← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 41

Sashe 17

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin jin dadi ta gyara wajen, ta toshe hanci da dankwalin ta, ta juye doyar a leda ta sa a shara.

Tea itama ta hada mai kauri ta hada sandwich, da ita da shi, ta dau nata ta kai daki, sannan ta dau nashi ta kwankwasa qofa, ya bata izinin shiga,yana zaune yana kallon wani American movie mata kamar tsirara suna ta yawo da maza ana shan iska ana ta kisses, saurin dauke kai tayi tana istigifar, ta aje masa, ta sake bashi hakuri sannan ta fita.

Ko kula ta bai ba, ta na fita yayi sufa ya dauke plate din ya fara ci.

"Yarinya qarama sai iya girki da kuma dadi wajen......."

Aeeshaa sai da taci ta qoshi, tai nawafil sannan ta kwanta.

Bacci tasha mai dadi, ba takurar Khaleefa for the first time tin da aka kawo ta.

Yana can yana vedio call da Rebecca, gaba dayan su tsirara suke daga shi har ita, hankalin shi kwance.

Suna cikin aikata masha'ar su Rebecca ta mai tambayar data ja mata katsewar harkar su.

"Where is ur sweet wife, da ake kirana da sunan ta wataran, tsabar dadin ta?"

"Shut up, i said shut up, don't u ever mention her name again, in kk sake maganar ta, daga yau alaqar mu ta yanke, na fada maki kar kina sa kan ki cikn iyalina, stupid"

Duqawa yayi ya kashe dik da kiran sunan shi da tai tayi tana bashi hakuri,haka nan baya son matan banzan shi na waje suna maganar iyalin shi, ko ma meye matar shi ce.

Takaicin ta yasa ya kwanta rufda ciki har bacci ya dauke shi.

(Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, what if ya mutu a haka fa? Shin ya ku masu biya ma kan ku buqata da kallon fina2n batsa da karanta novels na batsa in kuka mace fa? Aka xo ganin ku a ga film na playing na batsa? Mala"ikun daukan rai suga novel din batsa? Ko kuwa ki/kaje lahira da record din last abinda kayi shine buyawa kan ka buqata ko kallon haramun? Wallahi mutuwa na kusa da mu fiye da yanda muke tsammanin ta. Ya Allah ka kare mu ka tsare mu ka katange mu daga aikin dana sani, Allah ka kare mu daga zina babba da qarama, ya Allah ka yafe mana laifin mu babba da qarami, wanda mukai bisa kuskure ko bisa ganganci, ameen ya Rahman).

Da safe Aeeshaa wainar flour take kwadayin ci, tinawa tai ta kwan biyu sosai rabo ta da cin ma wainar flour, murmushi tai dan dadin dataji ya kama zuciyar ta data tina zataci din.

Nama ta tafasa ta yanka qanana, ya sha kayan qamshi harda garlic, ga dandano, ta jajjaga attaruhu, ta yanka albasa mai yawa, ta dakko kwai, ta aje gefe, sai da ta fara kwaba flour da ruwa tai dan kauri kwabin ba tsululu ba, sannan ta saka maggi, da curry da yankakkiyar albasa da attaruhun data jajjaga, ta fasa kwai biyar, ta kada ta fara suya da man gyara, dakko yajin ta tai mai tafarnuwa, data soya daya ta dale kujerar kitchen din ta cinye, a haka sai da ta qoshi sosai.

Sannan ta hadawa Khaleefa nashi, ta kai dinning ta aje, ta san ki sallah bai ba, tinda baya kwantawa da wuri,yana aikin sabon Allah, haka zai makara wataran sai alarm ya buga ya farka, kuma sai ya sake bata lokaci wajen wanka, sa kaya sannan a jefe sallar a fita a ci abinci a fice.

Daki ta gudu dan bata son su hadu, amma yau Khaleefa baya jin fita ko ina, yana son ya fanshe daren jiya da bai samu yanda yake so ba, shi kuwa ba wai mai hakuri bane akan wannan harkar, gashi sunyi fada da mutuniyar tashi, balle ya je mata.

Bari ya gani in yarinyar nan ta iya yin girki yau a kan ta zai fanshe, in kuma batai ba sai yaje ya yi kallo har ya samu yanda yake so.........

*wayyoooo wa zan aika yaje ya fada ma Aeeshaa taje ta kwashe abincin dinning? Ga azzalumin nan zuwa😨😨😨😭*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

Page 13:

Sai da ya shirya tsaf, ya tabbatar ba wani qazanta a jikin shi, har da tirare sai da ya fesa, ya sake brush, sannan ya nufi dakin, ya daga hannu zai qwanqwasa ya tsaya, kakarin amai ya ke jiyowa a ciki, wai meke damun yarinyar nan ne? Kamar zai koma ya daure dai ya bude qofar, tana toilete so bai gan ta ba, shiga yayi tare da toshe hancin shi, dan tsakanin jiya da yau ya tsani ya maimaita ganin amai.

"Kinje kinci wani abun ko?"

Cikin nishi da kuma zazzabi da take ji ta daga kai ta ga yanda ya toshe hanci yake qyanqyamin ma ya isa gare ta,

"Wainar flour naci, na sha tea ban sani ba ko qarnin madarar ne ke sani amai,"

"Ke kk sani, kije garin kwadayi ki kashe kan ki,"

Juyawa yayi ya fita, ya koma dakin shi, ya shirya, dan ba zai wani zauna ba tana faman amai, gwanda yaje su daidaita da Rebecca ya dan yi buyagi yayi fushi a shirya a bashi abubuwa.

