← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 73

Sashe 42

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tana sallah ya gama shirinsa cikin 'kanan kaya black long sleeve shirt da faded jeans, ya fito ras dashi kaman ba shine ya jeme kwana biyun nan ba though akwai sauran raman.
"Tana sallamewa ta mike zata fita ya wani rikota ya matse cikin jikinsa yace " no even good morning kiss zaki wani fita... hararansa tayi tace what is good about the morning, bayan kasa na rasa sallan asuba, you should have wake me up ai.... rungumeta yayi yace "Oh am sorry my eternal, ba wai 'kin tashinki nayi ba, on the contrary na tasheki amma kika 'ki tashi sai gwarti kike, kin samu sound and deep sleep wanda kika jima baki samu ba, nasan dan kinjiki a jikina ne shiyasa, ashe kinyi missing dina that much.. " Turesa tayi tana masa mugun kallo tace " Allah sawake ni nayi missing dinka, I was exhausted ne kawai shiyasa kuma ni wllhi bana snowing ta karashe maganar tana shirin sa kuka.... " dariya taso basa ya dan dake yace Ok fine nayi recording ai idan kina musu yanzu na maki playing kiji.... dukansa a 'kirji ta shiga yi tana fadin wllhi bani bace saiko kaine... ganin zata yi kuka yayi saurin matset jikinsa yana fa'din, its ok ba ke bace I was mistaken ashe one of my girls ce da tazo tayamu kwana ta bani what my wife refused to give me ashe ita keyi.... 'dago kai tayi tan binsa da kallo da mugu mamaki kafin tace "Oh really, fine naji toh ni ina ruwana iyakaci dai idan na ganta a nan gidan korarta zanyi tunda ba gidansu bane, ni ka matsa mun na fice.... kallonta yake yanda ta 'daure fuska tamau kafin yace "meyasa zaki koreta, ba haka kikace wasu Abba ba, so kinga kowa yasan.... toshe bakinsa tayi tace " fine zanje na fada masu gaskiya yanzun nan right the way... " mirmushi yayai yana shafa gashin kanta yace " ai bazaki iya fada masu ba cos you love me.... "Galala take kallonsa kafin tayi murmushi ya'ka tace " idan kana tunanin sonka nake shiyasa na rufa maka asiri then you'er mistaken, never bazan ta'ba sonka, I did that saboda tsare kaina dan ni na samu mijin aure yaji haka zaiyi suing dinka ne snn kaga bazan so a tozarta ka ba ko dansu Abba, darajansu kaci...."Shutt up, ya daka mata tsawa... dago face dinta yayi suna kallom juna kafin yace " 'karya kike you love me, kina sona kina sona kina sona Haneefahh, kuma wllhi ni Haidar ni kadaine *Mijin Haneefah* duniya da lahira. You can even do your worse amma wllhi bazan sake ki ba, shi wanda kike cewa zeyi suing dina I don't care what he does, yakaini kotun koli na duniya am ever ready na duskanci ko meye akanki... kallon yanda yake huci kawai takeyi, a hankali ta furta " let me go, "Saketa yayi yace get out now... kallonsa tayi kafin tace " you have no ghost of chance, saki kuma ya zama dole.... " bakiji abunda nace bane, ki fice mu a daki kafin ranki ya 'baci... tsaki taja ta fice tana hararansa.... a zuciye ya jawota yana mata mugun kallo kafin yace " waye kike masa tsaki, ni sa'anki ne, dan kinga ina biyeki koh, toh kici gaba, idan baki da kunya kije wajen 'dan iskan mutumin nan ki ga abumda zan maku ke da shi... oya get the heck out of here.... kaman zata tashi sam haka ta fice gamida banging kofar... tana tafe tana hawaye.

"Mamy ta fito sashen Abba knn suka hadu da Hanifah, baki sake mamy ke kallomta kafin tace " daughter ya da kuka this early morning, ko Innan koroki tayi ne.... rumgume mamy tayi tana share jawaye tace " mamy ba yaHaidar bane...nidai kice ya sake ni wllhi na tsanesa... ta soma kuka, "rarrashinta mamy ta shiga yi tana fadi ki kyaleni dashi zai fito ya sameni, dole ya baki takardan ki a yau, wuce mu shige ciki kiyi break.
"A dining ta samu Sumy na breakfast nan ta tsaya wajent bayan sumy sun gaisa da mamy ta haye sama, Sumy ta kalli Hanifa tace ke kuma jiya shiknn daga kawo wa bako ruwa kika kaiwa mijinki koh kika kyale bawan Allah.
"Tabe baki Hanifa tayi tace Silly, ke wllhi I was kidnapped ne..... dariya Sumy tayi tace I see, so are you guyz fixing..... bata gama rufe baki ba Hanifa tace never that will never happen, dariya Sumy tayi tace uhm kunfi kusa ance ba'a shiga fadan mata da miji kai zakaji kunya, ta mike ta dau mayafinta da handbag dinta dake bisa kujera a parlor tace toh am leaving, zan tafi sch, Hanifa tace morning class kike da, Sumy ta girgiza kai tace wllhi registration ne ban gama ba almost a week ina abu daya, abun ba sauki sai a hankali.
"Jinjina kai Hanifa tayi tace su student ba sai kin dawo ni barin shiga nayi wanka.
"Mamy ce ta sauko ta mika wa Sumy key tace ki duba ko Haruna ya iso yayi dropping dinki, ta karba tana fadin toh mamy.

