← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 41

Sashe 5

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umma ce ta leqa bangaren su Khaleefa domin kiran su Ameena su wuce gida, da sallama ta shiga, da gudu Ameena ta fada jikin ta,bayan ta zauna Maman Khaleefa ta koma ta zauna itama, shir sukai, yanzu sun zama surukai, cann Maman Khaleefa ta nisa tace,

"Khadeeja in kina ganin wannan hadin bai maki ba karkiji komai ki sanar dani, zan ma Abban su magana, a yi wa Baba General bayani sai a fasa, dan na kula kamar baki son wannan hadin, kar ki damu ba zan ga laifin ki ba, Khaleefa mutum ne a baibai, ba ka gane gaban shi bare bayan shi, ni kaina hakuri nake da shi,balle qaramar yarinya kamar Aeeshaa."

"Aunty ni ba ni da wata matsala ta bangare na, matsala daya ce dama, naga kamar Hassana ke son shi, kuma an juya an bawa Aeeshaa shi, hakan anya anyi daidai kuwa?"

"Kar ki damu, Baba General na sane da hakan, ya duba yanda Khaleefa bai son Hassana ne kwata2, a haka da halin shin nan na shiru2 ma ya aka qare, balle bai son abu? Amma a qalla sukan gaisa da Aeeshaa, na kula har 'yar tambaya yana mata ya makaranta? Ki fadan a gidannan banda ina kwana ko ina wuni wa Khaleefa ke kulawa? Tin da ya shiga shekarun balaga yaron nan ya sauya halaye, ya tashi daga mai son mutane zuwa wannan mummunan hali, mun kai shi asibiti yafi a qirga dan aga ko akwai abinda ke damun shi, amma inaa,"

"Aunty babu wata matsala,Allah ya shige mana gaba,"

"Ameen"

"Ku shirya mu wuce ku kuma,"

"To Umma, amma ni fa naga Yah Sabeer ya fita kamar yana kuka,har yanzu bai dawo ba, wa zai maida mu gida?"

"Muje na gani, in ya dawo ya maida mu, in bai dawo ba sai mu tafi,"

Sallama sukai, sannan suka shiga bangaren su Sabeer, cikin fara'a Ummeen su ta masu maraba, Hassana ta hade girar sama da ta qasa, dan ummeen su ta mata fada taji ba shi zai sa ta sakar wa da goggon nata fuska ba, har yanzu haushi suke bata.

"Aunty Sabeer fa? Yana ciki ne ya zo mu wuce gida, dare nayi,"

"Sabeer kam ban shigo na isko masa ba, sai dai ki gwada wayar shi,"

"Ok to bari muje waje, na jira magariba ta gabato,"

Keys din su Hassana ta miqa mata ta dauke kai, a ran Umma tana tausaya ma diyar yayan nata, amma ba yanda zatayi, karba tayi, ta kama harda hannun ta, sannan ta daga kan ta, suka fuskanci juna,

"Hassana i knw what is going on between u and ur brother, but i can't do anything about it, i wish i can do something, u ar both my children, and i love u so much, bana son abinda zai bata ran ku, yanzu abinda nake son ki maida hankali akai shine, addu'a, in rabon ki ne Khaleefa Allah za baki shi,koda kuwa ya auri Aeeshaa ne, tinda ba haramun bane, share hawayen ki kinji?"

Kuka Hassana take sosai, sannan haushin Goggon nata ya ragu mata, ta fuskanci itama ba a son ranta akai hadin ba.

Goge hawayen ta tayi, daga nan sukai Sallama suka fita, ta kira wayar Sabeer amma taji ta kashe, tasan za ai haka.

**********************

Azkar take koda suka shiga gidan, direct Ameena ta je wajen ta tana murnar ganin ta, kamar wadda suka shekara basu tare, Abdul dakin shi ya wuce danyin alwala yayi sallah, Umma ce ta zauna a kujera tana nazarin abubuwan da suka faru, tana tinani ta sanar da diyar taga ko ta bari sai ta kammla karatun ta?

