← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 73

Sashe 65

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yau ta kama sauran sati uku biki tana zaune tana cin manda'ko da Inna tayi mata a parlorn mamy kaman daga sama tajiyo sallaman sa, daskarewa tayi tana kallonsa cikin kakinsa yayi matukar kyau ,tabbas shine ba gizo yake mata ba, murmushinsa me tsada ya sakar mata sanda yake shigowa, kasa ce masa komai tayi sai kallonsa da take babu ko 'kyafta ido, ya 'kara kyau sosai harda 'dan 'kiba yayi,
"Karasowa yayi ya zauna gefenta ha'de da rungumo kanta cikin 'kirjinsa yace I missed you Beautiful, ya kuke and my baby, ya sunkuyo da kansa saitin cikin yana mamakin yanda cikin ya girma sosai, kiss ya manna wa cikin kafin yace" Oh Champ and Princess daddy is here, you know what guyz I missed you so much.... "Hanifa de kallonsa kawai take, 'dago kansa yayi yana dubanta kafin yace" Beautiful kin 'kara kyau I love you, cikin nan ya maki kyau sosai tashi muga yanda ya maki.
"Bata tashi ba sai ta'be baki datayi, kallonta shima yayi kafin yace" wait aren't you suppose to be happy, ko baki murnan zuwan nawa ne uhum Beautiful. Com on tell me waya ta'ba mun ke ya fa'di yana ri'ko 'yan yatsunta.
"Baki a ture tace " toh ba kaine ba all these while ka'ki zuwa sai yanzu, and daka tashi zuwa koma kace mun kana hanya. "Haidar ya rungumeta cikin 'kirjinsa yana fa'din" Oh am sorry Beautiful I just wanted to surprise you, that's why ban fa'da maki ba, am sorry pls kinji, rashin zuwana kuma aikine ya min yawa Beautiful, nike ri'ke da mtsayin Acting Admiral kafin a saka sabo shiyasa ban samun time yanzu, commitments sunmin yawa Beautiful, yanzu ma zamewa ma ayyuka nayi na taho all the way just to see my Beautiful wife,.... zatayi magana ya zura harshensa cikin bakinta..... sosai yake kissing dinta gaba daya jikinsa 'bari yake lallai yayi missing Beautiful dinsa, gaba daya ya mance a parlorn mamy suke.... " ko kadan basuji 'karan foot step din mamy dake saukowa daga bene ba.... "Hanifa nata kiciniyan 'kwace kanta, "mamy kam sosai taji kunyan ganinsu a haka, da sauri tayi niyyan juyawa karaf sukayi ido hudu da Haidar, matsawa baya yayi yana shafa kai" Mamy sannu da sau'kowa, dole mamy ta amsa masa snn taci gaba da saukowa, Hanifa kuwa kaman 'kasa ya tsage ta shige ciki haka taji. Wani irin kunya ne ya mamayeta.
"Haidar saukan yaushe, mamy ta tambaya.
"Yanzunann shigowata mamy, mun sameku lafiya, nan suka soma gaisawa da mamy. Mamy tace yaya da zuwa kwatsam babu notice. Ko ka sanar wa matanka da zuwan naka ne.
"Haidar ya 'dan kalli Hamifa daketa juya manda'kon dake hanunta ta kasa 'dago ido, yana murmushi yana kallon Hanifa yace a'a mamy kawai ina so na nayi surprising dinku ne. Mamy tace toh ya aiki" Mamy akwai aiki fa sai godiya, Toh Allah ya taimaka, ameen mamy.
"Mamy ta kalli Hanifa ta 'bace shiru kaman bata wajen tace" Daughter ko a 'karo maki mand'konne, Hanifa ta girgiza kai tace a'a mamy na 'koshima ta mi'ke tayi hanyan kitchen...."Haidar ya bita da kallo har ta shige snn ya dawo da dubansa ga mamy yace " Mamy pls wake bata such kind of food,
"Harara mamy ta galla masa kafin tace" abunda take so ai shi za'a bata ban son iyayi. Haidar ya wani marairaice fuska yace but mamy gani nake kaman it will affect the baby, ki gani fah...
"Banson sakarci dankalin hausa nefa ba wani abu ba, murmushi Haidar ya dan yi ya mike yana fadin mamy barin 'karasa nagaida Inna . Mamy tace bazaka ci abinci first ba, no mamy Hanifa ta kawo mun side dina. Daga haka ya fice.
"Hanifa kuwa kasa fitowa tayi daga kitchen gaba daya kunyan mamy take ji sosai, a kitchen mamy ta sameta tsaye, mamy ta kalleta cikeda kulawa tace daughter akwai wani abu ne ko bakijin da'di ne, Hanifa ta 'dan sunne kanta tace a'a mamy lafiyata lou barin duba Sumy...." mamy tace ok ki kirara ku ha'da abincin Haidar sai ki kai masa sasnensa. Hanifa ta amsa da toh mamy snn ta wuce.

