba ya 'karaso yajata da 'karfi zuwa 'daki. Jefata yayi kan gado yana mata mugun kallo yama rasa me ze ce mata yayi tsaki ya rufo dakin harda saka key snn ya wuce 'dakinsa ya shirya.
"Aisar de na zaune yana jiran fitowan Haidar mintuna kadan Haidar ya fito parlor. Mika masa hannu yayi suka gaisa fuska babu walwala snn ya zauna.
"Captain wai me 'kanwarka tazoyi Lag ne.
"Karatu tazo, ko da matsala ne?. Ya fadi a ta'kaice.
"No babu matsala, but why are you mistreating her. Ko baka son zamanta a gidanka ne, idan baka so sai ka kaita hostel mana.
"Wani uwar harara Haidar ya sakar masa kafin yace" and who do you think you are to tell me what I should do. Waima me ya kawo ka gidana at this hours in the first place hum.
"Aisar ya ta'be baki kana yace " what's wrong with you Haidar naga de mun saba zuwa gidan juna ko 'karfe nawa ne, your question sounds ridiculous. Anyway zuwa nayi naga beautiful and tunda na ganta I'll take my leave, ya mike yana saka hannu a aljihu ya nufi 'kofa. Haidar kam kasa tanka sa yayi wani irin 'kunan rai da beta'ba ji ba yake ji, wato Aisar ya biyo Hanifa ce. Yasan halin Aisar asalin womanizer ne. And he's pretty sure zai iya ta'kurawa Hanifa ta ko wani hali, kodai ya fa'da masa gaskiya ne. "Kai no way yaya ma zaice wann 'yar yarinyarce matar shi kawai dole ya takawa Aisar burki babu shi babu shiga masa gida ita kuma Hanifa babu ita babu fita ko 'kofa. Toh waima me ya fitar da ita har Aisar ya ganta? Ya daki hannu sofa da 'karfi sanda ya tuna 'dazu fa Aisar da kayan barci ya kalle masa Hanifa, wani haushin kansa dana Aisar harma da Hanifa ne ya turnu'kesa. Yana huci ya mi'ke ya nufi 'dakinta.
"Kwance ya sameta da alama tayi barci tana rungume da wani hoto, ya karasa ya zauna a bedside yana 'kare mata kallo, quite alright tanada kyau na 'daukan hankali ya sauke idonsa kan bakinta wanda yake kaman ta shafa lipstick ya ha'diye miyau wani mugun sha'awanta ya taso masa, take ya runtse idonsa yana 'karyata zuciyansa. Juyi tayi cikin barcinta hoton ya koma gefe a hankali ya 'karasa ya 'dauki hoton yana gani. Murmushi ya sake ganin hoton mamy ne tayi kyau sosai. Lallai ya yarda soyayyan mamy da Hanifa a cikin jinin jikinsu yake. Ganin tana shure shrene yasa sa saurin ficewa daga 'dakin zuciyansa cike da kwa'dayin kasancewa da Hanifa.....

👸🏻Queen Samy😍💄💋........
[5/9, 6:18 AM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
25

"Koda su Shema suka dawo mamy ta shaida masu Hanifa na gaishesu ba 'karamin haushi sukaji ba na rashin yin video call da ita.
"Oh we really missed, ni dama ban raka Inna ba wllhi cewa Sumy baki a ture.
"Me either, Sady ta fa'di rai 'bace.
"Mamy pls call them back kinji Shema'u ta fa'di.
"A ina kuka ta'ba jin an kira mutane karfe goman dare, ai sun riga sunyi bacci kawai saidai next time kunji.beside na masu hoto ai gashi ku gani. Har suna rige rigen jawo laptop 'din, wani ihun da'di suka sake.
"Wow this is wonderful, they really looks muah😘 cewan Shema.
"How sweet perfect match, lallai soyayya ba 'karya ba I never thought yaHaidar da Hanifa zasu falling love not even in my dreams, Sady ta fadi haka. Mamy kam ficewa tayi ta barsu suna kan zuba surutu.
"Hmm love at first sight, dama wnn fa'dan nasu yayi kama da love Shema ta fa'di.
"Sumy kam murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.. Sady ta 'dan bugeta a cinya tace talk mana am pretty sure akwai magana a bakin ki. Me zance Allah ya basu zaman lafia me 'dorewa. Ameen suka amsa baki daya.
"Kai guyz gaskiya nimafa auren nan zanyi wllhi, cewan Shema.
"Sady ta kyalkyale dariya tace" toh fah kice kin gaji da zaman gidan Abba😆.
"'Kwarai kuwa gawara nayi aurena naje naci soyayyana na more ko yaya kukace ga lada me tarun yawa, rayuwan duka duka nawa ne yau kaine gobe ba kai ba, idan ka samu opportunity gwara kawai kayi aurenka.
"Sady tace gaskiyan ki ne nima wllhi aure zanyi, ki duba baby sis da yaHaidar yanda suke more rayuwar su gwanin ban sha'awa muma ya kamata muje mu gina namu rayuwan.
"Sumy dai ta'be baki tayi ta mi'ke tana fa'din gwanda ku I have a lot to do... Shema ta bita da kallo baki a ta'be tace toh mu kuma masu zaman banza koh, ke na lura da anyi maganan aure se ki wani tashi ki fara zance boko wa mutane, naga dai wacce ta fiki son karatun karewa tana can tare da mijinta suna shan soyayyansu. Ta dubi Sady tace mudai zamuyi koh. Sady ta nodding kanta tace 'kwarai kuwa ai aure baya hana karatu. Suka tafe hannu suka ci gaba da firansu..
Chapter 12 · 0% Book details