← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 73

Sashe 47

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jawota dad dinta ya shiga yi a 'kasa yana wani huci yake fadin " do you really want to test my patience, ya mika mata wayan sanda ya kama gashin kanta wanda tsaban ja da yake yi har jijiyoyin kan sun kumbura snn oya go ahead go ahead call him back ki sanar dashi ni Admiral. Tanim Razak your Fucking Father zan kashe ki,
"Kuka kawai Latifa keyi tana fa'din pls let go of my hair, I beg of you pls. Jifa da ita yayi saida ta fasa goshinta. Juyawa yayi da niyan fita ya wani huci.... bai ankaraba yaji sau'kan flower verse a 'keyarsa Latifa ce ta lalla'ba ta 'dauka ta sau'ke masa.
"Abunka da soja wanda yasha training iri da kala, shafe wajen kawai yayi yaga jini..... wata murmushin mugunta yayi ya dawo yanda take..... " Idon Latifa ya 'ke'kashe cikin 'karfin hali take fadin, " Kai ba mahaifina bane, banida mahaifi, wllhi ban ta'ba ganin abun ysana abun 'kyama irinka ba in my whole life time, ka cuce ni ka zalunce ni,
"Latifaaaah ya daka mata tsawa, ko gizau bataji ba taci gaba da fadin " I dont fear you anymore, ka kasheni idan kaso, Alhamdulillah ko a yanzu na mutu na gode wa Allah da ya tsamo ni daga cikin ba'kin duhu zuwa haske, ta juya ta kalli mahaifiyarta dake dashe a wajen snn tace " ka zalunci baiwar Allah nan muma knn wayasan irin zaluncin dakayi wa sauran jama'a, kar ka manta Tanimu duniya ce wllhi ta ishe kowa riga da wondo, kar ka ga Allah ya barka kayita zalunci talala yake maka akwai rananr da zaka biya, ta 'daga hannu sama tace " Allah na ro'keka ka kawo mana nida mahaifiyata 'karshen zama a hanun wann azzalumin bawa naka, Allah na ro'keka kafin wnn bawa naka ya bar duniya Allah ka 'dai'daita shi ka 'kas'kanta shi....... Admiral bai iya jurewa yaci gaba da sauraren wnn addu'o'i na latifa ba ya kifa mata mari.... ya nausheta fa'duwa 'kasa da zatayi ta fa'di akan fashesshen kwalban flowern data jefeshi dashi, aikuwa nan ya huda mata ciki..... " Wani 'kara mai firgitarwa Mum dinta ta sake daga nan ta kwanta luf a wajen kaman bata motsi, 'karan da mum ta sake yasa guguwa ya kaure cikin dakin Lawo ya 'bullo.... " gaba daya Admiral ya rude ya razana da abunda yayi dan Latifa dai kam Allah ya kar'bi abunsa Allahu Akbar.....
"Dad ya shiga jijjiga ta yana fadin Latifa my daughter, meyasa kika mutu meyasa kika za'bi bijirewa umarni na ba da yanzu hakan bata faru ba.... dagosa Lawo yayi snn ya kwashe da wata dariya yace " Admiral. Tanim Razak ka kalli kanka yanda ka wani burkice da wnn 'yar taka mai taurin kan tsiya ta mace, mutuwanta shine rufin asirinka, mutuwanta shine zai maka maganin Aliyu, mutuwanta shine zai binne asirinka da yake gab da fitowa fili na kisan tsohon kwamandan rundunar sojin saman ruwa...... " hawayen taurin raine ke fitowa daga idon Admiral kafin yace Lawo fada mun, fada mun yaya mutuwanta zai zama solution to my problems.
"Lawo yayi wata dariyan basawa snn yace " yanzu kake magana soja, sharri zaka 'kulla wa yaron nan da gawarta shikenan, na baka clue saura ya rage maka ka shirya yanda abun zai kasance. "Kaman wanda ya sami ta'bin kai haka Admiral ya soma fashewa da dariya, har yana juyi a cikin dakin ya shafi kan Latifa yace " am sorry my dear daughter, mutuwanki ya zame mun gobarar titi a jos, ya kalli mum din Latifa yace wnn fah.
"Lawo yayi murmushi yace ka mance ka jima da aura mun ita, ai ranar daka ga wnn ta dawo hayyacinta to ranar asirinka ya tonu ko kuma na mutu.... " Admiral ya kuma fashewa da wata dariya yana jinjinawa Lawo.....

