← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 73

Sashe 59

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A staircase Aisar ya hadu da jumy me masu aiki, kallonta yayi yanda yaga itama jikinta a sanyaye tana gaishesa ko amsawa beyi ba ya shiga bu'de 'kofoffin yana fa'din mum! Mum! Mum, fitowa yayi a guje ya dur'ko daga stirs ya nufi kitchen yana tambayan maikatan ina mum, babu wanda ya iya basu amsa cikinsu, a tamanin Aisar ya dawo parlor yanda Dad ke zaune yana sharan kuka,
"Pls Dad tell me what's going on, whare is my mum, ka fa'da mun dad mutuwa tayi.... " Dad ya mi'ke ya ri'ko hanun Aisar ya zaunar dashi bisa kujera snn yace" Aisar my son please calm down...... " No Dad how could you expect me to calm down, ina mum 'dina take meke faruwa.... " Dad ya kuma matse hawayen da suka zubo masa cikin rawan murya na yanayin kuka ya soma fa'din" Aisar na dawo gida ban samu mum dinka ba an sace...... "Ai Dad bai gama rufe baki ba Aisar yayi tsalle ya cuku o wuyansa yana fa'din " ina ka kaimun mum din ka fada mun ina ka kaita.... A sittin securities din dad suka janye Aisar dake 'ko'karin kai dad lahira..." chief security din dad ne ya soma fa'din" Aisar you need to calm down, your dad have nothing to do with this, muma dawowan mu gidan nan kenn muka tarar da haka harta securities da suke gate a sume muka samesu, haba Aisar ka lura da halin da mahaifinka ke ciki.... " wani kuka ne kawai ya kufce wa Aisar ya zube a wajen yayi mai isansa kamannwanda ka zabura ya mi'ke ya haye sama ya fa'da dakin mum ya shiga bincike har 'kasan gado bai ganta ba, haka yayi daddaya da dakin karshe ya zube a kasa yana rusa kuka me tsuma rai, dad ya mike yabi bayan Aisar ganinsa yayi zaune dirshan a kasa yana kuka sosai matsowa yayi zai rungumesa, Aisar ya daka masa tsawa don't come near me, don't you dear come near me I hate you, you invincible.
"Aisar I swear I have nothing to do with this, can't you see am also suffering, matata ce ta 'bace Aisar da wanne zanji pls son don't turn your back on me..... " Aisar ya dago idanuwasa masu zuban hawaye yana kallon dad kafin ya karaso kusa dashi yace, idan ka damu meyasa na ganka a gida meyasa baka fita nemanta ba, meyasa baka kai report ba....
"Babu wanda banyi ba Aisar believe me my son, ko yanda kazo ka tarar da gidan zaka san cewa nayi.... wayan Aisar da tayi ringing ya katse dad, hannu Aisar yasa a aljihunsa ya ciro wayan, wata number ce ake kiransa kaman bazai daga ba sai kuma ya 'daga.
"ina magana da Captain Aisar Hashim ne....
"Aisar be iya cewa komai ba, dad ya kar'bi wayan yasa a hands free.
"Mutumin yayi wata dariya kafin yace" I know you can hear me little Brad, your mum is here with me..... " Ai a harzu'ke Aisar ya soma fa'din who are you, what do you want froom us I swear am gonna kill you, you Coward....." dariya mutumin ya she'ke dashi kafin yace " relax soldier, and don't do anything stupid idan ba haka na dauke kan mum dinka da bindiga, oh barin sa maka muryanta kaji nasan zakafi yarda.... " jin miryan mum dinsa tana kuka yasa hankalin Aisar tashi ya shiga fadin " mum kina ina ne fada mun mum yanzu zanzo na dauke ki..... " Dariya miyumin yayi kafin yace" Oh really navy, mum dinka bazata bar nan ba har sai ka bamu hadin kai..." don't you dear hurt my mother you idiot, I swear am gonna kill you, just tell me what do you want from us, how much money do you want....
"Captain knn, ashe har kayi ku'din da zaka fanshi mahaifiyarka da shi, toh ko worthless dad dinka bashida ku'din da zai fansheta....
"Ran Aisar yayi matu'kar 'baci" ka fada mun me kake so ko raina kake so zan fanshe mum dina dashi just tell me...
"Hahah now you're talking navy, " all I wanted from you is your testimony, if you testify againt Captain AA yor mum will be free, I'll release her. And if you try to do anything stupid or if you file a complaint ka kaddara mum dinka ta mutu, snn wann trader dad din naka shima bamu gama dashi ba tunda ya juya mana baya, he must pay for it. Kar ka mamce idan kayi gigin kai report uwarka ta bar numfashi.....
"That invincible coward Admiral, am gonna kill him with my very own hands, ya fadi haka gamida buga wani tsalle zai fice.... " da sauri Dad ya ri'ko Aisar yana fa'din " calm down son mu duba lamarin son, mum dinka tana hannun su zasu iya kasheta kaman yanda suka ce, please son you need to calm down..... rungume Aisar dad yayi banda kuka babu abunda Aisar keyi yana fa'din no no this can't be happening I can't loose my mother, why my mother meyasa basu dauke ni ba sai ita.... he just couldn't help it.
"Haka dad yaci gaba da bubbuga bayan Aisar yana basa baki. Dago kai Aisar yayi yana kallon dad da rinannun idanunsa kafin yace " get out, dad yace son am here for you.... " I said get the hell out of here, I wanna be alone, just leeeeeeave." A hankali dad ya mike yana share ragowar hawayen idonsa ya fice.

