← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 41

Sashe 15

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba adamu ne ya fita d sauri, dan budewa, Aeeshaa kuwa hantar cikin ta ce ta kada, da sauri ta dora qaton hijabin ta akan dinkin atampar data saka, tana zaune tana zare ido tare da cin frtan hannun ta, ko dame zai dawo? Sai Allah.

"Waye kai?

"Ranka shi dade nine sabon mai gadi da Hajja Aeeshaa ta aiko na zauna anan, dan kula da gidan,"

"Dan sa ido dai, ba gadi ba, zo nan,"

Matsawa yayi da mamaki a fuskar shi, kudi Khaleefa ya zaro masu yawa, ya miqa ma Baba Adamu, ya ce yaje ya sallame shi, kar kuma ya koma gidan Hajja ya ja masa surutu, dan ko an dawo da shi ba zai zauna ba, bai son sa ido.

Cike da mamaki da jin takaici yaje ya dau kayan shi ya bar gidan.

Bude qofa yayi, ya fice yana ta tsaki, ya kwashe kayan shi ya shige ciki.

Lokacin ta tada sallah a daki, sai kwala mata kira yake, kamar a wata unguwar take ba a gidan ba.

Daidai ta yi sallama tana qoqarin fita suka hadu, ranshi bace ya ke mata wani irin mugun kallon..............
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

*SAMEERA, Bilkisu mai gado, Ameena,Mero Tsokana😝, Muheebbah,......da dikkan masu comment akan wannan novel thank u, comments din ku na shiga ta da kyau2, yana sa ni jin baku novel din gaba daya😘 One love from Haermeen Haermmaerh❤*

Page 11:

"Me kk yi ina ta kiran ki ba zaki zo ba, ba za kima amsa ba na san kinji ni, raini ne ya shiga tsakanin mu?"

"Yah Khaleefa Allah kar ya nuna min ranar da zan raina ka, sallah nake ban ji ba, kayi hakuri,"

Tsaki ya ja sannan ya qarewa dakin nata kallo, lallai da gaske wadannan tsoffin ke son suyi zaman aure, meye babu a dakin nan? Ga wani qamshi dake tashi na musamman, kallon ta yayi yaga yanda take saka hannu a hijab tana kare qirjin ta kar su dga ya gani, cikin daure fuska ya ce,

"Meye hakan? Meye amfanin rufe qirjin ki d hannu bayan kin dora hijab? To bari kiji, daga yau sai yau, kar na sake ko da wasa na gan ki tare da hijab, in ba fita zaki ba ko sallah kk, kina jina ko,"

Tabbas ya shirya cin zalin ta ne wannan, cikin matse kwallar data taru mata ta daga masa kai alamar taji,

"Baki d baki ko?"

"Ina da shi, naji, inshaa Allahu zan kiyaye.....ga abincin ka can na a shirya maka,"

Banza yayi da ita yana kallon ta yana jiran ta fara bin umarnin shi tin yanzu, gane hakan ne yasa ta sauri cirs hijab din, tana kame2n me zatayi next dan ta bar gaban shi.

Da sauri ta sakada ta gefen shi, tayi hanyar dinning, abincin ta bude ta fara zuba masa, dambun cuscus ne data dafa fari amma ta saka masa kayan lambu da albasa mai yawa, sai tayi miyar dankalin turawa da kayan ciki, sannan ta hada masa fruit salad mai mugun dadi, yaji ayaba, da madara, ga lemon abarba da lemon zaqi da ginger data masa, Khaleefa yaso yayi miskilanci yaqi ci,amma inaaaaa wane shi, abincin kwararru bai isa kauda masa kai ba.

Zama yayi yana wani babbata rai, ya fara cin abincin, wani irin gardi ne yake ji na ratsa shi, dan masifa sai dai yayi fada, kallon ta yayi, yana muzurai,

"Ina ruwa? Ko ahaka zanci ina shaqewa?"

"Yi hakuri ga lemo dana hada maka nan,"

Tsiyaya masa ta fara ya wani daki table din,

"Ruwa na ce maki ba wannan ba, kina gani yana shaqe ni ba zaki yi sauri ba?"

A kidime ta wuce dakko masa ruwa tana hawaye, meye abun fada, ga cuscus nan na ta shigewa, amma dan zalinci sai ya zabure ta haka.

Tana dawowa da ruwa taga jug empty, sai muzurai yake,

"Dakko ruwa ne kawai zai sa ki dade har mutum ya galabaita kisa shi shan abinda bai niyya ba, ke fa kina sani hayaniya, tinda na hadu dake na zama me yawan surutu,ki kiyaye abinda zai sani magana, in ba haka ba ranki zai mummunan ba......"

Wata arniyar gyaza ya sake, alamar qoshi ya tabbatar masa, ita dai bata gama gane komai ba, abincin ba dadi ne? Bai qoshi ba haka ya tura? Kwata2 bata gane komai ba, fatan ta dai ya daina wannan daukan zafin, tinda ba abinda ta masa sai alkhairi.

