Sashe 21
Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hello, gate din a bude ne ku shigo kawai,"
Cikin Mama ne ya bada wata iriyar qara, qululuuuu, su waye zasu shigo????
Aeeshaa ma shi take kallo, shi ko fuska a daure ya isa bakin qofa ya bude yana jiran koma su waye su shigo.
Da sallama Hajja ta sa qafa ta shigo, sanye take da wani dakakken lace,ta sha gwalagwalai,kunne da wuya, sai Baba General daya sha shadda kalar kayan Hajja, sai Baban shi da ke Bayan su.
Mama kashi ne kawai bata saki ba a wando dan tsabar shiga rudani.
Aeeshaa bakin ta sake tana kallon ikon Allah, shi waye ya masa wannan gayyar dik irin iskanci da cin zalin ta da yake? Shine zai ma mahaifiyar shi wannan gayyar rashin mutuncin,lallai Khaleefa halayyar shi daban ce a mutane.
"Sannu mai d'a, wato nan kk zo kina zuba masu mulki da dokoki ko?ke wa ya maki haka? Eyye nace ke wa ya maki hakan? Har kina ikirarin tsine mishi in baya baki kudi da kayan dadi, wai kayan dadi sai kace wata mayunwaciya, meye ke baki ci a gidan naki mijin? Na taba daga kai na na kalli me wannan yaron ke maki? Kin girma kina aikin jahilan yara, dibi ba girman Khaleefa,dan ki ne, kin ko san ke ba ta yau bace ko? Hakan bai sa kin nutsu ba wai kk zuwa roqo gidan danki? Tiiirrr da halin ki na ji matuqar kunya daya kirani yana fadan abubuwan da kk masu"
"Hajja qaraya yake min ban ce zan tsine masa ba, tambayi Aeeshaa,Baba kuyi hakuri ban kyauta ba,ku yafe ni,"
"Kin ban kunya, Maman khaleefa, me na rage ki da shi? Wannan ai qasqanci ne, da kuma tozarci, ki zo gidan suruka kina wannan abun, Aeeshaa fa diyar ki ce in akwai mutunci da kara, diyar qanwata ce fa,amma kk wannan zubar da qimar a gaban ta,kin ban kunya gaskiya,"
"Gwal da kk sa wa ido ni na sai mata, ni na bada kudi aka siyo mata su, kayan daki da na lefe da komai da kk gani Hajja ce ta je da kan ta ta siyo su, wasu ta bada izinin a shigo dasu daga waje, da kudin mu muka aura wa Khaleefa ita mukai komai, sisin shi babu, in banda yaro ne mai biyayya itama yarinya ce mai biyayya ba son juna suke ba mukai hadin, amma yanzu ba gashi komai ya wuce masu ba, ba zkai gode Allah da zamab lfyn da suke ba sai kin yi wannan qasqancin? Ashe in ba a tsaida ke tin yanzu ba har gidan yaran ki.mata sai kije ki saida daraja da mutuncin ahali na?"
Nadama ce mai yawa ta shige ta, nan da nan ta fara kuka tana bada hakuri akan halayyar data nuna ta son zuciya, ashe in kana da manya ba zasu barka ka yi rayuwa mara kyau ba komai girman ka, ba dan khaleefa ya kira su sun tsawatar mata ba da bata san inda mugun halin nan zai tsaya ba,
"Allah ya maka albarka da ka kira min magabatana, suka nusar dani illar abinda nake shirin aikatawa,Aeeshaa ki yafe min diyar albarka, gaskiya khadeeja tayi qoqarin baki tarbiyya mai kyau, Allah ya saka maku da alkhairi, a gaskiya naji kunyar wannan mummunan abun dana aikata,"
Hawayen na dama ne ke zuba mata, Khaleefa ke ta latse vedio call din da Rebecca ke ta damun shi da shi, tin ba wanda ya kula har baba General ya kula,
"Go and answer ur call,"
A tinanin su tsabar ladabin shi ne yasa bai son amsa waya suna magana mai mahimmanci.
Qauri ne ya tirniqe gidan,da sauri Aeeshaa ta tashi ta nufi kitchen, farfesun zabbi ya qone, kunya ce ta sake kama mama,dan ta san dan ita aka dora abinda tafi garfin shi.
"Don't call me i am with my parents,"
"K zaka shigo?"
"No"
Abinda ya fada kenan ya kashe wayar,Hajja ce ta kalle shi, wani abu ya darsu a ran ta game da wayar da Khaleefa yayi,
"Wa ce ta kira ka?"
Tambayar data jefa masa kenan, cikin daburcewa da in ina ya ke.amsa ta,
"Aaaaboookiiyar aikinaaa ce ta ta take tambaya ko zanje office yau,"
"Oookkkk, me xai sata kiran ka? Ko sama take da kai a wajen aikin?"
"Eehhhh itace babba dika wajen,"
"Oookkk"
Abinda Hajja ta fada ke nan tana ci gaba da kallon Khaleefa, akwai wani abu a qasa.
Ba zai iya jure wanan kallon na kusan kama barawon ba, tashi yayi ya bi bayan su Aeeshaa.
"Wannan amarya kamar a qauye,kin dora abu tsabar kin ga na sha kwalliya kin kasa dauke idon ki akaina shine kk babbake tukunyar da kk dorawa megidan abinci, dariya Mama da Baba suke, inda Baba ke kade hannun shi dan wajen taimaka wa Aeeshaa ta sauke tukunyar da tai baqi ya dan qone, Mama kam jikin ta qaura yayi isha'i, sai yaqe kawai take,Allah2 take a bar gidan kunyar su take ji yanzu.
