← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 73

Sashe 37

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hanifa da Amal zauna a parlor suna kallon animation momma ta 'karaso ta zauna tana zolayansau, Hanifa tace momma dama so nake na tafi gida tunda naji sau'ki sosai.jikin momma yayi sanyi ko ka'dan bata 'kaunar taji Hanifa tayi magann tafiya gida, musamman yanzu da suka saba, momma tace haka ne Hanifa bari Sameer ya shigo sai muji yanda tafiyan naki zai kasance, momma ta matso kusa da ita ta rungumeta tace "Hanifa zamuyi kewarki, jiki a sanyaye Hanifa ma tace nima zanyi kewarku momma ta shafi kan Amal tace "banson rabuwa da Amal dina. Sai snn Amal tace mummy wai ina zaki je. Hanifa tayi murmushi tace gidan mu zan tafi Amali na... kukan shagwa'ba Amal ta soma tana fadin" no nidai a nan zaki zauna, pls don't leave. Rungumeta Hanifa tayi tace ai mun zama 'daya Amali na zan rika zuwa wajenki da momma kema watarana zaki je wajena kiyi hutu. "Amal ta ma'ke kafa'da tace I want us to together forever pls pls pls.... haka ta rin'ka fadi wanda saida ta saka su Hanifa da momma dariya.
"Sameer ne ya shigo ya taddasu suna hiran tafiyan, yafi kowa son Hanifa ta kasance uwa ta har abada wa Amal, zama yayi yana taya su dariyan draman Amal, nan Hanifa ta dauketa suka nufi garden.
"Sameer yabisu da kallo har suka shige, ya juyo da dubansa ga momma dake kallonsa cike da kulawa, murmushi yayi ya shafa kansa, momma tace I know you're deeply in love with her son, " shafa kansa yayi yace yeah I do love her momma, ina sonta kaman yanda nake son Fauziya ina so ta maye gurbin Fauziya. Amma ban sani ba gaskiya ina tsoron sanar da ita... momma ta ri'ke hannayensa tace a hankali zak nuna mata irin son da kake mata, amma yanzu ka maidata wa iyayenta first sai abi komai in order, gya'da kansa yayi yace haka ne momma Allah ya shige mana gaba, momma ta amsa da Ameen. Ya mi'ke yana fa'din barin yi wanka naje sayo mana tickets, zuwa gobe sai mu tafi kanon insha Allah. Momma tace yawwa hakan yayi. Kan ya wuce saida yabi wajen su Hanifa da Amal a garden ya gansu sai wasa suke gwanin sha'awa, a ransa yake addu'an zama *Mijin Haneefah*.
"Bayan ya dawo ne Hanifa ta bada numbern mamy momma ta kira, sosai mamy taji dadin jin Hanifa na safe hand, saida tayi kukan murna, Hanifa tace su kwantar da hankalinsu zuwa gobe zata dawo da izinin Allah, da wnn labari me da'di yasa hankulan mutan gidan ya kwanta idan ka 'dauke Haidar da baisan me ake ciki ba, da wnn dadda'dan labari Abba ya samu strength na fita Office.

" 'karfe biyar da mintoci ya fito ya nufi sashen mamy, ko kallo bai isheta ba balle ta amsa masa gaisuwansa, karshe mi'kewa tayi tana masa mugun kallo kafin tace " gwara ka fice masa daga gida kafin yazo ya sameka.... daga haka ta wuce upstairs.
"Mikewa Haidar yayi jiki a mace ya suri motarsa ya fita, bai zarce ko ina ba sai gidan Hajiyan Saif. Zaune ya sameta a parlor, Hajiya ta razana da ganin Haidar kaman wanda ya jima yana jinya, yayi ba'ki ya rame, zama yayi dirshan a 'kasa ya kasa ce mata komai, hankali a atashe take tambayansa lafiya.... kasa furta koda kalma 'daya yayi, kukan da bai son ya fito ya shiga zarya a fuskarsa, ya kasa ce mata komai sai kuka.... sosai hankalin Hajiyan Saif ya tashi, Haidar yafi mintuna takwas a wajen ya kasa ce mata komai sai kuka.... 'karshe dai ta yanke shawarin kiran Saif a waya ta sanr dashi.... mintuna ka'dan Saif ya 'dauka ya iso....

👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
53

*This page is for all the members of Queen Samy Novels, thanks for your luv and support. I lUv YoU sO mUcH❤*

