Sashe 6
Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wanne dalili kk dashi daya wuce ka nuna min ka isa da kan ka?"
"Umma ba haka bane, maganar da akai jiya ne naga bai kamata naci gaba da zama da Aeeshaa cikin rufi daya ba,bayan an bama wani ita, wahala kawai xan sha, zuciyata zata ci gaba da son ta, bayan kuma na san ba zata zama mallakina ba"
Umma ta tausaya masa, dan haka ta amince da dalilin shi, sannan ta roqe shi daya dinga zuwa suna gaisawa, koda lokaci zuwa lokaci ne, anan ya karya,ya wuce wajen neman aiki, dan shi yafi son yayi fafutuka da kan shi,baya son a nema masa aiki a gida.
*********************
Kwanaki na tafiya, watanni na kamawa suna qarewa, shekaru sun ja, Aeeshaa ta kammala makarantar ta ta secondary, jarabawar su ta fito ta samu 4 credit, fada wajen umma ba a magana, yaran qawayen ta dik daga mai 8 credit sai mai 7.
"Dik karatun naki anan ya qare? Dik alhuda hudancin naki iya 4 credit kk tsaya?"
"Umma su fa biya sukai aka masu, ni kuwa da kaina na zauna na rubuta jarabawar, ba satar amsa,ban kwafa ba, Umma murna ya kamata ki tayani a wannan ranar ba fada ba, dan Allah i want to be happy just for today,"
"Ba za a barki ki happy din ba, na bata kudi na da lokacina a banza, sai ki fadan wace makaranta zaki ci gaba yanzu? In ba aure ba,"
Cikin zazzaro manyan idon ta ta maimaita aure, tana kada kai, bata da burin aure yanzu.
"Kwarai aure zamu maki, Baba General ya tsaida maki da miji, gobe ki shirya kije can, ki masu hutu kuma ki san mijin naki,"
Zama tayi a wajen hawaye na sauka a kuncin ta, tana karanto addu'ar neman samun sauqi akan wannan hali da take ciki,
"Aure za a min ni Aeeshaa,nawa nake?".......
*Goma kk yannan, aure dai ba fashi🙊*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼
*BY HAERMEEBRAERH*
Page 5:
Washegari Aeeshaa ta hada kayan ta ga murnar zuwa taga 'yan Uwanta, bayan tsahon lokaci, ga taraddadin me zata je ta tarar, tinani tai tayi,ko wannan dalilin ne ya hana Umman ta barin ta zuwa gidan kakannin nata, to ko Yah Sabeer ne mijin da aka zaba mata? Tinda ya bar xaman gidan sai dai yazo ya tafi, wataqila ma bai son ta shiyasa ya rage mata fara'a an qaqaba masa ita,komawa tayi ta zauna, tare da aje hijabin da take ninkewa, ta dafe kan ta, bata san me zata ji ba ma, murna yau zata sarara, ko kuma tinanin mijin da za a bata, Ameena ce ta shigo, wadda a yanzu ta kai shekara takwas, iyayin ta da surutu sai abinda ya qaru.
"Yah Aeeshaa, ya naga baki qarasa hada kayan ba Umma ta gama komai, kin san in ta shigo bata ga kin....."
Ai Ameena bata gama magana ba ta tattare sauran kayan ba ninki ta tura a akwatin ta,ta saka hijabin ta, ta fara jan akwatin, dariya Ameena ta dinga mata,dan in taga yayar ta ta na tsoron Umman su abin dariya da mamaki yake bata, sai kace wasu mage da bera.
A bakin qofa sukai kacibus,
"Ai na zaci sai na shigo na dakko maki kayan naki ne,"
"A'a gani nan na gama ma,"
Tafiya suka fara, cikin ran Umman nat tana hago damuwar da diyar ta ta zata shiga in ta ji waye mijin nata.
