← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 41

Sashe 38

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yarinya kin ci abinci, shi kk mayarwa da magana ko?"

"Soyayya ruwan zuma kar ku sata a gaba fa, ya isa haka,"

"Qaniyar ku, shin baku ganin mu ne a wajen?"

"Hajjar mu mukk na Allah,"

"Laaaa Hassana sai na falla maki tafi gaban mijin naki ni ba qaramin aikina bane kin sani, dan uwaki inna zama taku kuka zama na Allah ai na shigangadi,"

Dariya akai tayi cikin nishadi da so d qauna.

Ameerah ce ta farka daga baccin da take a jikin Maman Khaleefa, sabods hirar da ake ta yi, tana farkawa ta fara baza ido, akan Aeeshaa idon ta ya tsaya, can ta qara juyawa tana kalle2,tana hango Sabeer ra bangale bakin ta da yake dauke da haqora jefi2, ta sa dariya tare da furta,

"Baabaa,"

Shima dariya yayi ya je ya dauke ta, kowa kallon su yake cikin sha'awar hakan, ba kamar Aeeshaa, da har wata kwalla ce ta taru mata, tana jin dadin bond din dake tsakanin su, kusan kowa yaga farkawar ta, kuma sun kula da abinda tai.

Kitchen ya wuce da ita ya hada mata madara, yana bata, tana ta masa surutai yana amsawa kamar ya gane me tace, sai da ta qoshi ya dawo da ita, suka zauna a ka ci gaba da hira.

Hajja ce ta fita, ta je bangaren su Khaleefa, yana zaune yana bin karatun qur'anin da ya kunna,qira'ar Munshawee na babba da yaro, wanda ake yi kamar ana koyar da yaro, Hajja taji dadi sosai d sosai, tana shiga da sallama, ya daga kai ya kalle ta, rungume shi tayi ta dade a hakan tana jin son jikan nata na qara ratsa ta, shima haka, dik wani haushin ta daya ke dan ji dik babu ko dugo daya,(daya daga cikin amfanin runguma kenan) a hankali ta zare jikin ta daga gare shi ta zauna.

"Khaleefa Allah ya maka albarka, ya qara kare mana kai daga fadawa sharrin zamani,naji dadi fiye da yanda kk tsammani, akan daidaituwar ka da lamuran ka,Khaleefa ka zama jika mafi soyuwa a zuqatan mu bayan Aeeshaa, ina son baya ta zauna a baya, yanzu kai facing gaba, ka kyautata gaban rayuwar ka, na sani ko a da akwai laifin mu a wajen lalacewar ka, ina son a yanzu na ka nuna mana akwai hannun mu wajen gyaruwar ka,komai d muka umarce ka kana aikatawa daida iyawar ka,sai abu daya ka gaza akai,"

Daga ido yayi yana kallon ta tare da tina me ye suka ce yayi bai ba a yanzu dai kam, bai gan shi ba.

"Hajja me ne kuka sani wanda ban ba a yanzu?"

"Shiga cikin 'yan uwan ka, sake fuska a tare da su, yin nishadi a cikin su, sada zumunci d sallama a tsakanin ku, ka dai na qunta ta kan ka a waje daya, dik da ba zaman banza kk ba karatun qur'ani ka ke, amma shi zumunci shima yana da lada,dan Allah ka sakewa qannen ka, suji dadin babban yaya,daure masu da kk bai da amfani, kai a takure su a takure, plsss for Allah's sake,"

Shiru ya dan yi na wani lokaci daga baya ya numfasa yace

"Hajja a da son girma da kuma girman kai ke hana ni shiga cikin su, kuma yasa nake daure masu fuska, sannan ina daure wa ne kar wani ya shiga rayuwa ta mu shaqu ya san me nake aikatawa,amma a yanzu ina qin haduwa da su ne saboda kunyar abubuwan dana aikata a baya,"

"Habaaa Khaleefa ai kasan ku din gaba dayan ku gadon hankali ne, da nutsuwa, tare da karrama mutum, yau ko kafurci kayi ka dawo musulunci 'yan uwan ka zasu karbe ka hannu bibbiyu, dan haka kar kaji komai, yanzu ka tashi muje ayi hira da kai, an saka maku ranar aure daga nan zuwa sati biyu, ka sake ran ka,ka daina daure fuska, kaji, baka san da biri kk kama ba in ka daure fuska ko?"

