← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 73

Sashe 43

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

" Abba ya dubi Hanifa dake zaune kasan carpet gaban inna sai faman wasa da 'yan yatsun hannunta take yace "Mamana kar ki damu I understand you, kar kiji nauyin fada mana abunda ke zuciyarki, babu wanda zai sake saka ki abunda baki so, idan kika ce baki son ci gaba da zama da Haidar, dole ya sawake maki, har kullum ke diyace me biyayya Allah ya maki albarka, hakika kin mana biyayya mun maki aure babu sanin ki, koda kika sani kikace kinji kin gani kinyi na'am da za'binmu, wann biyayya da kikayi Allah ya saka maki da alkhairi Allah kuma ya baki 'ya'ya wa'enda zasu maki fin haka. Gaba daya suka ce amin idan ka dauke Haidar da Hanifa wa'enda keta sake sake cikin zuciyoyinsu.
"Ke nake saurare Mamana kina son ci gaba da zama da Haidar a matsayin miji... "Dago kai tayi tana kallon Haidar shima ita yake kallo, gaba daya ya wani susuce kaman bashi ba,... da sauri Inna ta ture 'keyan Hanifa daga barin kallon Haidar.
"Girgiza kai Hanifa ta shiga yi ba tare da ta iya cewa komai ba, Abba ya dubeta duk ta basa tausayi kafin ya dubi Haidar yace " Aliyu, Haidar ya dago a zabure yana duban Abba jin ya kirasa da asalin sunan sa kafin Abba yaci gaba da fadin " inaso ka bani takardan sakin diyata yanzun nan..... kaman saukan aradu haka Haidar yaji saukan magana nan Abba, ya nemi yawun bakinsa ya rasa, duk da sanyin ac dake raysa cikin 'bargo da tsokarsa bai hanasa jin zufa ta karyo masa ba.
"Kai ake jira Zaki maza rubuto ka mi'ko mu fara shirshiryen biki... cewan Inna.
"Haidar kam baima gane me ake cewa, he's completely lost, ..... tswan da Abba ya daka masa ya dawo dashi daga duniyan da ya tafi.. na'am Abba, rai bace Abba yace am pretty sure kaji abunda nace, ka bani takardan sakin 'diyata.
"Abba pls don't do this, I beg you Abba don't let this happen, Abba Allah mafa baya son saki, Abba ina son matata I can't do without her.
"Abba yace au sai yanzu kasan da wnn, na sani Allah baya son saki amma shi ya halatta saki, duk auren da akwai cutarwa a ciki saki ya halatta, ka zalunci 'yar marainyan Allah, ka salwantar da rayuwarta and now you're expecting me na sake damka maka ita ka kasheta, you must be stupid comon rubuta mata sakinta yanzu nan ka bata let her be free.
"Girgiza kai Haidar ya soma yana fadin " Abba no, pls no, mamy say something pls... haba mamy na kema kin bar sona ne, pls don't this... mikewa Inna tayi ta riko hanun Hanifa ta dubi Haidar tace " idan ka gama dogon tirancin naka ka aiko mana takardan mu ko kaji sammaci a kotu, snn suka fice...
"Mamy kam 'kwllan da suka ciko idanunta ta shiga kokarin mayarwa, she never want this to happen, taso Haidar da Hanifa suyi rayuwa ta har abada a maysayin ma'aurata.
"Bazaka kuma maidani mutumin banza ba kaji na fada maka, na baka nan da gobe ka gama jimaminka snn ka kawo mun takardan idan baka rubuta takardan nan ba ni da kai ne, daga haka Abba ya mike ya nufi sama, mamy ma tabi bayansa suka bar Haidar kaman an dasa dutse. Innalillahi wa inna ilaihirraji'un kawai yake iya ambato, " a fili ya firta kai, inaa no no way, that can't happen, I can't loose her, she's my whole life. Mikewa yayi ya fice dama already car key dinsa na aljuhun sa ya nufi parking lot.
"Daidai nan ya hadu da Sameer yana parking ya dawo daga kai Sumy sch, kallo daya Haidar ya masa ya watsar wani muhun haushinsa yake ji, ji yake kaman ya kai mai naushi,
"Sarai Sameer ya gane Haidae shine jiya ya punching dinsa a hanci, ya dake dan Sumy ta sanar dashi ysakanin Haidar da Hanifa, karasawa Sameer yayi ya mikawa Haidar hanu alamun suyi musabaha, " wani mugun kallo Haidar ya watsa masa kafin yace " let me make this clear to you, Hanifa is my wife, don't you dear think of getting her, idan kuma taimako kayi an gode pls ka koma yanda ka fito we don't need you here, she's already happy with her husband. Wllhi kayi gigin shiga between us sai na kashe ka. Mark my word. Daga haka Haidar ya fincike motarsa ya fice a guje kaman zai tashi sama.
"Kallo Sameer yabi motan dashi har ya fice kafin yayi mirmushi yace " Allah sarki luv is given this guy a tuff time, tabe baki yayi ya girgiza kai kawai ya wuce.