Nasiha Baba General da Hajja sukai masu sosai, sanan suka sake yi ma mama gargadi da nasiha itama, wadda sai da ta da Khaleefa yaji ba dadi shi ya janyo mata wannan tonon asirin, amma gwanda daya mata hakan, da ba dan haka ba da ba xai samu sakewa ba a gidan shi, kuma ba zai samu sakewa ba, dan yasan Mama in ta qafdari zuwa gidan, ba zai dinga sakewa da iyalin shi ba,kuma ba zai sake ba da kallace2n shi komai a darare xai dinga yi,sannan zuwa wajen Becca zai na masa whala, so gwanda ya yiwa tufkar hanci.
Baba General sai da ya bama Aeeshaa kudi yace koda zata yi wani abu da su, tinda ga ciki tana dauke dashi, sannan suka tafi,Hajja na qarewa Khaleefa Kallo, kallon ina ganin ka,kome kk qullawa zan binciko.
Dauke kai yayi, yana qoqarin saka fuskar shi ta ba abinda nake aikatawa mara kyau, rungume Aeeshaa yayi a gefen hannun shi, yana daga masu hannu bayan sun shiga motocin su, Hadiza na ganin manyan motoci suna wucewa sai zare ido take, ta qara tabbatar da lallai su din masu hi ne, burin dake ran ta sai qara habaka yake,yana qara girma.
Har zasu rufe gate din, ta yi saurin fitowa daga soron gidan nasu, tna taku daidai.
"Hadiza, kina gida dama? Dan Allah amson quli na dari biyu wajen Goggo in kin kawo na baki kudin,"
Wani kallo khalefa ya watsa mata, akan me zata masa gayya bayan ta kula da yanayin shi yana buqatar ta.
Shigewa ciki yayi, ita kuma ta sake iskar bakin ta, sarai ta gano shi, ita kuwa she is not ready, haja kawai bai da aiki sai yayi ta....... ba zata iya ba gaskiya.
Gudu2 sauri2 Hadiza take diban qulin nan dan ta kai ma Aeeshaa,fatan ta Allah ya sa khaleefa ba fita zai ba su hadu.
"Ina zaki ne kk sauri haka?"
"Amarya ke son quli na dari biyu,"
"Tau ki kyauta mata., ki kuma gaida min ita,"
Gudu2 take tafiya har ta kai soro,
"Zataji,"
Koda ta isa gate bude yake, dan haka shiga kawai tayi, sai da ta dan gyaggyara sanan ta fara kwankwasa qofar, Aeeshaa taje fitsari, dan haka Khaleefa ne ya bude qofar.
Tana ganin shi ne,ta wani narke, tana lashe lips, tare da cizar lip din ta na qasa, tana wani kada ido, da banqaro qirji, ta miqa masa,
"Kace mata ta bar shi, Goggo na gaida ta,"
Khaleefa fa ya tafi da wannan salon, a iya sanin shi da mata in mace na haka tana son kasancewa da namiji ne, lallai wannan 'yar hannu ce, za a je da ita.
Hannu ya miqa dan karba, aiko wajen bashi sai da ta san yanda tai ta goga hannun ta sosai a nashi, wani abu yaju ya jashi, nan da nan ya sakar mata murmushi, wayar shi ya zaro da sauri, yace ta sa mashi no ta, ba bata lokaci ta saka kuwa ta miqa masa, murmushi suke sakar ma juna. Su,
"Hadiza kin kawo? Ga kudin, yi hakuri na dan zaga ne,"
"Ba komai zan bata koma ciki, na hana ki yawo a gida da wannan qaton abun ko, wuce ki je ki sauya, itama tafiya zatai, bana son ana takuramin a gida,"
Jiki ba kwari da kuma kunyar hadixa a ran ta ta bar wajen, yanzu a gaban maqota ma sai ya nuna halin shi, kuma a fakaice yana nuna ma Hadiza kar ta na zuwa masu gida fa kenan.
Bayan ta shiga ciki ya rage murya.
"Zamuyi waya, zan fada maki inda zamuna haduwa,kinyi min"
"Nima ka yi min,ina jiran ka,"
Juyawa tai tana tafe tana rausaya, Khaleefa ya gama miqewa, Allah2 yake dare yayi, yau in bai kadaita da Hadiza ba akwai matsala...................
*Khaleefa kai dan akuya ne, wake tare dani akan hakan?*
*Ina da tambaya, shin kuna ganin akwai miji kamar Khaleefa? Ko kuwa kuna ganin Inaaa ba za a samu miji haka ba? Ina jiran ra'ayoyin ku, koda kuwa da labari ne na makamancin halaye irin na Khaleefa*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼
*BY HAERMEEBRAERH*
*Sorry jiya page 16 ne na yi mantuwa ban saka no ba*
Page 17:
Aeeshaa dai bata da anmsar bashi dan haka kwantawa kawai tayi a kusa da shi tai shiru,
"Ina miki magana kin yi min shiru, wannan ai raini ne,"
"Yah Khaleefa nima ban sani ba, tida yace mu jira wata biyar mu gani mu jira mana, me ne ne abin saurin a ciki, muka jira watannin baya sai na gaba ne zai mana wahala? Dika2 wata nawa ne ya rage yanzu, dan girman Allah kayi hakuri bacci nake ji,"
Whaaaatttt? Did u hear that? Aeeshaan ku fa ta fara zama babbar mace😅
Khaleefa bai samu bakin magana ba, shiru yayi yana nazarin a wanne yanayi wai take maganar nan ne? Fada ta masa ko fada masa fact din take kawai? Yana wanan tinanin har bacci ya dauke shi a dakin Aeeshaa, yau ne rananta farko daya kwana a dakin, da sai dai lalurar shi ta kai shi da farkon dare ya tafi ko ya je mata da tsakiyar dare ko kuma da asssuba kamar maye🙊