A bakin gate ta aje ta, ta ce ta gaida mata mutan gidan ta wuce kai kaya, gidan qawayen ta, dan ta saro wasu sabbin kayan.
Mai gadi ne ya yi saurin amsar mata akwatin ta ya shiga da shi bangaren Hajja, da sallama da tsalle da murna ta shiga, ba kowa a parlour, dan haka ta qarasa bakin qofar dakin Hajja tana ta doka sallama.
"Wace tsohuwar ce haka, take mana sallama kamar bata san hanyar shiga ba?"
"Tsohuwa ce mai kama dake, kuma mai suna irin naki,"
Idanun Hajja har kwalla suka kawo dan ganin jikar ta ta, hali irin na Khadeeja sai ita, amma inshaa Allahu yanzu ai ta tako qafa ta shigo gidan taga wanda zai fidda ta ba da izinin ta ba.
Rungume junan su sukai, Aeeshaa kuka ta sa, tana shagwaba.
"Hajja kowa baya so na, unguwannin mu a kusa ba wai gari ne ba daya ba, amma ba ku taba tinanin ku ce Umma ta barni na zo ba, kullum daga makaranta sai gida,"
Shafa bayan ta Hajja tayi, cikin lallashi, sannan suka koma dakin, zaunar da ita tayi a bakin gado, suna fuskantar junan su,
"Aeeshaa, ba wai rashin so bane, dik a jikokina banda wadda nake qauna a zuciya ta kamar ki, amma dole na kauda kai akan ra'ayin mahaifiyar ki, tana da wauta ta nuna kunyar 'yar fari, ba irin abinda bamuyi mata ba dan ta daina wannan halin, amma abin ya gagara, bana son ya zamana tana maki tarbiyyar da take ganin ita ce ta dace dake, ni kuma na shiga na ce ba haka ba, ita ke da iko dake sama dani, beside tana boye ki ne saboda yanda zamani ya lalace, a cikin gida ma sai a lalata maka yaro ko yarinya balle kin samu qafar yawo, baki nan baki can, ko kuma ace kin tara qawaye kala2, wani lokacin ina matiqar jin haushin ta akan yanda take maki, amma wani lokacin sai naji dadin tsayawar da tai akan ku, kuma bamu son ki san waye mijin da zaki aura dan kar ki zama distracted, karatun ki nada mahimmanci."
"Na fahimta yanzu, amma Hajja zumunci ma nada mahimmanci, Ummana bata son jerawa dani, a qalla ko sau daya in zata zo muzo tare, amma sai tace in naga zan zo sai in ba da ita za a je ba, ni kuma tsoron fita nake ni daya, ta saba min kaini makaranta da dakkoni,"
"Kiyi hakuri tabbas bamu kyauta maki ba ta wani bangaren, haka Allah ya qaddaro, yanzu tashi muje mijina ya na hanya na dora masa abinci mai dadi,"
Dariya Aeeshaa tayi, tana rufe baki, ita kalmar mijina ya kusa dawowa ya bata mamaki, da kunya, Hajja ta tsufa fa, yaran ta ma ba wai na zamanin yanzu bane balle ita.
"Hajja ke kam baki tsufa, ai yanzu yanda kk tsufa masu aiki ne ya kamata suna yi maki hidima,"
"Waaaa niii Allah bai tauye ni ba daga halitta har lfy na zauna sai mai aiki sun ma mijina hidima? Ba dani ba gada a kushewa,in banda halin yaran zamani zama waje daya ba qiba zan ta tarawa ba kitse yamin yawa, na fara ciwon qafa da hawan jini? Yanzu da na ke ma mijina abinda ya dace baki ganni kamar ban kai shekaru na ba? Ki zauna ki koyi dikkan tattali da dawainiyar miji a wajena,"
Dariya Aeeshaa tayi, ita da kunya Hajja ke bata, aiki suka shiga yi na abinci, da abin sha, na gargajiya,masu qara lfy a jiki, Aeeshaa gwanace wajen girki, amma sai taga kamar bata iya komai ba da ta ga yanda Hajja ke girki.