"Yana fita ya shiga neman layin Saif, Saif ya dauka yana fadin Sojan Sea how fa, Haidar yace so far kaidai, where are you. Saif yace gani nan ina fitowa daga BUK, just dropped my wife, daga nan Office na nufa is anything the matter, Haidar yace ok mu hadu a office din, Saif yace alright see you then snn yayi hanging.

"Saif yana shigowa ya hangi motar Haidar a farfajiyan office din, karasawa yayi da motarsa yanda staff ke ajiye nasu motocin snn ya nufo wajen Haidar, gaisawa sukayi ta hanya musabaha kafin suka soma tafiya suka nufi building din.
"Saif ya bude fridge ya ciro drink mai sanyi ya ajiye gaban Haidar dake zaune kujeran hefen na Saif, gani yayi Haidar ya dafe kansa baiko ansa masa maganar da yake masa ba.
"Haidar where are you? Saif ya fadi yana ta'ba table din gabansa. Ajiyan zuciya Haidar ya sau'ke kafin yace " what if I lost her, kai no no that can't be.
"Saif baki sake yace ka soma magana kai kadai ne, wcece zaka rasan. "Galala Haidar ya dago yana kallonsa kafin yace " no bazan rasata ba, she and I are meant for each other, we gonna fix this insha Allah. "Saif ya cire hulan kansa ya ajiye bisa table ya soma dariya wa Haidar kafin yace " what's all this navy, haba kaikuwa kar mace tasa ka zare, nasan bazai wuce akan Hanifa ba. " gajeren tsaki Haidar yayi yace " this is not funny, yeah its obvious is about her, could you just imagine su Abba are asking me to get her divorce,.
"Saif ya kuma sa dariya snn yace " So isn't that what you want, ka mance kasha fada mun you never loved her, you'll never fall for her this and that bla bla bal..... "Enough dalla malam, Haidar ya katse sa, kafin yaci gaba da fadin " you never take things serious, idan bazaka tayani neman way out ba then fine, sai nayi tafiyata.
"Saif ya dan daina dariyan kafin yace " Haidar gaskiya this is pretty complicated, dama Hanifa tana sonka ne da... " And who told you bata sona, stop talking silly. Ya mike gamida daukan phone dinsa yana fadin" I must find a way out, I cannot loose her, she's mine. Saifa dai kallonsa kawai yake kafin yace "har zaka tafi. Ba tareda ya kallesa ba yace yeah zan barka kayi aikinka..... 'karan da wayansa tayi ne yasa yin shiru... Aisar ne me kiransa, ya danyi tsaki kafin ya daga.
"Har yanzu dai basu koma normal da Haidar ba, a dan takaice suka gaisa kafin Aisar ya tambayesa Hanifa, nan Haidar ya sanar dashi an sameta tana gida, hamdalah Aisar yayi snn ya sanar da Haidar ya dauki leave na sati daya, yanzu haka yana Zariya shida mum dinsa sunje ganin Family. Haidar yace good for you, Haidar be bari sunja hiran ba yayi masa sallama.

"Ya kalli Saif dake fito da files yace toh civilian ni na wuce sai kajini, Saif ya mike yana saka hulansa har waje ya rako Haidar bayan ya basa baki kan cewa komai zai zama normal inshaAllah.

"Yana gama parking a haraban gidan kai tsaye dakinsa ya wuce ya kulle kansa yana tunanin solution.
Chapter 43 · 0% Book details