Dariya yasa sosai, dan in ba son kai zai ba har matan gidan bayan Aeeshaa da Bilqis yafi kowa kyau,

"One zero Hajja, zan rama ne,"

"Sai dai ka rame, dannema mai goshi kamar an qunsa gorubar nera sha biyar,muje a fafata d kai,"

Fita sukai,sai sa shi dariya take har suka isa bai kula bama, yana ta babbaka dariya,itana tana taya shi, shiru wajen ya dauka, kowa ya nutsu ganin Khaleefa, dan baya wasa da kowa, Aeeshaa cikn sanda ta fada daki, Hassana ma tashi tai zata fece yace,

"In kin shiga ki kira ta ku dawo nan,"

"Nnaa'amm?"

"Eh cewa nai ki kira ta ku dawo nan,"

"To to bari na kira ta,"

Waje ya samu ya zauna, ya gaida iyayen shi mata dake wajen, sannan ya bama su Sabeer da Ammar hannu suka gaisa, Sabeer ya kalla yaga yanda Ameerah ta maqale shi, surutu kadan tace "Baba", yace "Na'am 'yar baba"

Murmushi yayi mai ciwo, YA MAKARO, ya rasa wannan damar ta zama uba a gare ta, amma ba zai cire rai ba wataqila a gaba ta so shi, koda kuwa taji me ya aikata.

"Gamu"

Sake gyara mayafin ta tayi, ya rufe har kan ta, dan nauyin shi take ji musamman da taga ya sauya halayen shi.

"Na zo nan ne saboda na nemi gafarar dik wanda na sabawa a cikin ku, musamman ke Aeeshaa da Ameerah, dik da tayi qanqanta ta san ina neman gafarar ta,amma na tabbata in kk yafe min itama zata yafe min ko a gaba ne, ina roqon ku gafarar dik abinda na maku physically and emotionally, ina son ku karbe ni a matsayin Yaya, wanda zai kula da ku da kare ku daga dikkan cutarwar da zai iya, ku dauken a matsayin aboki wanda zaku yi hira kuyi raha da shi, inshaa Allahu dik wani halina na baya mara kyau ba zaku sake ganin ko jin na aikata shi ba, ina fatan zan kar bu a wajen ku, a yi hirar dani nima,"

Dariya da sowa wajen ya dauka,Aeeshaa dik wani abu da ya mata ji tayi kamar bai taba yi mata komai ba a rayuwar su da sukai a baya, ji tayi koma me ya mata ta yafe masa har abada, kamar an zare mata qaya a jikin ta haka take ji.

"Na yafe maka Yah Khaleefa, Allah ya yafe mana baki daya, nima kanyafe min bisa abubuwan dana maka, musamman da cikin Ameerah,"

Dariya sukai dika tinawa da yanda take maida masa magana, dan da cikin ta fara masa hakan.

