← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 41

Sashe 16

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bude qaramin qofa tai, cike da murna ta koma ta fara bude babban, tana matse kwallar farin ciki.

Shigowa tai dauke da mamakin ganin Aeeshaa ke bude gate, ina gate man?

"Aunty Aeeshaa nayi missing din ki alot, ina ta son zuwa Umma sai tace ba yanzu ba, kuma...."

"To cakwaikwaiwa, zaki iya bari mu shiga ciki?"

Turo baki tai gaba, ta fada a hankali,

"Ta fara"

Murmushi Aeeshaa tayi, ita kam she missed this fada thing, how she wished everything will go back to normal.

Ruwa da lemo ta gabatar da abubuwan motsa baki, sannan ta zauna a qasa gefen umman ta gaida ta, tare da tambayar ta suna lfy?

"Ke za a tambaya kina lfy? Kinga yanda kk koma kuwa? Sai kace ana yankar ki ana miya? Meke damun ki, ina me gadi kk bude qofa d kan ki?"

"Ammm Umma ya aike shi ne, kumaaa immm...niii ba abinda ke damuna, Umma i missed u so much,"

Wani irin zazzafan hawaye ne ya ke kwaranya a idon ta, Abdul tabe baki yayi, a ranshi yana fadin

'Kukan gulma, ji gida kamar a waje, ga kayan alatu, dik ita daya, ga vedio game, wai take kuka, kamar a can wani dadin take ji'

Umma ta tausaya matuqa amma a zuci, dan ji tai kamar ta dora hannu akai tai ta zunduma ihu,

"Meye abn kukan? Ke Ameena ce? Kowa haka aka masa auren ya zauna, da bamuyi zaman auren ba xamu same ku ne? Kema haka zaki hakuri....."

Cikin fadan da hantarar ta bata shawarwarin da zasu mata amfani in kadaici ya dame ta.

Godiya tayi, ta miqe zata dora masu abincin dare, a zaton ta sai dare zasu wuce.

"Dawo mu wucewa zamuyi, yanzu na san wannan mara kunyan mijin naki na tafe, gwanda mu tafi kan ya gan ni ya raina ni, kar kuma naji labari a ko ina cewar na zo nan, in ba haka ba bazaki sake gani na ba,"

"Na gode Umma inshaa Allah ba zan fada wa kowa ba..... haba Abdul tinda kuka zo ko ci kan ki baka ce min ba, me yayi zafi?"

"To ci kan ki"

Wasa ta maida abun sukai dariya da Ameena ya yi murmushin gefen baki shima, nan ta hada ma qannen ta abubuwan dadi da na shafawa for Ameena, amma Umma ta hana karba, ran Abdul ya mugun baci, musamman daya ga chocolates din dayake so.

A cikin fushi ya bude mota ya zauna, Aeeshaa ma cikin hawaye ta bude masu gate suka fita.

Fitar su da minti sha biyar ta fara dora girkin dare bata san me yake so ba, kawai ta fara dora doya zata masa sakwara.

Doya na tafasowa Aeeshaa ta fara jin kamar zatayi amai, abu sai gaba yake, da gudu ta nufi wajen sink ta fara kwara amai, kamar wadda zata amayar da hanjin ta🤮🤮🤮🤮🤮........

*Tooooohhhh Aeeshaaa watahafen?*

*Happy 10years Anniversary to us💃🏻💃🏻*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

*Iyaye na,mijina 'yan uwana, qawayena, addu'a ta a gare ku itace Allah ya muku albarka, ya saka maku da alkhairi, ya sa kuyi kyakkyawan qarshe, na gode sosai da soyayyar da kuka nuna min yau, Allah kuma ya amsa addu'o'in ku, albarka itace addu'a madaukakiya da zaka yiwa masoyin ku, ina nema maku ita wajen Allah, na gode sosai❤*

Page 12:

Bayan ta gama ta wanke bakin ta, ta sauke doyar cikin toshe hanci, ta tace ta ta saka a fridge, sannan ta koma dakin ta ta kwanta, tare da qudindinewa a bargo, saboda sanyin da take ji.

Kamar kullum yauma ya makara dawowa gida, sai dai yau gida ya je ya kai ma iyayen shi ziyara da su Hajja, dan gulma har da cewa bari yayi sauri ya tafi yasan tana can tana jiran shi.

Hajja tai ta sa mashi albarka, tana yabawa halayen shi,

"Matsalar ka daya Khaleefa baqin hali, baka son hayaniya har yanzu, ince dai ba dinkim kk mata ba, ba ko 'yar hirar nan ta miji da mata?"

Ran shi ya fara baci, sun ma samu ya ziyar ce su sai sun kai shi maqura, cikin danne bacin ran shi yace.

"Really? Ina da mata kamar Aeeshaa me zai sani bata rai?"

Hajja harda shewa ta fara tina masa lokacin auren su, tana yi tana dariya, Baba General na taya ta, nasiha Baba General ya mishi, kamar na Allah, ya nutsu yana saurare,amma ta shiga ta dama ta fita ta hagu, mahaifin shi ma sai da ya mishi nasiha, suka raka shi har bakin mota, da roqon ya kawo masu Aeeshaa, kar ya zama miji mai kulle, alqawari ya musu zai kawo ta ranar juma'a mai zuwa.

Qarfe 10pm a gida ta mishi, Aeeshaa bacci ne mai dankaren dadi ya dauke ta a kujera ,dan abinda take yi kenan, yanzu, goma nayi zata zauna a kujerar dake daf da fita daga parlourn.

