← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 41

Sashe 31

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(Goggo kin iya qoqarin ki, sana'a harda saida quli kinyi a shekarun da wasu suna can suna cashewa a gidan miji, babban laifi na dangana shi ga dangin uban Hadiza da basu taimaka maku ba financially, sannan kuma sun gaza wajen tsayawa a koda yaushe suna zuwa Hadiza taji akwai namiji fa akan ta da yake kula da ita, har da matsalar dangin ki Goggo ba ke daya bace, saboda da basu dorawa kan su girman kai ba na in kana da shi muyi da kai, in baka da shi ba zamuyi d kai ba, rayuwar mace bazawara wadda mijin ta ya mutu ita daya akwai illa a barta sakaka, musamman gata da diya itama bazawara, ku dubamin Umman Aeeshaa, da dangin ta suka tsaya mata suka ja ta a jiki, aka hada su da namiji yake zaune da su, bayan ya tafi Umman Aeeshaa dik da tsananin ta yayi yawa amma ba laifi an samu Aeeshaa mai kyakkyawan hali matsala daya bata da wayewa ta zamani dan haka bata san ya zata tafi da rayuwar gidan auren ta ba, har ta samu na sarar gyara tauratauran mijin ta ba, so ni dai a ganina Goggo kar ki dorawa kan ki laifin, ko ya kuka ce fans)

Hadiza na zaune tana qulla irin rashin mutuncin da zata yiwa Khaleefa, dan haka miqewa tayi ta yi wanka, ta shirya cikin shigar ta da take yaudarar mutane ta leqa taga Goggo na kan sallaya dan yin sallar asr, fita kawai tayi dan tasan Goggo ta san ina zata hanawa za tai, bata shirya haifar dan da bai da uba sananne ba.

***********************

"Hajja dan Allah kiyi hakuri, ki saurari me zan fada maki, kar ki ga laifi na akan qin sanar dake abinda ke faruwa agidan aure na, ba wai soyayya ce tsakani na da Yah Khaleefa ba, komai zai min a cikin hakuri zai min nima haka,dan haka ban ga dalilin da zai sa na kawo qarar shi ba. Rayuwar shi dama ya saba ta tin kafin nazo, ni shaida ce, sai da nai kuka,nai roqo kar a hada auren mu, Hajja ke kk ban hakuri kuma na hakura, hakurin na ci gaba da yi dan baki nuna min yanda zan kwaci kaina ba in ana musguna min, Ummana bata koya min ba, Hajja laifi na ne?"

Hajja da sauri ta rungume Aeeshaa dake kuka, dan iyakar gaskiyar ta take fada, (ku kula da wani abu, still Aeeshaa bata fadi aibun Khaleefa ba fa har yanzu, saboda bata son aibata ma Hajja jikan ta a gaban idon ta, tana son komai Allah ya bayyana masu shi su gani, domin addu'ar ta ke nan a boye kullum, hakan ne zai bata qima a idon kowa da daraja da daukaka, da kuma soyayya da tausayawar kowa)

"Aeeshaa ki yafe mana, mune muka tura ki inda zaki wahala, da na san boyayyen halin wannan dan banzan da ba zan dage a hada ku ba, a tinanina shi din mutumin kirki ne, MUN MAKARO yanzu, cuta ya riga ya cuce ki, ki kwantar da hankalin ki, yau yau dinnan za a dakkon dan iska ko da kuwa a kan magajiyar karuwai yake kwance ba karuwa ba,"

Kunya ce ta kama Aeeshaa ta sunne kai, hira suke ta tabawa, suka ji horn din motar gidan.

"Is time, saka hijab muje,"

Saqo Hajja ta duba a wayar ta, nan da nan ta fara kiran yaran ta gaba dayan su, har Umma.

Sojoji ne majiya qarfi, wanda in aka hada mutum goma da daya sai sun ji a jikin su, dan dukan mutuwa zasu mashi, su biyu ne, sai muzurai suke, dik wata cika da bunqasa da kamalar Khaleefa ta bace, Sabeer ne da Hassana suka fito, Hassana na ganin wasannan gidiga2n ta koma baya tana karkarwa, meke faruwa? Sabeer ma dan namiji ne, ya sa ya tsaya yana matsewa tare da tambayar su su din su waye?

Banza sukai da shi, sikabi kwatancen Hajja, dayan ne ya leqa cikin mota ya damqo Khaleefa, ya wurgo shi waje, Khaleefa dai ba baki, yayi magana bai san wadannan mutane me aka umarce su smasa ba, dan haka a gaba ya wuce tin kafin su yi magana da muryar su kamar aradu.

Motar Umma da Keke napep din Hadiza a tare suka iso, bude masu akai kowa ya shigo, Umma na kallon Hadiza Hadiza na kallon Umma, kowa da abinda yake saqawa a ran shi..............................

*Ba zan iya aje ku cikin jira da jimamin me zai faru ba, thanks for the love, Uhibbukum fillah,Allah yasa nima domin shi kuke so na ba domin novel ba❤*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

Page 23:

Kowa ya taru a parlour, Hajja ta fita waje da sojojin da tai ta sawa aikin kula da shige da fice Khaleefa waje, kudi ta dakko masu yawa ta basu amma sam suka qi amsa, saboda sun sani ba zasu biya General abin da ya musu ba na kyautatawa.