Su kadai suka san me suke wa dariyar, dan haka Hajja tayi gyaran murya,

"Alhamdu lilLAAH a gaskiya kun sani farin ciki mabayyani, yau inna koma ga mahaliccina na san na kyautata rayuwar iyalina, na basu tarbiyya cikakkiya, kuma na kula da buqatun su, dan haka ina son sanar da ku wani abu,ku yi hakuri da junan ku,ku so junan ku, saboda in baku so juna ku ba maqiyan ku zasuyu nasara akan ku, in kana tare da abokin zaman ka,kaga ya sauya, lamarin ka yana neman lalacewa, to ka so rayuwar da kk ciki, kar ka hango ta wani,

Saboda daga lokacin da dan adam zai daina son kan shi, ya fara hangen wasu yana sha'awar rayuwar su, to daga wannan lokacin rayuwar da yake ciki zata koma masa kamar wata dadaddiyar rayuwa koda kuwa bai dade a cikin ta ba. Lokacin da ya dawo baya ya fara son kan kanshi, ya bar hangen rayuwar wasu, ya fara sha'awar tashi, a lokacin rayuwar da yake ciki zata koma masa sabuwa filll, koda kuwa ya dade a cikin wannan rayuwa.

A kullum muna tina wannan sai rayuwar mu ta yi ta sabunta, Allah ya muku albarka, bari naje na huta da dan tsohon mijina nima,"

"Mun gode Allah daya bamu ke a matsayin tsayayyar uwa uma kaka, a wajen Yaran mu,kin zama mana babban jigo, Allah ya baki babban sakamako mai kyau duniya da lahira, ba abinda zamu ce sai dai mu maki addu'ar fatan yin kyakkyawan qarshe, mun gode Hajja mun gode sosai,"

"Ummeen Sabeer yi wa kai ne,in na so kai na na zama tsohuwar banza zuri'ata na lalata, inna so kaina na zama tsohuwar kirki zuri'ata na gyara,Allah y muku albarka,"

"Ameen tsohuwa mai rannqarfe,"

Dariya kowa yayi, ta tafi, suka ci gaba da hirar su kamar me, yanda khaleefa ya zaqe yana basu labarai kamar ba shi ba, har mamaki suke dama yana tare sa wannan labaran fal cikin shi yake kakkamewa yana wani daure face.

***********************

Kwanaki hudu suka rage saura ayi bikin su Hassana,Hussaina,Hamdiyya,Bilqis, duk sun xo, da yaran su, masu gidajen su sunyi alqawarin zuwa banda mijin Hamdiyya da baya qasar yayi tafiya,dan kasuwanci, tin kan su zo Hajja ta dakko mutan maiduguri da na Sokoto(Deejee yau na fadi abun alkhairin Sakkwatawa🤣🤣🤣akwai ku da kayan mata ance) sai gyara amare ake, Ammar ya koma gida tini suna can suna nasu shirye2n, mutan Yola akwai kashe dukiya wajen aure, dan haka gidan ma da za a kai Hassana abin kallo ne ga kowa dik kudin ka kuwa, ba wai dan girman gidan ba, a'a sai dan kyau da tsaruwar shi.

Har da su Bilqis aka hade akai ta gyarawa, Aeeshaa wataran gudu take saboda yanda ake dirka mata kayayyaki, wai saboda ita bazawara ce, ana son a gyara ta sosai, yanda Sabeer ba zai banbance bazawara da budurwa ba,(na lie him go ganewa aradu, dan dai samrayi ne bai san banbancin su ba, kodake samarin fa yanzu sun san komai😨🙊).

An fitar da anko kala biyu, na dinner, da ranar yini, masu kyau sosai, amare kuwa an masu sabbin dinki har ba zan iya lissafa maku ba.

Su Sabeer unguwar su daya da Umman ta, sai dai akwai nisa sosai sai ka dan hau abun hawa ko ka isa kana nishi, Baba Abubakar ne ya mallaka masa gidan, gida ne daya yake dauke da sama da qasa, mai kyau, kowanne bangare an cika shi da kaya na alfarma, komai na gidan purple da ratsin pink, hatta fentin gidan haka yake, ta waje an masa purple mai haske, gwanin sha'awa tsarin gidan.

Hadizan Goggo ma ana can ana shirye2, Hajja tayi2 Goggo ta bada ita a mata gyara amma tace kar ta damu zaqewar zatai yawa.
Chapter 38 · 0% Book details