"Umma nace sannu da dawowa, ya kuka baro su?"

"Lafiya, debon ruwa kuma mara sanyi, me kk dafa?"

"Tuwon masara nayi da miyar busasshiyar kubewa da busasshen kifi, da ganda,"

"Zubomin, ki ajen a daki, bari naje nai sallah,"

Amsawa tayi sannan ta miqe dan cika umarnin mahaifiyar tata,

Lokacin da ta shiga dakin tana sallah, dan haka ta aje, nan ta ga yanda Umman nata ta wurgar da kayan ta, jaka takalmi a qasa, mayafin data yafa a gado yana reto yana taba qasa, sarqa da dan kunnen data saka a gado ta watsar, dakin da ya sha gyara mai kyau,ga qamshi mai dadi, ta mayar haka daga dawowar ta.

Cikin yar shagwaba bayan Umman ta idar Aeeshaa tace,

"Umma baki ga yanda na gyara maki daki ba ne? Diba yanda kk bata Ummaaa,"

"Na bata din,nace na bata din, dakin ki ko nawa? Gyaran ma d dik qura,"

Saida Aseeshaa tayi dana sanin wannan magana da tai, fada Umma ta fara tayi ta kuma.

Kanta a sunkuye ta fara debe kayayyakin, tana saka komai a muhallin shi, wai ace magana mao dadi ta gagara a tsakanin su, tana kammalawa ta fita, ranta na mata suya.

******************

Cikin dare Sabeer ya dawo ya kwashr kayan su daya bayan daya, ya sa mai gadin gidan ya rufe gate, shi kuma ya wuce, ba zai taba iya ci gaba da zama da Aeeshaa a gida daya ba, bayan sanin wannan mummunan labari.

Yana mota yana tafiya, cike da tinanin rayuwar da kullum yake tsara masu, ya ga motar Khaleefa, baqin glass gare ta ta kowanne gefe da gefe, amma ta gaba haske ne da shi, ta nan ya hango an kwantar da kujerun motar, tsayawa yayi da tashi motar daga neda da su, sai da aka dade, sannan yaga wata yarinya ta dago tana maida rigar ta, Khaleefa ne shima ya taso ya na gyara rigar shi, matsanancin mamaki ne a fuskar Sabeer, m hakan yake nufi? Bai gama tunani ba, yaga Khaleefa ya fito, yarinyar ta fito itama, kudi Khaleefa ya bata, ta tsaya tana kadasu, tare da yi masu kiss, tana wani karairaya a gaban shi, shi kuma ya rungume hannayen shi, daga masa hannu tayi zata tafi, ya daki ***** ta baya, ta sake kada masa su, sannan tai gaba.

Sabeer sumane kawai bai yi ba dan tsoro da mamaki tare da tashin hankali, yaushe Khaleefa ya ke harka da mata? A kusa da unguwar su, dama haka halin shi yake ko kuma dai yau ya fara saboda damuwar dayake ciki? Dan ya kula bai son hadin shima sam, anya yau ya fara, kuma khaleefa ne harda wani dariya da wani yi mata wasa, kaiii mafarki yake.

Yana nan yana tunani bai san khaleefa ya wuce gida ba, da sauri ya tada motar shi ya nufi gidan, ko a hanya basu hadu ba, ajiyar zuciya ya sauke, sannan yace,

"Alhamdu lilLAAH ba shi bane, habaa har zuciyata na neman bugawa, bari dai na tambayi Baba mai gadi naji,"

Sallama ya ma Baba mai gadi, sannan ya masa tambaya akan yaushe Khaleefa ya dawo, Baba mai gadi shiru ya danyi, yana tina kudi da Khaleefa ke bashi akan yana rufa masa asiri,ga tsoratar da shi da yayi dik sanda ya fada ma wani baya dawowa da wuri gida washegari zai bar aiki a gidan.