" Dad na fita ya wuce dakinsa ya kulle, wayansa ya ciro ya shiga neman layin Admiral, Admiral na dagawa ya fashe da wata dariya kafin yace" kar ka damu Mr chairman your wife is safe here, all we wanted is your son's testimony against Haidar. " Dad ya sauke numfashi kafin yace" look Admiral you forced me to do this so bana so a samu failure dan yanda naga Aisar yayi reacting it terrifies me alot, dan har sha'ke wuyana yayi,
"Admiral yayi dariya yace da'dina da kai ragwanci gashi you want to make money, kai fa naga alama bakayi shirin neman duniya da gaske ba, tunda kana son familynka sama da ku'di, ai idan zaka nema ku'di da gaske to a gefe ake ska komai sann a saka kudi a sama, sai an samu ku'di ake gina family, life is all about money....
"Dad yace ni dai na fada maka bana so a samu failure, dan ni na 'kagu ku gama shari'anku na tafi States dan na gaji da zaman nan, ku'din da na tara sun ishe ni...
"Admiral yayi dariya yace" idan EFCC basu ysareka ba knn, dan kasan kana da case na corruption me tarin yawa... tsaki dad yayi kawai yayi hanging dan gaba daya ji yake duniyan ta masa 'daci.

"Ranan haka Aisar ya wuni a 'daki ko fitowa beyi ba balle yaci abinci, yana son mum dinsa ita ta kula dashi tum yana yaro baisan soyayyan kowa ba sai nata, why is this happening, why his mum, dad ne yayi knocking a kofa baice komai ba, dad yasan bazai amsa ba dan haka ya shigo ba tareda yace komai ba, zama yayi gefen Aisar ya dafasa kafin yace" Son, wnn shine abunda nake gudu ma family dinmu, nasan Tanimu bazai 'kyalemu ba tunda muka 'ba'be, snn nasan bazai bari ka cimma burinka na taimaka wa Haidar ba, he's capable of doing everything son, saboda he's so desperate, bazai ta'ba yarda ya rasa matsayinsa ba..... " Enough pls Dad, I don't wanna talk about it, let's think of yanda zamu samu mum ta ku'buta daga hannun Animal dinann.
"Dad ya danyi murmushi yace that's my boy, yanzu kaci abinci muje muyi report..... " da mamaki Aisar ke kallonsa kafin yace report kuma haba dad, yanda mutumin nan bashida imani zai kashe mun mum dina, we think of another ways..... " Dad yace Aisar yaya zamuyi toh, you no I can't loose your mum..... I can't loose my only wife... Dad ya soma kukan munafunci. Kaman bazaice komai ba ya matso kusa da dad ya dan ri'ke hanunsa yace" I can't let that happen, I must find a way out, daga haka ya mike ya zuri car keys dinsa ya fice...

A ranar ma iya cewa kwana zaune Aisar yayi, yana ganin kiran Sameer na shigowa amma gaba 'daya ya kasa 'dauka, sosai abun ya dami Sameer dan baisan meke faruwa ba gashi washe gari ne shiga kotun su.

"Hanifah na zaune saman sofa tana cin tuwo miyan 'danyar ku'biya, kana ganinta yau zaka shaida tana cikin farin ciki. Inna ta dubeta tace wnn murnan duk na meyene, murmushi tayi har saida ha'kwsranta suka bayyana kafin tace haba Inna kaman kin mance daga gobe insha Allah yaHaidar zai bar gidan yari, zai dawo mu ci gana da rayuwar mu tare, babu abunda zai kuma rabamu sai mutuwa, mutuwa ma rana 'daya zamuyi insha Allah.
"Inna ta murmusa tace" Oh yaran zamani baku kunyan nuna soyayya wa junanku, 'yar ba'do naga da ai cewa kikayi baki sonsa amma ni nasan kina sonsa dan jikan nawa 'daya ne tamkar ga dubu.
"Dariya Hanifa tayi tace kai Inna ai shima yana sona, a haka momma da Amal suka fito suka samesu aka ci gana da hira cikin jin da'di.
"A ranar Hanif kusan kwana tayi tana sallah tana ro'kon Allah ya wuce masu gaba cikin wnn shari'a, kai duk 'daukacin masoyan Haidar kusan hakan ne ta kasance dasu.
"A 'bangaren Sameer kuwa ya kira Aisar yafi abunda yafi amma Aisar bai daga ba, karshe ma kashe wayarsa yayi, sosai abun ya dami Sameer, Aisar kuwa ba ya'ki dagawa bane baisan abunda zaice wa Sameer ba.
Chapter 59 · 0% Book details