← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 41

Sashe 14

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannun shi ta kama ta sakar mashi cizo, tin qarfin ta, da sauri ya sake ta, yana yarfe hannu, diba tai a guje zata fita, ya sa qafa ya yarfar d ita a qasa, faduwa tai tare da sake qarar azaba, ta gaji matuqa, qoqin rashi take ya bi ta ya kwanta a jikin ta, shi kan shi ya gaji, bai zaci tana da qarfi haka ba.

Mutsu2 take dan ya daga ta ta gudu, amma da ta san me xai haifar da batai ba, domin dik albarkatun qirjin ta ke taba nashi, nan da nan kuwa jarabar shi ta dawo dabuwa.....

Qarfe 4:01am, Khaleefa ne kwance a gefen Aeeshaa, wadda ajiyar zuciya kawai take,tana tsiyayar d hawaye ta gefen idon ta, sama take kallo, ido bude, bata gane komai a saman, ji take kamar ba a duniyar take ba.

Qasanta kamar an sa abu mai kaifi an yanka haka take ji, ko hannun ta bt iya dagawa,b binda ke mat yawo akai,illa yndaya dinga saduwa d ita kamar ba zai barta d rai ba, ga shi yana yi ya na sauya maimaita film din da yake kallo, ba addu'a, ba komai daya danganci sunnah, sai kace arna.

Kuka mai qarfi ta fashe da shi, mara sauti, saboda muryar ta ma bata fita, ta dade tana kuka, ko motsawa bai ba, dan tini bacci ya share shi

Yunquri ta dinga yi dan tashi amma ta kasa, ko dukan da ya mata ma da ta qi tsayawa ai ya isa sa jikin ta tsami, fuskar ta har kumbura tayi saboda marin data sha, wai ace musulmi ne ke saduwa da mace yana kallon wannan iskancin, remote ta qoqarta ta janyo daga hannun shi, kashe wa tai gaba daya, tare da sakin tsaki,

"Yan iska kawai, Allah sai ya sakamin ba zan taba yafe maku ba dikan ku,"😭😭😭😭

Juyi yayi ya ringumo ta, ya ci gaba da baccin shi, hawayen baqin ciki da tsana mai tsanani ne suke zubar mata a idon ta, ashe Yah Khaleefa tantiri ne haka?

Kiran sallah take taji a kunnen ta, ba halin tashi,har ta gaji d kukan ma, sai sake ajiyar zuciya take.

Tana ji tana gani aka gama sallah ta kasa tashi, daga baya ma bacci ne mai nauyi ya dauke ta, ga gajiyar biki, ga ta Khaleefa.

8:00am ya farka, saboda alarm da ya saka a wayar shi, kullum in 8 tayi sai ya buga saboda koda ya makara ya tada shi, a hanzarce ya tashi yayi wanka, ya shirya, zai fita ya kalle ta, yaji wani irin abu ya tsarga masa a jikin shi, na tsantsar gamsuwa da yayi d ita a daren jiyan, kada kai yayi tare da shafar cinyar ta.

"Zamu je dake, kina da zaqi sosai,"

Farkawa tai, suna ido hudu ta zabura tana kare qirjin ta, ido tsilli2 take kallon shi cike da hawaye, tana kada masa kai.

"Calm down babes, ba yanzu ba, ki jinyata min kan ki, naga waje, sai na dawo,"

Ficewa yayi ba tare dayaji me zata ce ba, kamar mutumin kirki, manyan kaya ya saka, wanda suka karbi cikakken halittar jikin shi mai kyau, ka rantse dan gidan limamin makka ne, a nutse ya durqusa gaban ta, dan bai taba zaton zata zo da sassafen nan ba.

"Hajja ke ce da asussuban nan?"

Baki ta bude daga baya ta wara hannayen ta alamar daquwa.

"Amshi naka, nace amshi naka, maras kunya, yanzu ka duba agogon hannun ka kuwa? Tara na safiya yanzu, ga abinci can na sa an dafo maku, ina Aeeshaan take?"

Cikin alamar wai yaji kunya, ya shafa kan shi, ya nuna mata hanyar dakin, murmushi Hajja tayi, da dikkan alamu, an yi nasarar gamuwa😉, kuma yanda fuskar shi take dauke da annashuwa ya samu abinda ake nema kowacca diya mace ta kai gidan auren ta.

Miqewa tai cikin kuzari irin nata,dan ita sam badan fatar ta data fara nuna alamar ta kwan biyu ba ba zata ce mata tsahuwa ba.

Har ta kusan isa dakin ya yi wani sufa sai gashi a qofar dakin, hannu ya daga mata, ya bude qofar ya shige da gudu ya tattara disc din dake qasan dakin, ya tura qasan gadon, ya daga dik wani abun iskancin shi, sannan ya fice.

Hajja dai qara murmusawa ake, jikar ta ta kai budurci gidan aure lfy, lallai Khadeeja an gaishe ta, ta yi qoqari, dik wani haushin ta da Hajja ke ji sai taji ya kau.

Aeeshaa dai na bakin gado, tana zare ido, kan ta ya daure, meye hakan ke nufi? Ko wani abun ya gani zai gudu ya barta, kuka ta fara, ta ja jiki da kyar xata tashi, da hanzari hajja ta tare ta, tana jera mata sannu.

Zubewa tai a jikin Hajja tana kuka kamar wadda akai wa sabuwar mutuwa, sai kuka take tana gwana numfashi.

Tsam hajja ta rungume ta tana matsar kwalla itama, tare da zagin Khaleefa a ran ta, na rashin tausayin marainiyar Allah da bai ba, da dikkan alama ta mai gardama ya hada mata da duka, bai la'akari da sabuntar ta ba.