"Baba magana nake, yaushe Yah Khaleefa ya dawo?"

"Ai yau Khaleefa in ba masallaci ba yana ciki, da dikkan alamu baya jin dadi, tinda shi mutum ne ba mazaunin gida ba,"

Hankalin Sabeer ne ya sake kwanciya, dan ba zai taba yarda a aurawa Aeeshaa mai neman mata ba, nan ya fara jin ba dadi daboda zargin da yayi ma dan uwan shi, tabbas kama ce kawai, da hukunci na Allah, dama yana ta mamakin dariyar wancan da ya gani da wasan shi, Khaleefa ba halin shi bane.

Kayan shi ya dinga diba yana kaiwa cikin dakin shi na gidan, yayi qura sosai, amma sai da safe zai gyara saboda dare yayi sosai, Khaleefa na hango shi ta window yana murmushin mugunta, domin ya hango shi shima, wannan dalilin ne ya sa yayi sauri ya dawo kan su hadu, dan zuciyar shi na raya masa yaron ya gan shi.

Sauke labulen yayi ya koma ya kwanta, ba dan Aslamiyya karuwa bace da ita zai aura, ta yi iya yi, ta kai dik irin macen da yake so, ita saboda ma yawon ta fito ta juya mahaifar ta, tsufa a tattare da ita ba shi kenan, ga jikin nan perfect yanda yake so, sabuwar sha'awar ta ce ta kama shi, miqewa yayi ya dakko laptop din shi, ya shiga wajen fina-finan shi na banza, ya saka wannan ya cirs ya saka wancan ya cire, a haka ya biya ma kan shi buqata ya kwanta yana hutawa, kafin daga bisani ya dauke komai ya shiga wanka, ya dawo ya kwanta, nan da nan bacci ya dauke shi.

(Innalillahi wa innailaihirrajiun, wannan shine kalmar da zamu yi ma matasan wannan zamanin,matasa sun maida biyawa kan su buqata shine mafitar rashin auren su,wanda Allah ba haka yace ba, Annabi Muhammad ba haka yace ba,bin umarnin su kuma wahala yake ma matasa, kuma anjima in wani yace masu basu son Allah da manzon sa ayi ta bala'i dasu, sunace an kafurta su, shin in kana son budurwa ta daga waya ta maka tace my love kazo ina son ganin ka,ba da sauri zaka tafi ba? Umarnin Allah ne zai maka/maki wahala? Allah ya kyauta ya tsarkake mana zuqatan mu).

Abdul ne yaje kiran Sabeer domin su karya yaga dakin shi ba komai, da sauri ya koma ya sanar da umman tasu, aikuwa wayar ta ta dauka ta kira shi,cikin sa'a ya dauka, cikin fadan ta daya zamar mata jiki ta bashi umarnin zuwa yanzu, amsa mata yayi da yana zuwa dama yanzu hakan, ta bashi minti 3, kashe wayar tayi ranta a bace, ko zai tafi a qalla she deserve an explanation.

Kusan minti biyar sannan ya shigo, yara dik suka gaida shi,Aeeshaa ma gaida shi tayi, ta kafe shi fa ido, taga ya rame, idon shi kamar wanda bai bacci ba, shidin ma ita yake kallo, zuciyar shi har wani sauri take wajen bugawa, gaskiya Baba General bai kyauta masa ba, tinda ko ra'ayin yarinyar ba a ji ba, wannan shine isa da mallaka.

"Kai ku tashi ku shiga ciki, zan magana da yayan ku,"

Tashi sukai, har Aeeshaa, sannan ya gyara zaman shi,itama shi take kallo.

"Yanzu abinda kai ka kyauta kenan?"

"Ban kyauta ba Ummana, shi yasa na dawo yau dan na maki bayanin dalili na,"
Chapter 5 · 0% Book details