"Sanda tayi knocking a 'kofan ya gama shirinsa tsaf knn cikin 'kanan kaya, kallo 'daya ta masa ta sunkuyar da kanta he's always handsome, kallonta yake yanda take tafiya ri'ke da tray din kaman ya mata nauyi, da sauri ya 'karasa ya karbi tray din yana kallonta yace" sannu maman en uku, harara ta galla masa kawai ta 'karasa zata zauna ya wani saurin ri'keta kaman me tsoron kar ta fa'di.... abun saida ya bata dariya. Shima zama yayi gefenta yana binta da mayen kallo, gani yayi duk ranta kaman a 'bace yake.
"Wai ni Beautiful me nayi ne, mutum yazo yau amma ko special tarba bazai samu ba, haba mana, if I'm not welcome ne fine sai nayi tafiyata.
"Hararansa ta kuma kafin tace" oh baka masan abunda kamun 'dazu a parlorn mamy ba koh,..... kan tayi shiru Haidar ya soma dariya yana fa'din" Ai ita kanta mamy tasan nayi 'ko'kari nayi kewan matata, kinga yanzu idan nace zan tafi dake she won't prevent me.... kallonsa Hanifa tayi galala kafin tace" ina zan iya zuwa da wnn cikin kasan ma bazasu bari ba, ni kaina bazan iya zuwa ko ina ba. Haidar ya dan saka fuska kafin yace" ni kuma sai a maidani gauron dole knn, I just couldn't help it anymore, ya rungumota cikin jikinsa sanda yake fa'din Hanee I need you by my side, I want us to be together. A hankali ta zame jikinta tace should I serve you,
"Of course sure, ya fa'di yana gyara zama, ta gama serving dinsa ta mike zata fice, hannunta ya ri'ko yace ban gane miji na cin abinci matansa zata fita ba, na koya maki logic din, the moment mijinki na cin abinci yana kallon beautiful face dinki, soyayanki ne ke 'kara shigansa, so you are not going anywhere until I'm done,
"Yana cin abincin suna hira, saida ya 'koshi sosai, da kyar ya bar Hanifa ta fito daga sashensa. Bacci yayi bashi ya farka ba sai wajejen bayan la'asar, sallah kawai yayi ya fito dan yasan Abba ya dawo.

"Zaune ya samu iyayen nasa a parlorn Abba, gaisawa sukayi Abba ya masa sannu da hanya, nan suka tattauna gameda bikin 'kannensa da ya rage saura sati uku, nan Haidar ma ya shaida wa iyayen nasa ginin da yayi a GRA sosai sukaji da'din haka, Abba yace zasu je su gani insha Allah. Sun jima suna hira kafin Haidar ya fice.