"Yana zaune a garden da newspaper a hannunsa ya hangeta tsaye a parking lot tana gyara files. A ransa yaji dadin ganinta har ya rasa dalilin hakan, he just couldn't resist starring at her.
"Jikinta ne ya bata ana kallonta, ai kuwa tana daga kai sukayi ido hudu, murmushin sa mai tsada ya sakar mata, itama ta mayar masa da martani, ta shiga takawa a hankali ta isa zuwa garden din, yana sanye cikin faran jallabiya kanta a 'kasa ta gaishesa, ya amsa yana kallonta face dinsa dauke da smile, tayi masa kayu cikin atampa riga da skirt green me zanen ganyen rogo yellow, ta yafa yellow veil a taikaice dai tayi kyau sosai.
"Dama ka tashi shine ka zo nan ka zauna, dan Allah kayi hakuri wllhi bamusan ka tashi bane da an kawo maka break.... "no kar ki damu ba yanzu zanyi breakfast ba, har kinyi shirin sch dinne. "Kai tayi nodding ba tareda ta kallesa ba, yayi murmushi da gefen bakinsa tana tuno masa matarsa Fauziya they have something in common, ya dago yana kallonta har lokacin idonta na kasa kafin yace " Ok toh ya naga kin tsaya a parking lot what are you waiting for, sai snn ta dago ta dan kalli gefe tace wllhi driver nake jira kuma har yanzu bai iso ba.
"Sameer ya rufe newspaper din gabansa yace " Shall I, ta dago tana dubansa da mamaki, daga mata kai yayi yace" I can drive you idan bazaki damu ba...
"Da sauri ta shiga girgiza kanta tana fadin " aa haba dai you don't have do that, zai zo yanzu nan, mikewa Sameer yayi yace I insist, pls don't reject my offer.
"Murmushi tayi tace barin sanar da mamy first. Snn ta shige ciki.

"Mamy wllhi bani na sashi ba, shi yayi insisting, Sumy ta fadi a shagwabe, Ok fine kice masa yana dawo wa ya shigo har ciki yayi breakfast, kuje Allah tsare hanya. Fuska dauke da fari'a ta fice tana fadin toh mamy.
"Yana hangota ya kunna motan data basa key din ya fito da ita nan Sumy ta shige suka dau hanya, suna tafe yace " ina saurarenki ina muka nufa, nan ta shiga masa kwatance har suka isa Bayero University...

"Da sallama ya shigo parlorn Abba dukda tunanin yanda zai fuskanci iyayen nasa da yake, dan rabonsa dasu tun jiya isowansu Hanifa, sanin darajan Sallama ce kawai yasa su amsa masa.
"Haidar ya nemi can 'kasan carpet ya zauna, ya soma gaida Abba dake breakfast ga mamy a gefensa tana tayasa, saida Abba ya 'dibi kusan mintuna uku masu kyau snn ya amsa masa da kyar, dan Haidar har ya cire rai Abba bazai amsa sa ba, mamy ma da kyar ta amsa masa gaisuwan nasa a ciki ciki.
"Shiru ne ya biyo baya sai dirin ac da sautin tv ne kawai ke tashi, Haidar ya mike a hankali zai fice Abba yace zo nan Haidar, babu musu ya dawo ya zauna.
"Ina maganar da mukayi jiya na takardan sakin Hanifa, ka bani yanzun nan.... zaro ido waje Haidar yayi yace Abba..... Pls Abbba don't do this to me, wllhi bazan iya rayuwa babu ita ba.... "dalla rufewa mutane baki, kana tunanin zaka 'kara raina mana hankali ne, kana tunanin zaka kuma manipulating dinmu ne kaman yamda kayi da, tunkan ranka ya 'baci ka kawo takardan sakin nan, dan 'yata ta gama zama da kai. Cewan mamy.
"Abba yace nama riga na gama magana zaka bani takardan sakin Hanifa like it or not, dan I won't force her to be with you again, za'bi na gareta, a randa ta gama idda ta kawo mun wanda take so zan aura mata..... kaman daga sama sukaji murryan Inna tana fa'din " Yo wani idda kuke magana, ai babu iddansa akanta jikata sabuwa take fil a leda, a yau ya saketa gobe zata auri loyan nan..... "Dan'kari ma'kari.... wani kallo kawai Haidar kayiwa Inna yama rasa ta cewa.
"Abba da mamy kam mamaki ne ya kamasu da kuma kunya, amma basu ce komai ba, Inna ta watsawa Haidar harara tace 'karya na fa'da daka wani kafe ni da idanuwa, ka musa mana idan 'karya ne, dama jira nake gari ya waye ka bata takardanta ko na maka ka a kotu,.
"Abba nidai wllhi ina son matata dan Allah mamy kisa baki wllhi I love her, don't even listen to this woman she's saying things out of anger. Pls Abba don't separate us, we both love each other..... ka gama 'karyan turancinka da zakayi amma saki kam kaman anyi an gama.Inna ta fadi tana zama bisa sofa.
"Abba ya dubi Mamy yace kira mun Hanifa, mamy ta mike ta fice kiran Hanifa.

👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 5:35 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
58
Chapter 42 · 0% Book details