"Sannu Aeeshaa, Allah ya shiryi Khaleefa ya yi hankali, shi ko dan lallashin nan babu, ji fuskar ki kamar an gasa biredin saba'in, ta tashi tai luhu2, wannan dan iskan yaron da bai fita ba sai na ci mai uba, Allah ya saka maki, muje na gasa maki jiki, jikina ya bani ba mutunci ne da shi ba sai kin wahala shi yasa na taho d kaina, tinda ba wanda zan aiko, Hussai ta koma ita da Hamdiyya, Balqis ba zata iya ba tayi nauyi, zata zauna har dai ta haihu, muje kar na cika ki da surutu"

"Hahhhaajjjaa kkkooo salllaaahh bann baa faa"

Sai ta fashe da kuka.

"Yi hakuri muje na tayaki ki gyara sai ki wanka kiyi sallar, Allah saka maki mugu azzalimi kawai,"

Ruwan zafi tin tana kuka in ta shiga,har sai da taji kamar kar ta fita ma, wankan tsarki tayi kamar yanda aka koyar d su a islamiyya, sannan ta fito.

(Yana da matuqar mahimmanci malaman manyan aji na islamiyya suna koyar da mata harda mazan ma yanda ake gudanar da rayuwar aure a musulunce, in ma ba a koya masu anan ba yahudawa da nasara zasu koya masu, ta haka ake samun lalatattun yara, kuma namiji dik gurman shi yayi aure bai san farillan daya kamata ya hau kan shi ba balle sunnoni, ayi aure namiji ya hau mace kamar awaki, ba nafila ba addu'a ba komai, saboda islamiyya ba a koya masa ba, iyayen shi ba su koya masa ba, wai ai mace kawai ake koyawa, to wasu matan ma ba a koya masu komai, akwai wanda wallahi iyayen su ne suke koyar da su komai na xaman aure kafin auren, har yanda zasu magana da tafiya gaban matan su, amma wasu wai kunya, gaskiya a daina kunya a inda bai kamata ba)

Kaya ta tarar Hajja ta debo mata marasa nauyi, doguwar riga ce da bra da pant sai dankwalin kayan da hijab.

"Bazan sallah anan ba Hajja muje can,"

Da kyar Hajja ta gane me ta fada, ta yi tsananin tausaya ma Aeeshaa, roqon ta Allah ya sa khaleefa ya dawo; sai ta masa dukan tsiya (kar dai ki ji ma kan ki ciwo yar tsohuwa).

Bayan tayi sallah, ta tsaya yin azkar, tana yi tana kuka, ita nata daren farkon a haka yazo mata, gaba kuma bata san wacce irin rayuwa za tai ba da Khaleefa.

Hajja ce ta leqo tagan ta, zama tayi a bakin gadon, ta yi ta mata nasiha.

"Ba a yi ma miji musu, sai dai in ya umarce ki da aikata sabon Allah, wannan kuwa ko kashe ki za ai kar ki biye masa, amma in ba sabon Allah bane ba a yiwa miji musu, yanzu dibi fuskar ki? Wannan cin zali d mi yayi kama?"

Hajja sai d ta tabbatar Aeeshaa ta ci abinci, ta qoshi, ta yi bacci ta huta sosai, sannan sukai azahar ta wuce gida.

Tana wucewa Aeeshaa taje dakin Khaleefa ta kwashe kayan baccin ta tsaf da komai nata da aka aje mata acan, ko wanne me neman maganan ne a cikin tayun nata ya aje mata kaya a dakin shi oho.

Tinani tayi, ya kamata ta sake dafa masa wani abi tinda akwai kayan abinci, wanda aka kawo ya jima aje, ga shi bata ko san lokacin da zai dawo ba.

'Ohhh ni Aeeshaa nan kuma Allah ya kawo ni, Allah ka dafa min kar ka barni d kaina😢 ba zan iya ba'

Sai fa tayi la'asar ta fara girki mai rai d lafiya ta gama, ta sake qalqale wajen, dan ba wani datti bane akwai, tana zaune taji ana buga gidan, hijab din ta babba ta zuba taje ta bude.

Wani dattijo ta gani, yaja ganin ta ya durqusa a qasa, yana kwasar gaisuwa, ai d sauri itama ta duqa, bata san ko wane ba, ba a mata tarbiyyar babba ya gaida ta ba har da durquso.

"Baba ban san kai wane ba, amma koma waye kai dan Allah ka tashi, ka daina duqa min"

Dan miqewa yayi kadan, ya tsaya a gefe, kamar akwai wanda yake jira.

Drivern gidan Hajja ne ya leqo suka gaisa da Aeeshaa sannan ya mata bayanin mai gadin su kenan,

"Ok Allah sarki, dazu munyi maganar kuwa, bismillah baba muje daga ciki, sai dai mai gidan baya nan, ka shiga ka zauna ka huta zan kawo maka abinci, kafin ya dawo, sai ku yi magana,"

"Allah ya miki albarka hajiya na gode, suna na Adamu, Allah ya bani ikon yin abinda ya kawo ni,"

"Ameen Baba dan Allah kar kana kirana hajiya, Aeeshaa sunana,"

Driver sallama ya musu, a kullum shi dai yana yaba tarbiyya irin ta Aeeshaa.

Baba Adamu dakin data nuna masa ya shige ya aje yar ledar kayan shi, yana ta kallon wajen, yana godewa Allah, an sha gwagwarmayar rayuwa, yanzu ga gida harda katifa makekiya, ga wata kujera da ledar daki, ga bandaki ai shi kam sai godiya.

Abinci ta kawo masa da ruwa, ya ci ya kwanta baccin gajiya.

Daf d magrib Khaleefa ya dawo, ya maka horn kamar shi kadai ne mai mota a unguwar.
Chapter 14 · 0% Book details