← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 41

Sashe 39

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan haka Hajja ta samu wasu masu gyaran su je can ayi mata na ta, Ahmad na ta girma abin shi, an gyara masu gidan nasu, dik da ba wani matsala ke gare shi ba, amma an kwashe kayan ciki an kai ma Goggo, tana a'a a'a haka Hajja ta sa dole aka aje mata su, aka Baba Generak ya sauya masu sabbi.

Hadiza ashe baqa ce irin baqinnan mai matuqar kyau da daukan ido, amma ta bata shi da man banza, nan da nan aka dage a kan fuskar ta, sai ga qurage babu, tabo ma va wani sosai ba, dama ita kan ta gwana ce wajen son gyaran, ana yi tana riqe dik wani hadi da akai mata amfani da shi, Hadiza an sha kayan mata anyi tatul, kun san dai mutuniyar taku ba dama.

Dangin Baban ta sun zazzo, musamman talakawan ciki, masu kudin sunqi zuwa wai tayi cikin shege, talakawan ma arziqi suka zo ci, amma a gefe sai zagin su suke, kamar ba a laifi a tuba ma Allah; kai bawa sai ka zagi wanda Allah ya yafe masa in aka hada zunuban ku ma kafishi zunibai, ko ya fika tarin lada, kana nan kana aikin zagin shi.

***********************

Yahhhhhhhhh yau ne ranar da za a fara gudanar da bukukuwan aure.................💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

*A special thanks to my group members, both HAMEE NOVEL, and KUN MAKARO NOVEL GROUP, thank u so much, comments din ku masu dadi ke qaran kwarin guiwa musamman KUN MAKARO GROUP, Allah ya saka ma kowa da alkhairi, Allah ya sa a amfana da abinda aka karanta, MAMU NOVELLA, a very special thanks to u all, Allah ya bar zumunci, godiyata ga dikkan makaranta novels dina wanda na sani da wanda ban sani ba, Allah ya sa a amfana da abin alkhairin da aka ji, sharrin dake ciki Allah ya goge shi a rubutuna da zuqatan bayin shi, Haermeen Haermmaerh na son ku saboda Allah* ❤

Page 30:

Tsayawa fadin yanda bikin mutane shidan nan ya wakana ma a gaskiya bata lokaci ne, domin kuwa wannan dan qaramin page yayi kadan, sai dai zan so mai karatu ya hango irin dukiya da kuma qayatuwar wannan bikin, komai yaji sunan shi.

Hajja itama har irin kwalliyar nan ta zamani sai da akai mata, Baba General kuwa ya dinga tsokanar su Aeeshaa da cewar Hajja ta fisu zama amarya, suje su qara yin kwalliya mai kyau.

Ameerah na maqale da Sabeer, an mata gayu sosai, gashin ta ya sha gyara, saboda yarinya ce mai tsaho da cikar gashi, kowa ya gan su sai yayi sha'awar su, Ahmad kuwa yana riqe a hannun Bilqis, kowa yayi kyau masha'Allah, shirin tafiya dinner ake, wanda daga nan angwaye zasu dau matan su su wuce da su gidajen su, ba wani maganar kai Amarya, Hassana kawai za a kai zuwa Yola, (garin fulani gari mai tarin albarka❤).

Kowa ka gani dauke yake da tsananin farin ciki,Hassana tayi kuka tayi kuka har t gode Allah,kukan farin cikin yau itama an daura auren ta d wanda yake son ta, take son shi, kamar sauran 'yan uwan ta, ashe aure lokaci ne ba wai sanda mutum ya ke son shi yake samu ba, Ammar sai lallashin ta yake, sai tayi shiru, da an gabatar da wani abun a wajen sai idon ta ya ciko da kwalla.

Dik abinnan da ake Hadiza Allah2 take a tashi, wato maganin nan da tasha ne ya fara aiki, sha'awa ce ke mugun dawainiya d ita ba kadan ba,da dai taga kowa sake sabin nishadi yake ba babba ba yaro,ta radawa Khaleefa a kunne, kan ta na ciwo su je gida.

Jimmm yayi yana tinani,yanzu dik idon mutane na kan su sai a neme su a rasa? Gaskiya yanzu ya san meye kunya, ba zai iya fara tashi ba.

A dayan bangaren Sabeer ma ya matsu su bar wajen kunya kawai yake ji, shine abinda ya hana shi tashi da amaryar shi, dan haka sai watsa ido yake ya ga wani daga cikin 'yan gidan su da zai iya cewa su tafi,ba tare da yaji kunya ba.

Baba General shine mutum na qarshe da ke sanar da taron labarin yarintar Khaleefa,Hassana, Sabeer da Aeeshaa, kowa na wajen dariya yake saboda labaran da Baba General ke bayarwa,Khaleefa kunya dik ta kama shi, mutane sai kallon hotunan su suke da suna yara, Sabeer kuwa hankalin shi na kan Aeeshaa da ta dage tana dariya, tare da tausayawa kan ta, ba wasu labarai akan ta masu tsawo, saboda kasancewar bata tashi sosai a cikin su ba.

A qarshe Baba General ya ba ango da amarya damar tafiya gidajen su in suna da ra'ayin tafiya da wuri.

Hadiza ce ta miqe tsaye, duba da yanda mutane ke kallon ta ne yasa ta wayance da kama goshin ta alamar ciwon kai, tare da riqe bayan ta,nan da nan Khaleefa ya tallave ta, sai tausayin ta kuma ya kama mutane, da alama ta gaji ne.

Sabeer na ganin sun tashi shima ya miqe, Ammar da Hassana suka mara masu baya.

