← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 73

Sashe 50

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Yana zaune yana jiran a fito da Haidar, duba agogon hanunsa yayi yaga time ya soma tafiya, ganduroba daya ya fito ya sara wa Aisar kafin yace "sir lokacin da aka ware dan ganawa da prisoners ya kusa tafiya, snn shi Captain AA yace baison ganinka. "A hasale Aisar ya mi'ke yana kallon ganduroban nan kafin yace " what the heck are you talking about, look am not leaving here until I talk to him, bazan tafi ba sai munyi magana is better idan ya fito. Now go in an tell him bazan bar nan ba sai ya fito munyi magana.
"Sara masa gandiroban yayi ya juya yana fadin yes sir, right the way sir. "Rai 'bace kaman baisan kalman dariya ba ya fito, Aisar yabisa da kallo shima rai 'bace. Daga nesa Haidar ya tsaya yana watswa Aisar mugun kallo, Aisar ya taso ya 'karaso gabansa ya dan sassauta murya yace" how you doing, ko kallo bai ishe Haidar ba yace " as you can see. "Aisar ya fuzar da iskan bakinsa kafin yace zan tafi Kano gibe.... " da mugun mamaki Haidar ke kallonsa kafin yace " what for?, me zaikaika Kano kuma.
"am gonna confront them, zan samu iyayenka Haidar zan fada masu komai everything, duk abunda ya faru it was my fault, inaga idan iyayenka sun yafe maka suka taho lag su zasu saka kayi magana tunda ni ka'ki jin nawa.
"No Aisar, don't even start, you will make them more furious, I've suffered a lot, pls ka kyaleni haka..... " no Haidar bazan kyaleka ba, on the contrary kai ka za'bi hakan ma kanka. who do you think you are hum Haidar, what you're do I is awful, don't be so maniac Haidar. I can't let you do that.
"Na fada maka don't you dear meddle, babu ruwanka da tsakani na da family na.
"Cikin daga murya Aisar yace you can't prevent me, I've already made up my mind, zan samesu maybe su zaka jimaganar su ka bari a daukar maka lawyer, have a good day.... daga haka Aisar ya juya ya bar Haidar tsaye yana kallonsa, kafin aka zo aka shige dashi.

"Aisar yana komawa gida ya tarar da mum zaune a parlor, karasowa yayi ya gaisheta kafin ya zauna gefenta so tired and exhausted, nan da nan wata made ta jere gabansu da kayan sha, mum ta kallesa tace yaya dai son, any improvement. "Aisar da kwalla suka ciko idanunsa ya goge kafi ya soma fadin" no mum, he refused to cooperate, he already give up, I cannot loose him mum, I've to confront his family, they shouldn't abandoned him just like that, wllhi mum zan iya rantsuwa Haidar was innocent, daidai lokacin da Dad yake saukowa daga stirs, Aisar ya mike yana fadin wllhi mum who ever did this to my friend, he's not goin to get away with it, he'll pay dearly. Juyawan da zaiyi sukayi ido hu'du da dad, sa kai Aisar yayi zai wuce dad yace" naji kana ce zaka je Kano, barin fa'da mak babu hanuna idan ka jawo ma kanka wani abun, am warning you ka cire kanka daga hidiman yaron nan, he's a murder, kasan halin Admiral wllhi Aisar kaja ma kanka wni abun babu ruwana.
"A hasale Aisar yake fa'din" kana nufin na bari a yanke wa Haidae hukuncin kisa, kana nufin na bari ya amsa laifin da bashi ya aikata ba... " So what! Dad ya katsesa, ko ya samesa ba shi yaja wa kansa ba... " Dad don't tell me you've something to do with that, Aisar ya fa'di idon kyam kan mahaifin sa.." What the heck are you talking about Aisar, this is ridiculous, don't be so stupid, nidai na fada maka ka cire kanka daga hidiman yaron nan.
"Girgiza kai Aisar yayi kafin yace" I swear I will never rest until the truth finally came out... daga haka Aisar yasa kai ya nufi stirs.... Dad nankiransa ko juyowa beyi ba balle ya tsaya, " ya juyo da dubansa ga mum kafin yace" kina jina better stop your crazy son, before he does something stupid, something that I cannot deal with.
"Mikewa mum tayi tana masa mugun kallo kafin tace" Ina bayan 'dana 'dari bisa 'dari, and I'll give him my complete support na ceto rayuwan innocent Aliyu, the guy doesn't deserve that, kar ka mance irin 'ko'karin da yayi wajen taimakawa har Aisar ya nutsu har kaima..... "Enough Hannatu, dad ya daka mata tsawa, kuje kuyi duk abunda kuka dama amma wllhi kunji na rantse kome kuka jawo keda 'danki babu hanuna ciki... "kallon takaici mum ta bisa dashi kafin ta girgiza kai kawai ta wuce, tana mamakin hali irin na mijinta, he will never change.

