← Book details Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 73

Sashe 66

Mijin Haneefah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Three bedrooms ne a asama snn akwai guests room a 'kasa, sai kitchen da mamakeken parlor with dinning area, sosai gidan ya burgeta babu wani shirgi ko ina an sama masa abunda ya dace dashi, daga waje kuwa har jim akwai sai wasu kujeru na sha'atawa, ganin hard playground na yara a gidan yasa Hanifa jin da'di sosai, lallai Haidar zai kasance irin iyaye masu son farin cikin yaransu. Sunzaga ko ina kafin suka dawo cikin gidan.
"Har akayi magrib suna nan, sanda ya dawo daga masallaci zaune ya sameta a 'dakin dake a matsayin nata ta idda sallah, zama yayi hefenta ya shiga ya soma yaye mayafin jikinta.... ta dago kai tana dubansa bata ankara ba saiji tayi ya soma kissing dinta sosai, daga yanda yake sarrafata zaka gane yana tsananin bu'katarta, itako Hanifa ko ka'dan batason shiga irin wnn yanayi, batasan ko cikinne kesata haka ba oho.... turesa ta soma yi tana 'ko'karin 'kwace kanta.... "matseta Haidar yayi cikin jikinsa har saida ya tuna da lular dake jikinta na ciki kafin ya 'dan sassauta ri'kon ya soma fa'din " pls Hanee, don't I beg of you, can't you see am dying to be with you. Kuka ta sake masa jinnyanda yake juyata.
"'Dago idanunsa yayi wanda suka koma jazur kafin yace" ki daina kuka bazan sake ba tunda baki so, but inso ki sani nima mutum ne kaman kowa I also have feelings yeah, ke ka'daice matata kece hakki ya rataya a wuyanki ki sau'ke wnn nauyin, remember I came here for you, na baro tarin ayyuka na ne dan nazo na ganki naji matsalollinki a matsayinki na matata, na sani yau da zan koma bin mata bazaki so ba, kodayake ba sona kike ba shiyasa baki damu da bu'katata ba, you were forced to be with me, ki sani Haneefah I love you with each and every breath, and I will love till my last breath. But I won't force you yo love me back, all I know is that I do love you. Snn idan kince kar na sake kusantar ki zanyi as you wish if that will make you happy, oya tashi mu tafi.... ya mike yana gyara rigarsa.
"A sanyaye ta mi'ke tana share hawayen idonta ta biyosa waje, ko sallama da gate man Haidar beyi ba, yana daga masa hannu ya fice a guje. "Haka suke tafiya cikin motan babu me cewa 'kala.

"Yana gama parking ya bude motan ya fito ko kallo bata ishe sa ba, jiki a sanyaye ta sauko, ba tare da ya juyo ba ya danna security lock daga jikin key.

"Parlorn mamy ta wuce kai tsaye, mamy na ganinta tace kun dawo daughter, kai ta gyda wa mamy tace eh mum dawo mamy suna gaishe ku snn ta karaso ta zauna bisa sofa, zamanta yayi daidai ta shigowan sumy dan dama ta ganta waje tare da telansu, zama Sumy tyi tana mitan wai Sady ta barta da komai ta'ki dawowa. Mamy tace toh zata bar karatunne tozo ta maki me, idan hidiman bikin ne ba gaki a gari ba ke sai ki maku komai ai, tinda tace sai week din bikin ta dawo, Sumy ta dan turo baki tace wllhi mamy da nice Sady fah bazata mun haka ba, Mamy tace ban son shashancin banza idan bakuyi wa 'yan uwanku abu ba ma waye zakuyi. Am sorry mamy Sumy ta fadi a hankali, mamy kam mikewa tayi ta shige t
amsa wayanta dake ringing.
"Hanif dai jinsu kawai take amma hankalinta gaba daya baya tareda ita yana can wajen Haidar...." Sumy ta 'dan ta'ba ta tace maman en 4 na mashi maganan 'dinkin ankonki nace gown za'a maki dan kar ya kasa, inaaa Hanifa kam jin Sumy kawai take amma da alama bata fahimtan me take cewa, 'karshe mi'kewa tayi ta nufi sama,.. "Sumy ta bita da kallo dan tasan definitely wani abun na damunta.

"Basu kuma haduwa da Haidar ba har ta kwanta, ranar gaba daya kasa bacci tayi tana tunanin yaHaidar, ji take bata kyauta masa ba, gaba daya saitaji babu da'di ta k'udiri niyyan bazata sake hanasa kanta ba.
"A 'bangaren Haidar kuwa sosai abun ya damesa, meyasa Hanifa take masa haka, shi a halin yanzu babu macen da yake sin kasancewa da ita sai ita, wata zuciya tace kila bata sonka ne shiyasa taje maka haka tunda bata ta'ba furta maka kalman so ba, take yaji zuciyansa na masa zafi sosai, hukumcin da yanke yafi masa gwara ma kawai ya tafi zaifi samun sau'ki.

