Sashe 32
Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ido ya ma Hadiza yawa, dik sanyin AC dake wajen bai hana ta zufa ba, musamman in ta kalli idon General da Hajja, idon Hajja yafi firgita ta, tin randa suka fara haduwa idon Hajja ke mata gizo, yau ma cikin rudani ta fara magana,
"Ddddamaama ci ci...ciiikiiii neee dddadddaaniii, shineee immm shinee immm....."
"Ya isa dalla, munji, yanzu wanne hukunci ne kuke ganin ya dace da wannan dan iskan,dan nayi alqawari sai na dandana maka azaba da wulaqancin da ka dinga yi wa wannan yarinyar, dik da taurin kan ta ya qi ya bar ta ta fada min irn zaman da kukai, amma na gano wasu abubuwa daga kalaman wannan maciyar amanar, ta saqon messages din ku, da kuma randa naje gidan naku,"
"Hajiya ke ce kikai zurfin tinanin gyara iyalin nan namu, da yin binciken da bamuyi ba da fari saboda son zuciya da kuma ganin dik gida ne ba lallai ne a yi bincike ba, dan haka mun bar maki wuqa da nama ki yi hukunci akan wannan lamarin, ni mijin mi na amince maki da ki yanke hukunci dari bisa dari,,"
"Na gode, Muhammadu kana da haqqi akan dan ka, me kk gani ya dace? Ko ke mahaifiyar shi kuyi magana,"
"Hajja ko wanne hukunci kk yanke daidai ne,"
Juyawa tayi taga yanda Khaleefa ke wan cika yana batsewa, wai shi tantiri,
"Dama na fada maka ni na haifi uban ka, dik wani tantirancin ka na dame ka na shanye, akwai ranar da asirin ka zai tonu, yau ce ranar, dan haka ni na fara qauna da sha'awar a hada auren ku ko? Yanzu na qara tinani akai nace ka sauqaqe mata auren, dan uban ka,in ka min taurin kai na ci uwar ka, kar ka ganni haka inna da ke ka sai an maka ruwan zafi a wajen, maza ga takarda da biro nan rubuta mata saki, ko kana so ko baka so,"
Da mamakin kowa a wajen budar bakin Khaleefa da ya kumbura yayi sintim shine,
"Balle ma bana so, auren da aka qaqabamin, bana so, ban taba son ta ba, kuma bana jin nan gaba zan so ta, taje na sake ta saki uku, "
Wani irin abu ne mai zafi ya soki Sabeer a zuciya, Aesshaa ake wulaqantawa haka, mace mai daraja a wajen shi, amma Khaleefa yayi asara, yayi asara mabayyaniya.
Ya ja takarda ya rubuta, ai Hajja bata san ta isa gaban Khaleefa ba, sai saukar maruka ya dinga ji, ko damar dafewa bai samu ba, sai da ya kifa,
Nishi take tana haki,tare da magana,
"Ba baki nake maka ba, amma Khaleefa zaka ga rayuwa, zaka ga rayuwa ta yanda ba ka taba tsammanin ta ba, zaka dora hannu ko a gaban mu ko a bayan idon mu ka yi kukan abinda ka aikata, Allah shine shaida mun fita haqqin ka,.....ke kuma, ki je gida, zamu kula da komai naki har ki haihu, bayan haihuwa zan sa a aura maki shi, ko kina so ko baki so, ni na yanke hukunci baki da miji sai shi, sai dai in Allah ne bai nufa ba.....tashi ki bar nan.
"Auwal, John!!! Come and lock him for me, don't set him free untill i said so,go with him,"
Tinawa da karon su ne yasa Khaleefa fashewa da kuka, ji yayi wani tsoro da kadaici ya kama shi, ai bai gama tinani ba yaji anyi sama da shi, ko qasa vaya tabawa, haka suka tasa qeyar shi a gaba, suka wuce da shi.
"Yanzu magariba ake kira, ke Khadeejaa ki je ki debo yaran nan ku rufe gidan, sabon mai gadin dana kai maku shi zai ci gaba da zama har n gama sa ke anan,.....kin rifen baki kin daina kukan nan ko sai na kokkora maki mari? Mara zuciya kawai, namamajon kikewa kuka? Dan ya rabu dake dubun shi na son ki"
Diff kk ji, dik da ba hakan ne ya sa ta kuka kadai ba, tausayin kan ta take, da qananan shekaru ta zama bazawara.
"Hajja Allah ya miki albarka, ya sanya ki a aljannatul firdausi, ba dan ke ba da ina nan ina daga kai a abokai daga 'ya'yana har jikokina ba dan banza,ba dan ke ba da rayuwar iyalina na cikin wuta ban gani ba, bayan Allah yace mu kiyaye kan mu da iyalan mu daga wuta, Hajja kin dauki role din miji yau na sama hotiho,"
Baba General ke zubda hawaye a karo na ba adadi, a yau, da kyar kowa ke bashi hakuri, sallah suka tashi suka tafi, Maman khaleefa da kyar ta tashi, sai da Ummen sabeer ta taimaka mata, a sannan ta samu kuka ya kwace mata, dan ta ne ya sama hamshaqn mazinaci haka, tana nan ba abinda ta sa a gaba sai kudi, da son gayu, bata san halin da yake ciki ba, bata damu da ina yaje, me yasa yayi dare ba, iyayen yanzu gani suke mace kawai ake ba tarbiyya, namiji daya balaga an gama da shi, bayan maza na ingiza mata yin zina, dik da matan ma ba a bar su a baya ba.
Sallah suka tafi kowa da abinda ke zuciyar shi.