" 'Karfe 11:pm daidai ya gama shirin baccinsa, ya zauna gefen bedside yana kallon hoton Hanifa yana murmushi yana tuna rayuwar da sukayi a gidan tun daga farko har sanda incidence din da ya raba su ya faru, ya share kwallan da suka ciko idonsa, wani hoton ya dauko daga cikin wardrobe dinsa yana shafa mutanen jikin hoton, yake furta... " am sorry uncle am sorry Aunty, I couldn't make it, I have failed, but believe me I love your daughter more than anything in this world, I've a feelings zata haifa mun tagwaye masu kama daku, and I'll name them after you insha Allah.... ya rungume hoton ya furta I love you soo much. Ya jima yana tunanin rayuwa kafin ya dauko wayansa ya shiga neman layin Hanifa, ya kira yafi sau nawa bata daga ba... kasa hakura yayi ya shiga neman layin Anty Hiba dukda dare da ya dan ja....
"Anty Hiba ta razana da ganin wayan Haidar at this hour, ta tashe mijinta ta shiga nuna masa screen din wayan ganin sunan Haidar yasa sa duba agogo, gani yayi karfe 12 saura, shima dai ya dan razana amma kunsan maza ba kaman mata ba, nan yace mata ta daga taji ko lafiya,
"da kyar saida tayi addu'o'i kafin ta daga.... tana dagawa Haidar ya soma mata kuka nan fah hankalinta ya kuma tashi.... salati ta hau yi tana tambayansa meke faruwa.. " da kyar ya samu ya saita kansa kafin ya soma fa'din " Anty why all this, why is this happening, Anty I want her back I want her in my life, I became so miserable without her, why now Anty I couldn't help iy anymore...... " jikin Anty Hiba a sanyaye ta soma fadin " Haidar you need to calm down first idan kana so komai ya dawo maka normal, damuwan da kake yi haka is pointless bazai kara maka komai ba saidai ma ya kara frustrating dinka ya kara maka agony, pls Haidar you need to calm down, before you knw it zaka ji ana maka zance hawan jini sabida depression. Addu'a Haidar addu'a shine maganin komai, nayi niyan maka fada dan ina fushi da kai sabida abunda kayi dan mamy ta kirani and she told me everything, I was mad at you sosai Haidar amma yanda najika yanzu jikina ya mutu kasa bazan iya maka fadan ba, kasan ina sonka Haidar you're my best nephew and best friend, bansan meyasa yanzu kake boye mun abubuwa ba unlike before, idan abu ya shige maka duhu mukanyi magana muyi sorting out, sabida kusan age mates muke, na maka uzuri kai namiji ne ni mace ce na sani as time goes on wataran shakuwan mu zata ragu, but Haidar when it comes to matsala irin haka we need to discuss it before you does something, yeah quite alright nasani Hanifa matarka ce you've every right for her, amma ba ta haka ya kamata kazo mata ba, you'll end up running everything, kaga yanzu duka suna fushi dakai, Abba mamy Inna dakuma Hanifan,
" Murya 'kasa Haidar yace " Anty I admit, I made a mistake but ya kamata su understanding dina I was so desperate, snn su suka da'da sani nayi haka, cewa suke wai sai na saketa, Anty kinsani ever since we were kids, mafarki na shine na zama *Mijin Haneefah* kinsan the last abunda zan iya a rayuwata knn na saki Hanifa. Yanzu dai dan Allah kimin favor daya.
"Anty Hiba ta sauke ajiyan zuciya tace na fahimce ka Haidar, yanzu wani favor kake so na maka.
"Yauwa my best, so nake ki dauko Hanifa ta danyi hutu a wajenki, saboda ta 'dan mance da duk wani hard time that she's going through. Nasan zaiyi wuya ta kuma amincewa dani but with zata gane am the man of her dream, and zatafi zama more company a tareda ke,
"Anty Hiba tace I was thinking of that too, yanzu dai zanje kanon na samu su mamy da Abba insha Allah.
"Yauwa my Anty that's why I always love you, you always understand me. Pls Anty idan kina tare da ita help me persuade her ta yafemun and and.... ta dawo muyi zaman auren mu..
"Taa'kaitacen dariya Anty Hiba tayi tace " Haidar knn *Mijin Haneefah*
"Dariya shima yadan yi yace " wato kin tuno sunan tsokanar da kike kirana dashi then knn,
"Eh mana a lokacin idan na fada sai munyi fada.
"Yanzu kam ki fa'da ki sake fa'da saidai na maiki kyauta ma, ni yanzu zan kara a suna na ma, " Captain AA *Mijin Haneefah*....
"Dariya Anty tayi tace Silly you...
"Toh my Anty na gode sosai, ki gaida Faruq pls na tasar masa mata cikin midnight din nan..... dariya tayi tace zaka sani ai Haidar sai na hadaka da inna kasan itace maganinka.... dariya shima yayi yace ai tana daya daga cikin dalilin da yasa nake so ki dauko Haneefah kar ta koya mata masifa.... dariya Anty Hiba tayi ta tambeyasa aiki daga nan shima ya tambayi Ajmal yace ta shafa masa kansa little soldier kafin sukayi sallama.
"Sosai Haidar yaji dadin a ransa at least yanzu zai dan samu peace of mind, cikin jin dadi yayi kwanciyarsa yana mai tuno kyakkywan fuskar matarsa.

👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
[5/21, 5:49 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
62

" 'Karfe 8:01am daidai ya fito cikin shirin fita office, as usual yana sanye cikin farar kakinsa yayi kyau sosai, da mamaki yake kallon motan Latifa dake pake can gefe, ta'be baki yayi a ransa yace kome ya kawota nan this early morning kuma oho, cikin ko in kula yaci gaba da tadiyarsa sanda yake danna security lock daga jikin key dinsa ya bude motar, a haka ya karasa parking lot ya shige yayi tafiyarsa, masu gadi na faman gaishesa.

"Asubanci Anty Hiba tayi ta dira a garin KN, bata wani sha wahala ba wajen amimcewan su Abba, hasalima sunji dadin hakan, Hanifah ma hakan yafi mata sauki, tunda kullum ita kadai ke wuni Sumy na zuwa sch sai ko Inna, mamy kam tun bayan abunda ya shiga tsakaninta da yaHaidar wani irin kunyan mamy takeji, duk wani shwagwa'ba da take mata a da yanzu ta rage, sosai take jin nauyinta, ita kanta mamy ta gane hakan, kasancewar Kaduna da Kano ba wani tafiya me nisa bane yasa suka juya Kaduna a ranan, Hanifa sai dauki take Sumy ma ta waya sukayi bankwana.
Chapter 47 · 0% Book details