"Washe gari wajejen 'karfe 9 saura ya shigo sashen mamy " a 'daki ya smu mamy alamun shigowarta knn itama, mamy ta dubesa da mamaki ganin sa cikin shiri,
"Haidar badai tafiya ba, gaisawa sukayi da mamy kafin yace eh mamy zan wuce dama kwana biyu kawai zanyi, Hanifa da tun shigowarsa ta tashi amma bata bu'de ido ba taji gabanta yayi mugun fa'duwa wanda yasa har abin dake cikinta ya motsa,
"Mamy tace Abbanka ya sani.
"Eh munyi sallama jiya da dare, ya 'karashe maganar yana duban Hanifa dake kwance bisa gado idonta alumshe.
"Mamy ta dune shi ganin yana kallon Hanifa tace" gashi Hanifa na bacci kuma, ko zaka jira ta tashi ne, ko zakaui missing flight ne.
"No mamy karki damu ai mun riga munyi sallama jiya...... "Innalillaji wa inna'ilaihirraji'un haka Hanifa tace a zuciyanta, kardai yaHaidar yayi fushi da ita sosai, wayyo Allahn ta meyasa zai tafi.
"Mamy tace toh bikin fah zaka samu zuwa inji de.
"Ya 'dan dubi agogon hannunsa kafin yace" Mamy gaskiya zuwan nawa is under probability am not quite sure idan zan samu zuwa.
"Haba Haidar ya kamata kayi squeezing kazo ko dan Sameer da Aisar.
"Ok mamy insha Allah zan duba lamarin. Ni na wuce.
"Toh Allah ya tsareko, ka shiga ku sake sallama da Abban naka bai fice ba tukunna. Haidar ya amsa da toh mamy kafin ya fice.

"A hankali Hanifah ta shigar da kanta cikin bargo hawaye na sau'ka bisa 'kuncinta, wani irin son mijinta take ji maras misaltuwa, ji take kaman ta ri'ko shi ta hanasa ta fiya, gashi ko sallama basuyi ba, tana jin fitan mamy ta soma kukan da gaske, 'karshe toilet ta shige tayi me isanta....

👸🏻Queen Samy😍💄💋........
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
79

"Saidatayi kuka me isanta kafin tayi brush ta wanke face dinta ta fito, zama tayi gefen bed tana tunanin yaHaidar gashi ya tafi ko sallama basuyi ba, lallai yayi fushi da ita sosai, kaman ance ta juya gefen bedside ta kalli wani envelope ajiye. "Dauka tayi tana juyawa note ta gani dan samansa, bude note din tayi ta soma karantawa.
_I already left, ga wnn kiyi hidiman biki, take care of your self and baby. I luv you_

"Wani hawayen ta kuma sharewa, tana bude envelope din taga bandir din 'yan 'dubu dubu ne wato hundred thousand, sababbi fil fil dasu. "Note din ta kuma karantawa Allah sarki yaHaidar he loves her with all of his heart, what she does to him is unfair. Wayanta ta ciro ta shiga neman layinsa yayita ringing ba'a 'daga ba, 'karshe taji an kashe. 'Kirjinta ne yayi mugun bugawa, shikenn yaHaidar yayi fushi da ita sosai, take taji wani sabon hawaye na zubota, she loves him without a limit..... Tana zaune mamy ta turo 'kofa, tayi saurin share hawayen idonta ta 'dan saita kanta ta soma gaida mamy.
"Kallonta mamy keyi kaman me son gano wani abu tace daughter lafiya de ko, gyda kanta tayi tace lafiya mamy,
"Haidar ya wuce ya shigo kina barci, mamy ta fadi sanda take bude sip.
"Murmushin karfin hali Hanifa tayi tace "eh munyi sallama mamy, ta dauki kudin ta mikawa mamy tana fadin" ga wnn ma ya bani wai nayi hidiman biki nikuma bana bu'kata mamy.
"Mamy ta dubeta bata amshi kudin ba tace" keep it with you daughter, you might need it ko ba yanzu ba, kinji. ALLAH yayi Albarka, a sanyaye Hanifa ta amsa da ameen. Mamy tace maza ki sauko downstairs breakfast dinki is ready, ko kinfi son a kawo maki nan. Girgiza kai tayi tace a'a zan sauko mamy. Daga haka ta mike daga zaunen da take.

"Gaba daya haka ta wuni ranan babu walwala, ta alakanta rashin kunna wayan yaHaidar da maybe yana jirgi ne, toh amma har yamma bai kunna ba, duk sai taji ta damu.

"Haidar kuwa yana isa wayan mamy ya kira ya sanar da ita ya sauka lafiya, Hanifa da akayi wayan a gabanta mikewa tayi ta shige daki tana matsan hawaye, ta kuma kira amma saijinta tayi a kashe, kwanciya tayi a wajen ta rika kuka maras sauti, gaba daya ranan haka ta wuni ta kwana kaman maras lafiya, koda mamy da sumy suka tambayeta sai ce masu tayi kawai bata jin dadi ne, babu yanda mamy batayi su tafi asibiti ba amma ta 'ki.

"Wasawasa saida Haidar ya shafe sama da sati beko kirata, kullum yayi waya da mamy sai ya tambayi lafiyan Hanee da unborn dinsu, Hanifa kuwa kullum cikin tunaninsa take, bata da burin da wuce ta ganta kusa dashi yana nuna mata soyayyansa me class.
"A 'bangaren Haidar ma duk sai yaji kaman be kyauta wa beautiful dinsa ba, at least he needs to be much more understanding with her, ya kamata yayi considering situation dinta, he shouldn't have judged her the way he did, pic dinta na saman screen din wayansa yaketa bi da kallo, yana sonta yana son kasancewa da ita, amma hukumcin da ya dauka ne kawai zai tabbatar masa matsayinsa a zuciyan Haneefah. Kissing pic din yayi ya furta "I love you Beautiful.
Chapter 66 · 0% Book details