Sabeer bai san a wanne hali yake ba, tsakanin baqin ciki da tausayin 'yan uwan nashi, ji yake kamar yaje ya lallashi Aeeshaa, Ameerah sai kuka take.
********************
Wani qaramin gida ne kamar ma hayar shi akai, masai na qasa, komai na qasa amma an masa plasta, da siminti, katifu uku ne a gidan daki biyu,daya na Khaleefa, daya na su, sai bandaki, daya,da kitchen, bandakin a rufe yake ruf, amma ba qofa, dakunan da gani sabbin qofofi aka sanya masu, na qarfe ne masu kwari sosai.
Ledar dakin mai kyau, amma ba zanin gado a katifar.
Wurga shi sukai, suka rufe, yana ta ihu, yana su bude shi, kar ya fusata, wanda aka kira John ne da gurbatacciyar hausar shi yace,
"Me sa ka yi in ba ah bude ka ba?"
Yana muzurai, lafewa Khaleefa yayi, ya yi shiru, idanun shi fal hawaye..............
*🤣🤣🤣🤣🤣Allah de ya biya Khaleefan Mero Tsokana🤣🤣🤣*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼
*BY HAERMEEBRAERH*
Page 24:
"Daga ina kk? Ashe dik maganar da mukai dake ba zaki dauki ko daga daga ciki ba ko? Ke rayuwar ki yanda kk so haka zaki yi ba wanda ya isa ya hana ki ko ya saka ko ko? N roqi Allah daya shiryar min dake, (kuna ganin rashin ji irin na Hadiza amma hakan bai sa mahaifiyar ta zazzage ta va, ko ta aibata ta, ko ta tsine mata, a'a sai fa mata fatan shiriya)"
"Goggo ba wani wajen naje ba, gidan su Khaleefa naje, kiyi hakuri ki zauna kiji me ya faru, da na je din,"
Zama Goggo tayi, Hadiza ta labarta mata komai,Goggo ta yabawa qoqarin iyayen Khaleefa na hadin kan gyara masa rayuwa,ba su damu da girman shi ba, da shi din magidanci ne, ba su kalli shekarun shi ba, suka hada qardi d qarfe suka hukunta shi haka, lallai da za a na samun iyaye irin na Khaleefa da wasu abubuwan sun ragu.
"To ba wannan ba kinyi salla?"
Sosa hanci ta fara, in bata manta ba ko ta la'asar batai ba ga magrib ta riske ta, ana neman yin isha'i ne ma yanzun.
"Hadiza ina maki nasiha kiji tsoron Allah, ki kiyaye dokokin Allah,Allah sai ya kiyaye ki,Allah ya baki rai, ya baki lfy, ya baki arziqi na wajen zama da ruwa kina iya diban ruwa kiyi wanka ki fice yawon tazubar amma alwala da ba zaki wahala bama tana maki wahala, kina iya kwantawa kiyi awa biyar kina chatting amma ki ware minti shabiyar kiyi sallah yana maki wahala,kina iya yin rawa wai san motsa jiki ki ta zufa,amma sallah na maki wahala, lallai Hadiza imani kk rasa, da kinyi imani da Allah kin kuma san yana kallon ki a dikkan abinda kk, numfashin ki daya bya fita face da sanin Allah, qifatawar idon ki daya baya kasantuwa face Allah ya gani, Hadiza da kina da imani da kin san hakan, da kin gyara rayuwar ki kin maida sallah abin so,kuma da kna yin ta da nishadi da shauqi, inace nan kk satar jiki ki tafi wajen dik wani qato da kk so? Ashe Allah ne bai so? Tinda ga dama har gida, har dakin ki sa zaki gana da ubangijin ki abin son kowane abin halitta, amma ke baki damu ba, sallah fa tsakanin bawa da Ubangijin shi ne suke magana,bawa ya kira, Allah ya amsa masa, bawa ya roqa Allah ya biya masa, bawa yayi godiya Allah ya mushi rahama, Hadiza wadannan ne baki so? Na saka ki islamiyya kin gudu, gani kk kin girmi islamiyya, amma shi iskanci baki girme shi ba, ke wai Hadiza ke ce zaki budema namijin da ba muharramin ki ba qafa ya gama zina ZINA fa Hadiza dake, ki tashi ki kade jiki ki dawon cikin gida ba kunya ba tsoron Allah na ganin dikkan abinda kukai inni ban gani ba, Hadiza kin cutar dani, kin cutar dani iya cutarwa,"
Hadiza kuka take barda majina mai yawa, ta ma rasa inda zata saka kan ta saboda tinawa da tarin zunuban ta, istigifari kawai take yi iyakar iyawar ta, tin tana yi a zuci sai da ta fara a bayyane, har wani shessheqar shidewa take, Goggo kam ta tabbata kalaman ta sun shigi diyar ta ta, hamdala ta yi a zuciyar ta sannan ta kama hadizan ta rungume, da qarfi ta qanqame ta, tare da sake fashewa da kuka mai qarfi, tinowa take da yanda take zama ta biyawa kan ta buqata da hannayen ta, da zuwa wajen samari da masu aure dan kawai tayi zina, kuka take sosai,
"Goggooo kkkkkiii yaaafee minnn,"
"Na yafe maki,Allah ya yafe mana dika, tashi kije ki fara gyara rayuwar ki tin yanzu,"
Da sauri ta miqe dan zuwa tai wanka,sai take jin jikin ta na jasa ne gaba daya, Goggo sai magana take mata, akan ba sai tayi wanka ba, kada kai tayi kawai ta wuce, ita kadai tasan qazantar da take ji a jikin ta, wankan ne zai sa zuciyar ta ta nutsu, kafin ta riqe ibada kamar yau aka haife ta.