← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 41

Sashe 28

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hawaye ne me ta zuba aa idon Aeeshaa, wa take gani, yau ko ba soyayya a tsakanin su bai kamata ba abinda Khaleefa ya mata, ko ba komai mijin ta ne, sun jiyar da juna dadin auratayya, har sun samu qaruwa, akwai 'yan uwantaka a tsakanin su,

"Me ne ne? Me kk wa kuka? Mijin ki ko? Taso muje parlour, na kira kowa kafin na shigo, mu jira zuwan su,"

"Bar abincin nan kiga muje muji me Hajja ke wa kira na gaggawa haka da safen nan,"

"To Babansu amma da ka dan sha tea din nima sai na sha kasan muna da ulcer bamu san za a dade ko ba za a dade ba; zauna mu shanye kawai sai mu tafi,"

"Muyi sauri,"

A gaggauce suka shanye tea wanda ya sha kayan hadi yayi kauri, suka fito a tare, a ganya suka hadu da Hassana da Baban Sabeer da Ummeen shi, gaisawa sukai sannan suka rankaya.

Hajja da Baba General na zaune dik inda ran su ya ke ya kai qololuwar kuma qarshen baci, gaban su Baba ne ya dinga faduwa, yau me ye wannan ya faru mai tsanani, dika2 qarfe 9 ne yanzun amma tashin hankali irin wannan ya faru da zai dauke walwalar gidan gaba daya.

Umman Aeeshaa ake jira, dan zaman har da ita ya qunsa.

Sun gaida iyayen nasu inda suka amsa cikin daurewar fuska, sunq zaune suka ji tsaiwar mota, a zaton su Khadeeja ce ta iso, sai suka ji shigowar mutum kao tsaye yana sallama a tsakar gida.

Baban Sabeer ne ya leqa, dan shi ne qarami a mazan, wani matashi ya gani baqi kyakkyawa, amma rudani da tashin hankali bayyane a fuskar shi, ko gaisawa da Baban Sabeer bai ba ya hau fadin abinda ya kawo shi.

"Suna na Ammar Abdallah, ni abokin Sabeer ne na wajen aiki, yanzu haka mun kai Sabeer AKTH saboda bashi da lfy matuqa, ciwon yaje ya dawo, yau abun yayi yawa, yace a kawo shi gida, sai muka ga ya kamata mu kaishi asibiti ne in yaso sai nazo na sanar,"

Wata iriyar zufa ce ke karyo wa Baban Sabeer,

Baban Khaleefa ne ya fito

"Abubakar lfy? Meke faruwa,"

"Yaya Sabeer dina na asibiti ba lfy tin daga can Ibadan aka kawo shi nan AKTH"

"Subhanallahi, Hajja, Baba, ya kamata mu wuce asibiti Sabeer ba lfy,"

A kidime yake shiga ciki yake sanar dasu, inda suma suka tashi hankalin su a tashe suka nifi motocin su, sai AKTH.

Qarfe 10 daidai suka isa, Ammar ne ya musu jagora zuwa inda aka kwantar da shi, Aeeshaa kukan ta ne ya qaru, Yayan ta ba lfy, Ohh Allah yau wace iriyar rana suka tashi da ita ne?

'Allah ka sauqaqa mana abinda ya tinkaro mu na musiba, ya Allah mun miqa komai a hannun ka ka mana maganin dikkan abinda yake damun mu babba da qarami'

Ummeen Sabeer itama kuka take, Sabeer ne kwance sambal baya motsi sam, numfashin shi na fita kadan2 da gani da kyar yake samun shan su.

"Ina likitan daya ke kula da shi? Me aka ce yana damun shi?"

"Baba sai dai kuje kuji, muna kawo shi ogan mu ya koma ni na tsaya, so ban san meke damun shi ba"

"Muje ka nuna mana office,"

Suna shiga Dr. Ya dago daga duba wasu takardu, da alama gwaje2n da akai ma wani ne,tashi yayi tsaye ya miqa ma su Baba General hannu, da su Baban Sabeer da Khaleefa, bayan sun gaisa ya musu izinin zama a kujera, sun zauna cikin qaguwar suji meke damun dan nasu.

"Da farko ni ne Kakan Sabeer Abubakar da aka kawo maku daxu, wannan mahaifin shi wannan kuma yayan mahaifin shi, munzo dan mu san meke damun dan mu,"

"K masha Allah, dama yanzu nake son naje na sa a taho da magabatan shi, ni suna na Dr. Naseer Umar, yaron ku a bisa gwaje2n da mukai mun gano yana dauke da matsanancin ciwon malayria, thypoid, da kuma hawan jini, jinin shi ya hau sosai, wanda muke tinanin ko tsananin ciwo ne ko kuma wani damuawa yake dauke da shi, yanzu mun masa allurai, na malayria da thypoid, mun saka mashi magunguna ciki, inshaa Allah muna saka ran samun nasara na da wasu 'yan kwanaki, na hawan jini ma mun samu muna kan bashi kulawa akai, inshaa Allah za a samu nasara nan kusa,"

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun,wai me ya kawo ma sabeer hawan jini ni Muhammad? Me zai dami yaro matashi haka?"