**************************
" Washe gari da yamma yasa Hanifa ta shirya suje wani waje, babu yanda batayi ya fa'da mata yanda zasuje ba ya'ki fir 'karshe cemata yayi gidansu Saif zasu je. Da murnan ta ta shirya Sumy da Inna har na zolayanta, wai tunda Haidar ya dawo an soma ganin fari'anta, bata tanka su ba har ta gama shirinta cikin dohuwar rigar atampa flay ba wani makeup tayi sosai ba amma tayi kyau, ta fito ras da ita.... sashen mamy ta nufa ta fada mata sun tafi gidan Shema da yaHaidar, mamy tace a dawo lafiya snn Hanifa ta fito ta sami Haidar a parking lot.
"Tun daga nesa Haidar ke binta da kallo ta masa kyau sosai cikin nata ya mata kayu a jikinta 'das dashi. Da kansa ya bude mata marfin motan suka soma tafiya.

"Sosai Shema da Saif sukayi murnan ganinsu, Saif sai masa tsiya yake, Shema kuwa jan Hanifa tayu suka shige ciki, sun dan jima suna hira kafin Haidar ya mata waya ta fito su tafi, badan Shema taso ba haka ta rakota har waje.
"Ganin sun 'dau wani hanya daban yasa Hanifa cewa yaHaidar ina muka nufa,
"Saidake zanyi ya bata amsa,
"murmushi kawai tayi bata kuma cewa komai ba, kallonta Haidar ya 'danyi kafin yace "ko zaki driving dinmu ne.
"Girgiza masa kai kawai tayi batare da tace komai ba.
"Haidar yace "Beautiful banson shir shirunkin nan fa, open your mouth and talk, nidake fa we're one. Ko my champion da princess ne ke hanaki magana.
"Dariya kawai tayi sanda yake horn a wani makeken gida wanda basi an fada maka na alfarma ne, me gadi ne ya wangale gate Haidar ya rage glass suka gaisa..
"Hanifa sai bin gidan take da kallo, da gani sabo ne ga flowers ta ko ina, Haidar ya gama parking ya dubeta yace muje ko, ko bazki iya takawa bane na 'dauke ki...
"Kai yaHaidar stop being silly. Ta sa 'ka ta sau'ko tana fa'din ina muka zo yaHaidar, 'karasa yayi jikin 'kofa yasa mabu'di ya bu'de, baice mata komai ba sa suranta da yayi ya nufi cikin gidan da ita.
"Ya salam, ai har interior din yafi wajen, komai 'das 'das gwanin sha'awa dagani furniture din zakasan komai order dinsu akayi.
"Ajiyeta yayi bisa sofa, ya ha'de hannyayensa yana dubanta kafin yace" Mrs Aliyu, take a look of polishing and tell me if there is anything da bai maki ba ko kina so a canza,
"Da mami take kallonsa kafin tace" ban gane ba yaHaidar nan 'din inane.
"Haidar ya mi'ke yana murmushi kafin yace" this is your house, everything here is yours including me my self.
"Murmushi ta soma ta mi'ke ta rungumesa tace" yaHaidar zamu zauna a nan Kano knn, oh am so so glad, this is spectacular, thank you yaHaidar.
"Kiss ya manna mata kafin yace anything for you love, ya rungumeta cikin jikinsa yace kinfi so mu zauna a nan ne? Gyada masa kai tayi tana kwance cikin jikinsa. Shafa gashin kanta yake snn yace" Beautiful yanayin aikina bazai bari mu zauna a nan ba saidai mu riga zuwa hutu.
"Ta 'dan bata fuska tace nidai ka barni a nan.
"Beautiful bazan iya jure rashinki ba, I promise you zamu ringa zuwa hutu akai akai, kinji, ko kinaso nayi retire ne... " A hankali ta girgiza kai alamun a'a, ya wani da'da kwantar da kanta cikin 'kirjinsa yace" idan kinaso sai nayi, your happiness is mine. Oya tashi muje kiga gidanki ko, ri'kota yayi cikin arm dinsa suka soma zagaye ko ina a gidan.
Chapter 65 · 0% Book details