"Da mugun mamaki Saif ke bin aminin nasa da kallo, abune me kaman wuya kaga Haidar na zubda hawaye, bai gama karaya ba saida yaga irin ramar da Haidar yayi, ya 'karaso gamida kallon Hajiya alamun "meke faruwa".
"Girgiza masa kai tayi alamun "no idea, ta masa alama da kai akan su tafi sashensa... Riko Haidar Saif yayi suka nufi sashensa sanda yake samartaka, a parlor Saif ya zaunar da Haidar bisa sofa kafin ya fice ya nufi sashen Hajiya, ba'a jima ba ya dawo da bottle water, ya tsiyaya a cup ya mi'kawa Haidar, ba musu ya kar'ba ya kur'ba.
"Friend what's all this, what's going on. Why are you shading tears?. Ban ta'ba ganinka in this condition ba, pls talk to me Haidar meke faruwa.
"Haidar ya dago jajayen idanunsa yana kallon Saif kafin yace " I failed my parents, I failed my self...... I can't help it Saif, I can't loose her, meyasa ta 'bace mun, why things had to happens this way, I love her with all of my heart. I love her ever since she was born...... ya ri'ke hanun Saif sosai yake kuka... Saif ya shiga basa baki duk da ba wai ya fahimci asalin abumda Haidar ke nufi bane.. Saida yayi mai isansa kafin Saif yace " I don't get you Haidar pls spell it out, meke faruwa.
"Haidar be 'boue wa Saif komai ba tun daga farkon zamansu da Hanifa har I zuwa abunda yayi sanadiyan rba su.
" Kallon mamaki kawai Saif ke bin Haidar dashi kafin yace " why why Haidar, what on earth could possibly make you do that, it just doesn't fit in my head, haba Haidar haba that was so awful. You shouldn't have done that, you've made a huge mistake,
"I don't know Saif, I was stupid,
"Saif ya fuzar da iska, kallon Haidar kawai yake cike da tausayawa, rawan 'dari Haidar ya soma, ya ta'kure cikin kujera yana rwan sanyi. Kallon sa Saif yayi kadin yace " are you sick?, bai iya basa amsa ba sai daga masa kai da yayi. Saif ya taba goshin Haidar yaji zafi ra'dau" O gosh you having a fever, tashi muje asibit, girgiza kai Haidar yayi yace " no need, I'll be fine, just help me with panadol.
"Saif ya girgiza kai kawai ya fice ya nufi sashen Hajiya, zaune ya sameta a parlor ta rafka tagumi bayan ta gama waya da 'kawarta mamy ta sanar da ita komai, Saif yana shirin mata magana tace " Hajiya Mariya ta kirani ta sanar dani komai, oh my Allah give me some strength, ta fa'di gamida sauke numfashi.
"Saif yace Hajiya first aid yana ina, " me zaka yi dashi. "Haidar ne ba lafiya yanada fever. Hajiya tace "kuma" aida asibiti kuka tafi Saifu, Saif yace ya'ki yarda Hajiya.
"Ok ka duba 'dakin Jamila yana ciki idan jikin nasa baiyi sauki ba sai mu tafi asibiti, toh Hajiya Saif ya fadi gamida shigewa, Hajiya ta mike tana fadin barin hada masa ruwan shayi.

"Kwance Saif ya samu Haidar ya du'kun'kune cikin bargo, da 'kyar ya mi'ke yasha maganin nan bacci ya 'daukesa, koda Hajiya ta samu na bacci bata 'daga sa ba. Saif ya isa sashen Hajiya suna tattauna lamarin. Har kusan magrib Haidar be farka ba, Saif ya dawo daga sallah ya le'ka sa, ya samu ya tashi yana sallah, Hajiya da kanta ta shigo tasa Haidar ya saka wani abu a cikinsa,
"Saif ya kallesa bayan Hajiya ta fita yace I'll drive you home, girgiza kai Haidar yayi yace " no am staying here, I can't go there Saif, no one is willing to listen to me. "Saif ya fuzar da iska yace shikenn, idan Allah ya kaimu gobe sai muje mu sami Abba dga nan musake komawa can Lag din. 'Daga kai kawai Haidar yayi ya koma ya kwanta, kana ganinsa kasan 'karfin hali kawai yake amma baya jin da'di.

"Koda Saif ya samu Hajiya da batun taji da'din hakan, tace he needs your company, yanzu ka dauko Shema'u mu kwana da ita, Saif ya mi'ke yana fadin toh Hajiua sai na dawo.

"A parlor ya samu Shema tana kallo, yana shigowa ta 'dale wuyansa tana faman shagwa'ban ya barta ita ka'dai, zama yayi ya daurata bisa cinya gamida dafe kansa. Shema ta kallesa cike da kulawa, " Ya dai Sweet, is all well? Sauke ajiyan zuciya yayi kafin ya gyada mata kai kawai yana shafa gashinta, toh why the long face ta fadi fuskanta dauke da damuwa. Murmushi Saif yayi kafin yaja hancinta yace " tashi ki shirya mu tafi gidan Hajiya. Shema ta kafesa da ido kadin tace " wai meke faruwa ne, pls ka fada mun you making me nervous.
"Rungumeta yayi tsam cikin jikinsa kafin yace " I love you Shema, I love you so much, promise me you won't leave me, we'll always be together for the rest of our life. "Jiki a sanyaye Shema ta matse sa cikin jikinta kafin tace " You know I love you yaSaif bazan ta'ba barinka ba, we'll build our family together. Kiss ya manna mata yace tashi ki shirya. Ta mike ta shirya da kansa ya dauka mata kaya kala biyu. Ita dai sai kallonsa take.
"Zamu kwana gidan Hajiya ne, ta tambaya.
"Hannayenta Saif ya ri'ke ya zaunar da ita bisa gado kadin yace, you need to knw this, ko na 'boye maki zaki sani eventually. Nan Saif ya fada mata Haidar da Hanifa sun samu miss understanding and ya nemi Hanifa ya rasa, she disappeared. Sosai Shema take kuka, tana fadin "where she could have been possibly gone, I don't wanna loose her,.... rungumeta Saif yayi ya shiga bata baki yana fadin za'a sametq ta kwantar da hankalinta. Da kyar ya samu yayi calming Shema snn suka nufi gidan Hajiya. Haka Hajiya tayita rarrashin Shema tana bata baki.
"Saif ya tafi wajen abokinsa.

"Da safe koda Hajiya da Shema suka le'ka Haidar sun tarar na bacci, sosai Shema ta razana da ganin yanda yayan nata ya koma, ta tausaya masa sosai bata ta'ba ganin yayi irin wnn rama ba.
Chapter 37 · 0% Book details