"Kar ku damu, ganin damuwar ku sai ya qara jefa shi wani hali, ku kula da shi sosai, muma zamuyi iya qqarin mu, inshaa Allah,"

"Dr. Mun gode sosai Allah ya saka d khair"

Sallama sukai suka fita,Umma ce zaune tana ta sharbar kuka itama, mutuwar mijin ta ce ta dawo mata sabuwa, haka aka fada mata mutuwar miji katsahan, Allah ya kare mata Sabeee din ta, shi yasa bata son saka kowa a rai, kar abinda tafi so ya tafi ya bar ta, harda Umman Sabeer din aka hadu ana taba hakuri, su Baba General na fitowa suka miqe zuwa wajen su, tare da watsa masu tambayoyi, Baba Khaleefa ne ya masu bayanin komai, kuka suka rikice suna yi, Hajja ce mace mai kamar maza ta bankada masu tsawa,

"Bana son iskanci, me kukan ku zai masa? Sauqi zai bashi? Yanda kuke jin quncin ciwon nashi ya fi ku jin azaba, dan shi a jikin shi yake, kuda ya kamata ku masa addu'ar samun sauqi zaki cika masa kunne da kuka, ya tashi yaga kuna kuka ku sake rikita shi ya zaci ciwon ajali yake ko? Dalla ku rufe mana baki ku bar mu muji da abinda ke damun mu, kai kira min wannan dan iskan yaron naka,"

"Khaleefa na can yana shiryawa yau za su shaqatawa Abuja da Becca,ga shi ya yiwa Hadiza alqawarin zai je Abuja aiki zai kai shi zai kai mata tsaraba in ya dawo, tana nan tana murna da masa fatan dawowa qalaou.

Wayar shi yaga tana walqiya, zuwa yayi ya daga a zaton shi Becca ce ko dubawa bai ba ya dauka.

"Babe gani nan zuwa ki shirya, yau sai Abuja ta san da zuwan mu, zamu raqashe, babban club zaki kai mu wanda ya amsa sunan shi, bana son qaramar harka,"

Jiri ne ya fara diban Baban Khaleefa,

"Khaleefa CLUB????"

Da gudu Khaleefa ya datse kiran, yana zaro ido waje, qirjin shi ne ya fara bugawa da qarfin tsiya, ji yake kamar ranshi zai fito dan tashin hankali da damuwa, qafafun shi da hannayen shi har zufa suke.

"Wayyoo Allah na ina cikin tashin hankali,"

Hadiza na gida, tana jiran taji motar shi ta masa Allah kiyaye daga qofar gidan su.

Shiru har 11 ta gota bai fita ba, Wuf tayi zata fita Goggo na ta kwala mata kira ko waigawa, a gidan Khaleefa ta tsaya tana maida numfashi.

Tana shiga ta gan shi a parlour yana kaiwa da kawowa, ha kalin shi a mugun tashe, ya kai ya kawo, ya kai ya kawo yana sosa kai,

'To ai zama na ma a gida hadari ne, yana iya shigowa indai Baba ne ya ci mutunci na, gwanda naje gidan a gama komai a can, in anan ne maqota da mutan unguwa suka ji ai mutunci na ya zube'

Shafo shi tayi daga sama zuwa qasa ta baya,da sauri ya juya,

"Hadiza me kk anan? Bance maki tafiya zan ba?"

"Haba angon Deejee? Naga shiru baka fita ba shi yasa,"

"Ango kuma, baki da hankali, baki san tashin hankalin danake ciki ba ne shi yasa, fita kar wani yazo ya gan ki anan,"

"Daidai kenan, kaga sai kawai a jira na haihu a daura mana aure, dan ba a aure da cikin shege,"

"Whatttt????? Ciki? Nawa? Inaaa in kin isa shege ne ni, bar nan fitaaa!!!

"In fita inje ina? Ai Baba Khaleefa ko Daddy zan ce tinda ku 'yan gayu ne, ba inda zani, sai ka san ya za kai da ni, ka auren a haka ba wanda ya san ina da cikin ka na wata biyu, ko kuma ka kyale ni na tona mana asiri, kasan dai kai ne zai zama maka sabo, ni ko a jikina, kaji na fada maka,"

"Wayyoo Allah na, yau meke faruwa ne?............

*Shiga Google ka gani dan latsin hammata kawai*

*ku yi manaji da wannan dan ban son aje ku kuna jira ne amma wallahi yau na dan gaji da typing, thank u for the love and du'as, Allah ya amsa ya saka maku kuma da alkhairi*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

Page 21:

"Tsakanin ki da Allah yanzu ba zaki bar gidannan ba? Kin san irin tashin hankalin da na ke ciki yanzu? Ji nake yanzu haka kmar na bace a dain gnina haka nake ji,"

"Hhhhhhh kasan me? Kana ban mamaki da kunya, kai fa namiji ne, ni mace ina murje ido na nayi abinda nake so, amma kai sai ka na wai tsoron gidan ku, zawarawa yanzu iri na daidai ne masu kame kan su a gidajen su, amma dik fita mike farauta, ba tare da an gane ba, yanzu ni in ba Goggo na ba mutan unguwar nan da ke yawan gani ina fita ina dawo d dare ba a hanya muka hadu da kai zaka rantse ina ma da aure, ai ba dole sai ka yi abu kowa ya sani ba,(ta manta cewa Allah na ko ina, mala'iku na tare da ita, akwai mai rubuta komai take) look, u have to grow up, ka manta da wani zancen me mutan gidan ku zasu ce ka shana kafin lokaci ya qure maka, shawara na baka,"

Qwan !Qwan ! Qawan !

Cikin Khaleefa ne ya bada wata iriyar qara, kashin shi ya bushe yau,bai taba ganin fushin mahaifin shi ba,ba kuma ya fata, ya kama ta ya nemi mafita, ba katangar d xai iya kamawa ya haure a gidannan da ya haure, qara knoking akai d qarfi.

"Kaje kaga ko waye ko na leqa, bana son qara, tinda na samu cikin nan,"

"Fuck u Hadiza,don't u ever talk about that darn pregnancy, or else,"
Chapter 28 · 0% Book details