*************************************
" Saukansa knn a garin Kano, hotel ya nema ya kama daki kasancewar already yamma tayi, washe gari da safe misalin 'karfe 9:am ya fita neman gidansu Haidar, kasancewar Abba ba 'boyeyyen mutum bane a garin yasa bai wani sha wahaln samun gidan ba.

"Mamy na daurawa Abba agogo yayinda yaketa bin fuskanta da kallo, sosai zaka gano ramar da tayi, Abba yasa hanu ya dago fuskanta yace " Mariya ta look up pls, kasa 'dago idonta tayi ta kalli Abba, ya da'da tallafo fuskanta sai hawaye yaga yana zauka sirara a fuskan nata, rungumeta tsam yayi cikin jikinsa ya shiga lallashinta. Suna a haka Sumy tayi knocking, da sauri mamy ta saita kanta gamida bata izinin shigowa, gaishe da iyayen nata tayi kafin tace Abba somebody is waiting for you down stirs, Abba yace wanene?
"I don't know him Abba, yaxe dai daga lagos yake, daga Abba har mamy saida suka sha jinin jikinsu, Abba ya gya'a kai yace ki shigo dashi parlor, toh Abba ta fadi sanda ta dubi mamy tace" mamy na wuce sch.
"Mamy tace Allah bada sa'a dear.

"Kallon Sumy Aisar yake tayi ta masa kama da wata but ya rasa a ina yasanta, haka dai har ta fice Aisar na kallonta na son tuno yanda yasan face din.

"Alhaji pls dan Allah ku taimaka nasan idan ku kukayi wa Haidar magana he'll cooperate, dan Allah kar ku bari a yabke masa hukuncin da babu laifinsa.
"Abba yayi gyaran murya yace "young man da ka tashi ka tafi da yafi maka sau'ki, ta yaya zamu kare mutumin da ya amsa laifinsa da kansa. "Alhaji a duba lamarin dan Allah... Abba ya mi'ke yana duba agogon hanunsa yace" ina abunyi idan bazaka damu ba ni zan fita... Aisar ya dubi mamy yace "Hajiya pls say something, Mamy ta dan kalli mijin nata taga babu alaman wasa a tare dashi... har Abba yakai 'kofa Aisar yace ok fine" a 'kara minti biyu dan Allah, abunda zan fa'da yanzu is very important...... " Haidar bai aikata laifin da kuke tunanin yayi ba da ganganci, he was trying to save a life, shiyasa ya aikata haka, I was the guilty one, laifina ne, ni nace masa idan bai bari na fita da Hanifa ba bazan basa map din ba, kuskurensa daya da bai fada mun Hanifa matarsa bace, amma wllhi believe me ko a da can I've no bad intentions for her.... cikin rashin gane ina Aisar ya dosa Abba ya juyo yana masa mugun kallo, mamy is confused, gaba daya kallon Aisar suke kafin Abba yace" Spell it out, yi mun bayani me kake cewa.
" nan Aisar ya kwashe komai ya fada masu.... wani sabon tashin hankali ne ya ziyarci Abba da mamy, knn Hanifa bata fada masu gaskiyan abunda ya faru ba, lallai Haidar baiga komai a rayuwa ba.... A fusace Abba ya mike ya nufi sashen Inna, Hanifa na zaune kan darduma da idar da sallan walha, Na tare da Abba yace da ita 'kala ba ya ri'ko hanunta suka nufo waje, Inna data ga haka dan bata ta'ba ganin hakan ba nan ta shiga bin bayansu tana tambayansa lafiya, Hanifa kam tama rasa ta cewa sai bin Abba da kallo kawai take yanda taga fuskansa babu alman walwala, ga ' kirjinta da yake faman lugude...
Chapter 50 · 0% Book details