Suna fita farfajiyar Hotek din da aka gabatar da event din Sabeer ya daga Aeeshaa har zuwa bakin mota, sai zillo take saboda kunya, amma yaqi sauke ta, murna kawai yake kamar ya gan su a gidan su yake ji.

Hadiza kam tin a mota ta kwanta ma Khaleefa a jiki tana shafa shi, Allah2 take su isa gida, sanin halin mutuniyar tashi ne yasa shi kama hannun ta daya yana murzawa a hankali.

Hassana kuwa gida suka fara komawa, a daren zasu wuce Yola ta jirgi, tare da su Bilqis Hamdiyya Hussaina, da Maman Khaleefa.

Khaleefa na shiga gidan su d ya koma kamar sabo, ga sabon mai gadi, tai saurin maqalewa a jikin Khaleefa, da kyar ya kwaci kan shi, sai ta fashe da kuka.

"Da na san haka maganin mata yake da ban sha ba, dik iskanci na da ban taba shan shi ba, ban san ya ake ji ba, wayyoo Khaleefa dan Allah muyi sauri, kar na mutu."

"Subhanallahi, mutuwa fa? Ahhh ba zaki mutu ba, bari muyi sauri mu gabatar da sallah domin godewa Allah, sannan kar ki manta bamuyi magrib ba ga Isha'i ta yi, ina ga zai fi kyau mu fara gabatarwa ko?"

Kuka ta sake saki, dan kuwa akwai matsala, a mugun matse take, Khaleefa bai biye mata ba wannan karon bayan sallah da nafila harda addu'a ya ma matar shi, ai yana idarwa Hadiza ta dale cinyar shi ta fara kissing din shi, Khaleefa mai tsananin sha'awa, nan da nan ya fara kaebar saqon ta, sai dai wani babban al'amari daya same su, shine,, ga sha'awa sosai, amma gaban Khaleefa yaqi miqewa kamae yanda yake yi da, ya yu rauni.

Sosai Hadiza ta shiga tashin hankali da damuwa, wanda ya sa na kasa gane tsakanin su biyun wa ya fi shiga damuwa?

Da kyar Khaleefa ya samu ya yi harkar nan, qarshe daya samu biyan buqatar shi Hadiza bata samu ba sai romancing din ta yayi ta biya buqata.

Abun ya basu mamaki, amma daga baya daya tina aikin banzan daya yi aikatawa da kan shi yana biyawa kan shi buqata, sai yaji ya cancanci dik wani hukunci da Allah zai saukar masa.

(Biyawa kai buqata na raunana gaban namiji,ko ba jima ko ba dade, a kiyaye,mace kuwa yana buda ta ta rasa budurcin ta wallahi, kunji rantsuwa kenan ta musulmi, sannan yana kawo infection both maza da matan)

"Ka kula da a inda ya faru kuwa? Garin ya haka gaba daya ka kasa komai yanda ya kamata? Innalillahi na shiga uku ni Hadiza, yanzu haka rayuwar mu zata kasance?"

Rungumo ta yayi yana shafa hips din ta.

"Inshaa Allahu ba haka zamu kasance ba, zan nemi magani, bana son na tauye maki haqqin ki ta kowanne fanni,inshaa Allahu zN dage na nemi magani, ki taya ni addu'a,"

Kauda kai tayi tana share hawaye, lallai sun aikata babban kuskure a rayuwar su.

*******************

Koda suka shiga gidan su Sabeer da sauri ya bude mata mota, wannan karon kafin ya dauke ta ita ta maqale masa wuya, aiki cikin doki ya daga ta sama, a bakin qofar shiga parlour ya ajiye ta, ya bude masu qofa, suka shiga, sai da suka zagaye gidan suna kallon tsaruwar shi, sannan suka nufi bedroom, katafaren gadon su Aeesha ta kalla, nan da nan taji wani abu ya tsarga mata,alamar tsoro da fargaba, sakamakon tina baya da tai, da sauri Sabeer ya riqe ta, dan bata san tana ja da baya ba, tana girgiza kai, tare da hawaye.

"Nooo plsss my love ki manta da komai, this is our night, na maki alqawari yau dinnan zangoge maki dik wani memoryn da kk da shi, mai hunting dinki,nai replacing din shi da daddadan memoryn da har abada ba zaki manta shi ba i promise,"

A hankali ya fara zame mata doguwar rigar ta ta da ya kula ta dame ta, a hankali yake zare mata rigar, tare da kissing din kafadar ta, zuwa wuyan ta, Aeeshaa ido ta fara lumshewa, tare da fidda sautin da ya sa Sabeer sake ta a hankali, kar su manta da godewa Allah su maida hankali wajen.......🙊

A tare suka shiga toilete dan tsarkake jikin su da daura alwala, Aeeshaa tayi2 ya fita ta gama ko ta fita ta gama yaqi, sai da sukayi komai a tare.

Bayan idar da sallah, Sabeer ya dafa kan ta ya mata addu'a daga vaya ya musu addu'a, sannan ne ya tina su fa ko yar kazar amarcin nan ba wanda ya siya a cikin su, dariya ya sa ta bishi d kallo, qasan zuciyar ta tana son kasancewa da shi sosai, amma tsoro take ji, kar ta sha azaba kamar na baya.

"Mu fa ko kazar amarci bamu siya ba, yanzu ya kenan?kin yarda mu yi yau...... ko sai na kawo kaza?😉"

Sunne kai tayi dan ta gane me yaje nufi, a hankali ta matsa kusa da shi dan bashi amsar tambayar shi.

Yana ta dariya yaji ta a jikin shi, numfashin ta na taba wuyan shi, juyar da fuskar shi yayi suna fuskantar juna,a hankali sike fuskantar junan su har bakn su ya zama kamar abu guda.
Chapter 39 · 0% Book details