Sunyi kwadon zogale da cabbage, wanda ya ji tumatur da albasa ga qulin da yasha kayan qamshi wajen daka, harda garlic a ciki, Sugar da maggi taga Hajja ta kwadanta da shi, sanda ta dandana, ji tai tana ganin stars, tsabar dadi, ruwan da suka dafa zogalen Hajja ta matse lemo, da lemon tsami, ta saka sugar, kadan da flavor,ta juya sosai ta saka a jug, sannan suka mishi brabuskon alkama, da miyar kubewa danya, yasha man shanu, ga tantakwashi, yawun Aeeshaa ya gama cinkewa, ga mamakin yanda Hajja ke komai a nitse, tana mata bayani, sannan tana nuna mata nutsuwa a girki ba sauri ba garaje yana taimakawa wajen samar da abinci mai dadi, sannan mace ta kula ba zabga maggi ko gishiri bane abinci, barin abinci ya dahu da kyau yana daga cikin abinda ke dadad abinci.
Bayan sun gama,Hajja ta fara diban abincin Aeeshaa na taya ta, suka aje a kan tabarma a inda dinning table yake, can nesa da table din, Aeeshaa na ganin ikon Allah yanda tsohuwa ke kula da miji kamar kamar basu tsufa ba, ko dan ita mahaifin ta ya rasu bata saba ganin yanda ake ma miji hidima bane?
Wanka Hajja ta umarce ta da ta shiga tayi, yau ita zata tari angon nasu, suna dariya da raha ta tafi dakin da Hajja ta nuna mata, zuciyar ta wasai, ji take kamar ta fito daga kurkuku, ga dai shi aiki tayi, amma cikin nishadi, ba kamar a gida ba tanayi ba godi bare na gode ga hantara, dik da aikin iyaye ne amma godiya da sanya albarka ma wani abune babba.
Wanka ta yi, ta saka kayan ta, ita din ba wani kwalliya ta iya ba, dan bata da wannan lokacin, ta fesa turarukan ta ta fito, dakin Hajja ta nufa,ta mata sallama ta nemi izinin shiga, Hajja ta amsa mata sannan ta shiga.
Baki ta sake dan mamaki, kwalliya ce mai ban sha'awa a jikin Hajja, atampa ce riga da zani, wanda aka ma rigar dinki mai kyau, ga sarqa kalar kayan, Hajja ta shafa kwalli da powder, ga mai ta shafa a bakin ta, sai tayi kyau kamar wadda akai wa hadadden kwalliya, kallon Aeeshaa Hajja tayi ta daure fuska.
"Me ne ne haka nake gani? Na daiji qamshi, amma ina kwalliyq? Ke budurwar qauye ce?"
"Hajja me zan yi kuma?"
Jan hannun ta Hajja tayi, ta fara shafa mata kwalli, sannan ta shafa mata powder, ta shafa mata janbaki kalar rigar ta, mai pink, sama2, nan da nan sai ga Aeeshaa ta fito tauraruwa, girar ta ta taje mata ta kwantar dan tana da cikar gira.
"Wayyooo Hajja nice kuwa? Wayyooo Ina Ameena tazo taga yanda nayi kyau,"
"Ya dai kamata na dage na koya maki kwalliya mai kyau,domn wannan mijin naki miskili kwalliya ce zata ja ra'ayin shi gare ki."
Gaban ta ne yayi mummunan faduwa, dan tina me ye abu na biyu daya kawo ta gidan, tana son ta tambayi hajja waye mijin tana jin nauyi, kar a ce tayi rashin kunya.
"To yanzu kafin General ya dawo kije ku gaisa da Iyayen naki, kina jin dawowar shi dai kije ki tare shi, zai mmakin ganin ki sosai,kuma zaiji dadi,"