Tana nan tsaye tana tinani ya wuce ta, wanka ya shiga ya fito, isha'i ake ta kira a unguwar tasu, abinci ta dauka da niyyar kai wa Baba Adamu, ta saka hijabin ta qato har qasa abinci na qasan hijabin, tana fitowa daga kitchen ta gan shi ya dora qafa daya kan daya da remote a hannu, ya sauya wannan tasha ta rawa ya kai wannan ta kida, durqusawa tai kadan tace,

"Yah zan kai ma Baba mai gadi abinci,"

"Na kore shi,"

Zabura tai baya kadan,

"Yes na kore shi, ke zakina buden gate ki rufe, ko da wasa kar naji magana a gida, in an tambaye ki kice tafiya yayi ko na aike shi,"

Hawaye ne ya zubo mata ta gyada kai, tausaya ma Baba Adamu tai, bawan Allah dik inda ya fito a wahale yake, da yunwa, yanzu ya samu wajen da zai huta an kore shi,

"Wai ke kuka baya maki wahala ne? Zo nan aje abincin ki cire hijab din ki zo, sai ki ta kukan ina kalla"

Da hanzari ta hau goge idon ta,

"Bazan sake kuka ba inshaa Allahu, bari na je na ajiye wannan kayu hakuri,"

"F***k kar ki sake ban hakuri, ke wace iriyar yarinya ce wai? Aje hijab nace ki zo nan,"

Bakin ta na rawa da dikkan sassan jikin ta ta aje ta je gaban shi ta durqusa, hannu ya miqa mata ta dade kan ta kama, sai da ya kafe ta da ido kamar zai kashe ta sannan ta kama, janta yayi d qarfi ta fada jikin shi, kamar mai jira kuwa haka ya wurga bakin shi a nata.

Hawaye ne kawai ke zuba mata, sai da Khaleefa ya gama romancing din ta, ya biya buqata da jikin ta, ba tare da ya sadu da ita ba, sannan ya wurga mata tarkacen rigar ta da dik wani abu daya cire a jikin ta,

"Bar nan,"

A guje ta kwashe wasu na faduwa a hanya ta shige daki, tana kuka, kuka take kamar idon ta zai fito,

"Alhamdu lilLAAHi ala kulli halin, Allahumma ajirni fee musibati wa aklifni khairan minha, Allah ka qaramin juriya da hakuri na cinye jarabawar ka, Allah na gode maka daka zabe ni a cikin bayin ka ka.min jarabawa daidai yanda zan dauka, baka dora ma rai abinda bazata iya ba ya kareem,"

Fadin wadannan golden kalamai ba qaramin tasiri sukai ba a ran ta, nan da nan ta nemi quncin ran ta ta rasa, illa zafi da qasan ta ke mata, Khaleefa hannu ya sa mata dik d ya san bata gama warkewa ba, a hankali ta je bandaki ta kunna ruwan zafi ta zauna ciki,tasbihi kawai take a cikin ran ta, ga Allah, dan bata da abin yi, nutsuwa ce sosai ke shigar ta.

(Waman yatawakkal alallahi fa huwa hasbuh)

Wanka tayi ta fita, ta yi sallah, ta kwanta, bayan tayi addu'a ta shafa, ta kashe fitila ta ja bargo, gajiyat zuciya da jiki ta sa bacci mai dadi daukan ta, mafarkai ta dinga yi masu dadi, da faranta rai, ta jima tana baccin nan, taji ana shafa ta, bude ido tayi a hankali saboda nauyin da sukai mata, Khaleefa ne kunnen shi toshe da earpies,sai qaramar waya a kunnen shi, magana yake alamar waya yake yi, kuma magana yake ta batsa, qirjin ta kawai yake matsawa kamar ya samu fura zai dama.

Da hanzari ta janye jikin ta ta kunna fitila, hannun shi daya a gaban shi, earpies a kunnen shi ta gani,

'Ahhh me wannan yake yi haka? Tabdi jam aiko za a yi ta,ba zata hana shi jikin ta ba amma ba zai yu yana waya da wata 'yar iskar ba ita kuma yana son ya sauke buqayar shi akan ta'

Bata rai tayi sosai ta kai qarshen gado, da hannu yake mata nuni ta dawo, kuma ya mata alamar baya son surutu, maqe kafada tai, wani azababben kallo ya watsa mata, jikin ta nan da nan ya dau bari, amma data biye masa gwanda ta gudu waje in yaso ya dake ta in ya gama iskancin nashi.

Waje ta kwasa da gudu, a qasan dinning ta zauna, ta hade jikin ta sosai, Khaleefa ya duba dika dakunan bata ciki, dan haka anan parlour a tsaye ya gama tijarar shi ya shige dakin shi, dik ya bata mata qasan waje.

Toshe bakin ta tayi tana ta kuka, ya ilahi shi bunsuru ne? Baya gajiya da fidda ruwan jikin shi? Watarana zai kashe kan shi kuwa.

A hankali ta rarrafa ta koma dakin ta rufe da key, bacci ta so komawa amma inaaa ba zai samu ba da dikkan alamu, alwala ta dauro ta yi ta nawafil har bacci ya kama ta, sannan ta sallame ta haye gado ta yi baccin.

*******************

Haka rayuwar Khaleefa da Aeeshaa take ta tafiya, sati biyu kenan a dangi qalilan ne suka je mata, burin ta taga qannen ta da Umman ta abokiyar fadan ta, in ta tina da fadan Umman ta sai tayi dariya tace,

"Ummana gwanda fadan ki sau dubunnai akan halin danake ciki yanzu,"

Aeeshaa ta dashe tayi wani irin fari, sai dogon hanci da dan qaramin baki, hips din ta da boobs ne kamar an hura, amma ta zuqe tayi ramin wuya, kamar wadda tai ciwo.

Kwance take tana karanta hadith,dodon nata ya tafi office kuma yace zai dare, ta san bai wuce wajen Rebecca, dan yanzu ta san ta sosai.

Dan haka dole ta jira ko nawan dare zai dawo taje ta bude masa gate.

Horn taji, kamar irin na motar Umman ta, kada kai tayi inaaa ba ita bace, ai da wahala ta zo sai dai ta sa a kawo su Ameena, murmushin yaqe tayi ta gyara kaanciyr ta, horn ta sake ji, da gudu2 cikin saka hope din ganin Umman ta da qannen ta.
Chapter 15 · 0% Book details