Haka tai ta masu godiya, ta koma ciki, General kan shi yayi mamakin wannan abu, dan baida masaniya akan ko daya, kowa jira yake yaji me Khaleefa ya aikata da aka masa wannan kamun kazar kukun, banda Baban shi, dan Baban shi ya san tabbas Hajja na sane da iskancin da yake aikatawa, shine dalilin taron, ran shi baqiqirin saboda taron akan ahalin shi ne.

Sallama tayi a bakin parlourn ta jira akai maya izinin shiga,

"Baiwar Allah daha ina?"

Umma ta tambaye ta,

"Khadeeja bar ta ta zauna, zaman itama ya shafe ta,tin sanda na gan ki dama na san ke ba alkhairi bace a cikin iyalina, zauna kema,"

Hadiza dik jiki a sanyaye, to me aka sani game da ita kuma?

'Yau na kawo kaina makasa, dan naga wasu qattin sojoji a waje bayan dattijuwar nan ta gama.masu magana naga sun qame, Allah k kare ni kar a nadan duka,'

"Assalamu alaikum, kamar yanda kuka sani, dik wani abu mai mahimmanci muna masa zama, saboda mu samu mafita in muka hada kai wajen warware dikkan matsalar mu, dan haka wannan karon ma ni Hajja Aeeshaa na gayyato ku dan na sanar daku halayen Khaleefa wanda mu kakanni da iyayen shi bamu san yana dauke da su ba, wanda ko mai Khaleefa ya zama a yau, zan dorawa ma ku laifi iyayen shi da General kan shi, sakamakon sangarta shi da akai, wanda kullum fada na kenan da yana yaro, ba laifi bane bawa yaro gata, amma irin wanda akai ma Khaleefa yayi yawa, kasancewar shi jikan fari a gidannan, yasa aka shagwaba shi, komai extra ake masa akan sa'o'in shi,kar na cika ku da surutu, ku duba wannan hotunan, sannan ke kuma ki nuna masu abinda kk gani a wayar ki,"

Nan da nan Aeeshaa ta shiga wajen hotuna inda tai screenshot din hoton Hadiza da Khaleefa, Hajja ta rarrabawa iyalan ta hotunan da aka wanko mata,

Masu salati na yi masu hawaye ma nayi, masu kada kai da bude baki nayi,kowa da irin reaction din shi, a sannan ne Aeeshaa ma ta samu ganin hotunan, Hadiza kam ba baki, sai raba ido take,saboda in wasu suka kalli hotunan hannun su sai su kalli Hadizan,

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un,yanzu Khaleefan mu shi ke aikata wannan mummnan zunibai? Camerar mutum ta dauke ka haka Khaleefa ina ga vedio da zaka gani na kan ka a lahira wanda daga ubangiji yake har na dakunan da ka shiga ka aikata laifi sai an dakko? Mun fita dikkan haqqin ka Khaleefa, gaskiyar ki ne Hajja laifi dik namu ne musamman ni, a ganina shine jikana na farko, shi yasa na shagwaba shi, na bashi dikkan gata, ashe gata na yawa? Abinda zaka saka mana da shi kenan? Zina?da auren ka? Ka ban kunya Khaleefa, ka kuma fita daga raina,"

Kuka General ya fashe dashi dik daurewar da yake ba zai jure ba, irin wannan hotuna haka.

"Ita wannan din wace ce, wannan dai gata a gaban mu,"

"Ita ce inajin wadda ka kk cewa zaku Abuja ko? A kai ku club mai tsada, tin da ka tafi ja kashe wayar ka,ko ina baka nan, ba yanda za ai a gan ka ko a ji ka,"

Tashi yayi ya hau dukan Khaleefa, ko ta ina duka yake, Maman shi kallon shi kawai take, ta kasa koda kukan ne, lallai wannan zamani na da abin tsoro, zina tayi yawan da har yaro zai na aikata ta iyayen shi na zaune baki bude basu sani ba, kuma mutane na gani, dan ga shi Khaeefa da Hadiza a bainar jama'a tana shagwaba yana lalashin ta wani ya dauke ta, wani a mota suna shan ice cream, na wayar Aeeshaa ma suna shan Ice cream ne a rana daya ne da wanda sojojin suka dakko, sannan ga in da ya aje ta, ga inda ya shiga gida itama ta shiga nasu gidan, ga inda da Aeeshaa tai ta fiya take satar jiki ta shiga da sanda take fita, har time sai da suka rubuta a jiki,

Aeeshaa ma kukan take, nan da nan Sabeer ya dinga tina ganin shi da yayi da wata, har ya tambayi mai gadi ya qaryata shi, ya rufa magana.

Hassana sai godewa Allah take da bai hada ta da shi a matsayin miji ba, da har zata cuci kan ta akan son zuciya.

"To yanzu dai kun ga ko nace mun ga waye jikan mu, kuma dan ku, in ka yi qoqarin boye mana halayen ka munana, Allah yana kallon ka, dan haka yanzu meye hukuncin daya dace da shi, dan ba zai zama an kyale shi ba,"

"Da farko da kan a yanke hukunci ya kamata aji me ya kawo wannan yarinya,"

Kallon kallo sukai da Khaleefa, ya mugun ba Hadiza tausayi, Aeeshaa ma sak da ta tausaya masa, dan da alama ya ci uban bugu wajen sojojin nan wajen masu taurin kai, bakin shi a kumbure yake kamar wani barawo, rigar shi ta yage ta gaba, da gani an jijjiga shi yafi a qirgawaya sani ma ko da rigr suke daga shi sama?

Amma da alamar har yanzu bai laushi ba, saboda yanda yake wani ciccin magani.

"Ke yarinya me ke tafe da ke?"
Chapter 31 · 0% Book details