Tin da ya fita take kwance tana kuka, wai bata da lafiya ko zancen kaita asibiti baya yi, gashi ita ba wanda zata fadawa, iyalin ta basu damu da ita ba sam,Hajja ce ke damuwa da lamarin ta,ita kuma ta rasa me yasa kwana biyu bata neme ta ba bata zo ba.

Yunwa take ji amma bata san me zata ci ba, kuka ta sake fashewa da shi, wannan wace irin rayuwa ce.

Haka rayuwar Aeeshaa ta ci gaba ita da Khaleefa, a cikin wannan halin quncin, da takura, Ameena ta zo mata inda tai weekend ta koma, cike da farin ciki, yanzu amai da tashin zuciya ya ma Aeeshaa sauqi,sai dan banzan kwadayi.

Yanzu cikin Aeeshaa ya kai wata uku, Khaleefa dik wata hanya da zai hana mutan gidan su zuwa yi yake, saboda yanda Aeeshaa ta rame tayi fari kamar mai tsutsar ciki, baya son a gan ta a haka, Hajja kullum sukai waya sai tace masa in bai kai mata Aeeshaa ba zata zo ta ci mai uwa a gidan, kullum qarya yake zabga mata, yau basu nan suna Abuja shaqatawa, gobe suna Kaduna, in tai waya ya ba Aeeshaa sai ya tsare ta da ido, ya sa a handsfree, Aeeshaa tayi sak kamar ba abinda ke faruwa, sai sun gama waya ta sha kukan ta, ko zuwan Ameena ma da kyar ya yarda tazo,bayan sharuda daya yi ta kafa mata.

Aeeshaa tsoro take ji ko wata cutar ce ta kama ta, dan kuwa cikin ta na dagawa, ga qirjin ta da ya cika taff, sai ido da ya zurma mata, ga shi sai kwadayin da take yawan ji ke qara tsorata ta.

'Oh ina ma ina da waya ko gida dana kira na sanar ma da ummana meke damuna yanzu, ko ba zata kula ni ba a qalla ko mutuwa nai an san meke damuna,'

Hawayen ta ta share, ta gyara kwanciya a kujera, wani qamshi taji yana tashi, kamar an soya man gyada irin asalin man gyadan nan, kamar kuma ana soya nama, qamshin dai mai dadi sosai, da ga dikkan alama daga maqotan ta yake fitowa, tashi tayi ta zauna tana ta shaqar qamshin, hankalin ta ke qara tashi in tana shaqa, tana mutuwar son taci ko me ake soyawa dinnan.

Ga shi ita ko irin gaisawa da maqotan nan batai ba Khaleefa ya hana, ko sau daya bata taba shiga masu ba,kuma ya bata umarni in an zo indai ta leqa taga bata san mutum ba kar ta bude ta kma ciki, ta tabbata sun sha ganin inuwar ta tana leqa su kuma ba ta bude masu ba, Ohhh wannan zaman kafurci haka, in ta mutu ba wanda ya sani sai ya dawo daga yawon ta bididin shi sannan.

Kasa hakuri tayi, dan yanda take jin ta ko zai kashe ta ne in ya dawo sai ta ci me ake soyawa.

Hijab ta saka ta dakko makulli ta fita, sai da tai addu'ar fita daga gida sannan ta taka waje, wata ni'ima ta ji ta daki hancin ta, tinda aka auro ta aka kawo ta bata sake fita ba, iyaka ta hango waje in tazo bude gate da safe ko da dare in zai fita.

Inda qamshin ke fita nan ta bi, tana zuwa soron gidan ta ji inaaa ba zata iya shiga ba, juyawa tai zata koma suka ci karo da wata matashiyar budurwa, ta girme ta amma ba sosai ba,

"Baiwar Allah sannu,"

"Yauwa"

"Wajen wa kk zo?"

"Ummmm.... damaaa... ni..nii maqociyar nan gidan ce, ni ke zama a wancan gidan dake dama da wannan, na dan leqo ne a gaisa, kuma na ji ba zan iya shiga ba, na dade a unguwar ban shi ba sai yau na ce bari na leqa a gaisa,ke fa? Wace ke?"

"Hummm... Ayyaaa ashe kece amarya me rowa ko?"

Dafe qirji tayi ta fiddo ido,

"Me rowa kuma? Rowar mi na maku? Anan gidan kk kema?"

"Hhhhh kwantar da hankalin ki, ina nufin rowar ganin kan ki, eh anan gidan nake, suna na Hadiza, mu shiga ciki, ai na sha zuwa baki bude ba, ni da Goggo ma mun sha zuwa baki bude ba"

Suna shiga ciki Aeeshaa ke bata hakuri,ta nuna mata mijine mai kulle take da shi, ba laifin ta bane, mamaki Hadiza tai, dan ita ba qaton da zai mata kulle tabbb, dama har yanzu ana kulle? Kusan akan kulle ta koma qaramar bazawara fa, inaaa, ba dan da zai mata kulle ta zauna.

"Goggo ga amarya mai rowa nan ta zo gaida mu yau,"

Wata dattijuwar mata ce mai tsananin kamala, da nutsuwa,tare da annuri a tattare da ita, tana ta soya quli2.

"Ahhh lale maraba da ke amaryar me rowa,"

Dan dariya Aeeshaa tayi, tare da hadiye yawun daya yanko mata, ganin quli mai zafi, ga qamshin nan kamar ana soya kaza.
Chapter 17 · 0% Book details