Horn ya dinga zabgawa baiwar Allah bata ji ba, takaici ba irin wanda bai ba ji yake kamar ya yi tsintsuwa ya gan ta gaban shi, ga yunwa yana ji, anyi2 yaci abinci yaqi, wai kar ya dawo tayi abinci bai ci ba, kuma a gaskiya tinda ya fara cin abincin ta ko a wajen aiki in an je cin abinci ci yake kawai, amma ba dan da dadi ba.

Kamar a mafarki taji bugun qofar tashi, cikin rawar jiki ta tafi ta bude gate, ya ko haske ta da fitila yaqi shiga, jikin tane ya hau rawa, dan ta san halin shi in ya dade bai abu ba to kallon ta yake da kallo kamar zai kashe ta.

Baya ta ja cikin tsoro, shigo da mota yayi, ya parker ya fito cikin fushi, ita kuma ta tsaya rufe qofar tare da yin addu'a, a zaune ta same shi, ya dora qafa daya kan daya, yana hura hanci.

"Wani sabon salon iskanci kk fito dashi? Ina ta horn amma baki ga damar budeni ba, ni da gidana?"

Durqusawa tayi kamar kullum, ta fara bashi hakuri, banza yayi da ita dan bai niyyar hakuri ba sai ya fanshe a wani abun,

"Kawon abinci,"

Nan da nan tinanin ta ya dawo mata ashe fa bata masa komai ba, amma a wautar ta bata ji damuwa ba, tinda kullum baya yabawa zagin ta yake yana cewa ci yake dan kar yayi asarar kayan abincin.

"Yah Khaleefa ban yi ba yau, na fara naji banda lfy sai na kwanta shine bacci ya dauken bayan nayi sallah, kayi hakuri, u dn't like the food anyway, amma in kana so sai na maka ko indomie ce,"

Wani irin qunci da danasani ne ya shige shi na qin cin abincin Hajja dayayi, a harzuqe ya miqe ya kifa mata mari, sai da ta ga duhu dummmm na wani lokaci, sannan ta dawo hayyacin ta, kuka ta sake mara sauti mai qarfi a zuciya, meye laifin ta? Taga bai ma son girkin ta, shine dan zalunci zai dake ta.

Janta yayi har kitchen, ya dangwarar da ita gaban electric da suke amfani da shi wajen girki,

"Oya hadamin tea mai kauri, ki hadon da snaks, sannan ki dawo ki dafan abu mai nauyi,"

Kuka kawai take dan ta san ba zata iya moruwa ba yau, bata da lfy sosai, ga jikin ta ya dau zafi, yq iya damqar ta ya daka amma bai iya jin zafin jikin ta ba, Allah na nan.

Tea ta dora, ta jingina da kitchen carbinet tana kuka.

Shigowa yayi daukan juice, ya ganta tsaye, dauke kai yayi, ita kuma ta hau goge fuskar ta.

Yana budewa yaga doya a wata roba kalar pink, qamshin doyar na fitowa ta toshe hancin ta, saboda wani yunqurin amai daya taso mata.

"Me wannan take yi anan?"

"Da sakwara zan maka, sai naji banda lfy, shine na ajiye, inna shaqi qamshin doyar amai nake, yanzu ma ji nake kamar zan amai,"

"Amai kuma? Yanzu ina qamshin nata yake har da ke da kk nesa zaki ji ni ban ji ba,"

"Kayi hakuri amma da gaske ina ji ni,"

."zo nan,"

Hawaye ne ya taru mata again, ta taka a hankali ta isa gavan shi, hannun ta toshe a bakin ta da hancin ta.

"Dakko,"

Kallon shi tai, with pleading eyes, amma ya basar, dakkowa tai hannun ta na rawa, ai kuwa kafin ta kai ga ajewa a kan sink amai ya taso mata gadan2, gudu take son tayi dan tai aman, ya tsaya a hanya, sai nuni take masa alamar ya matsa zata wuce yana ta kallon ikon Allah, yarinyar nan kamar wata mai allergy akan doya?

Yana nan tsaye qiqam, wani amai mai mugun yawa da tsaho ya taho ya wanke masa jiki daga fuskar shi har daidai jikin wandon shi.

Aeeshaa saboda amai kasa tsaiwa tai, tana ta yin shi,ga tsoro a ran ta da damuwar aman da ta masa.

Ta rasa ya zatai ta tsira akan wannan lamarin, kawai sai ta fadi a wajen, ta kwanta kamar ta suma, this is her only way to save her skin.

For the 1st time tayi qarya, Khaleefa na nan qame kamar wanda aka dasa, mamaki da takaici da qyanqyami sun hade sun masa katutu.

Bai bi ta kan ta ba sai da yaje dakin shi ya sauya kaya ya wanke jikin shi musamman bakin shi, sannan ya dawo, kuka take tayi ta gefen ido, yanzu da suman gaske ne sai ya gama.uzurin shi zai dawo, in ta mace ma baida matsala, to in da mutuwa tai qiyayyar har ta kai ko duba ta ba zai ba ya wuce? Dan uwan tane fa.

Ruwa mai sanyin gaske ya watsa mata, a gigice ta miqe tsaye, tana zaro ido tare da dauke numfashi.

Wuce ta yayi ya kashe electric ya tsiyayi ruwan tea ya debi abinda zai ci ya wuce ta, ba sannu ba Allah sawaqe, ba meke damun ki ko ina ke maki ciwo? Ko gobe zan kai ki asibiti je ki kwanta, nothing nothing, the mst important thing shine ba duka ba zagi.

Tana ganin haka dadi da murmushi suka kwace mata,lallai yau Allah ya so ta, da tai dabarar nan, da ba dan haka ba bata san wanne irin kisa Khaleefa zai mata ba yau.
Chapter 16 · 0% Book details