← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 41

Sashe 27

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ta sauka an samu mace, in kinga dama kizo ko ki zauna, muna nan muna dik abinda ya dace uwa tayi, "

"Hajja dan Allah kiyi hakuri ina nan tafe in kun koma gida,"

"Kar ma kizo ki zaman ki,"

Kashe wayar tai tana ta mita, Baba General ya san an tabo masa mata, ya fi kowa sanin a wannan yanayin ya yi shiru ya mata biyayya shi yafi masa alkhairi.

************************

Khaleefa daya koma gida,kwanciyar shi yayi ya na baccin rana, ko a jikin shi, dan an hana shi daukan yarinya ai dama shi bai so aka haife ta bama, suje suyi ta dawainiya su suka ga zasu iya.

Bai farka ba sai wajen magrib, qamshin abinci yaji, kawai sai Aeeshaa ta fado masa a rai,

'Amma wannan ba irin girkin ta bane, girkin ta ai tada shi zai a barci tsabar dadin qamshin shi, and ta haihu ya za ai tazo yi masa girki'

Sauka yayi a gadon yana murje idon shi, daga shi sai boxer, dan shi yana son zama haka, tafe yake kamar baccin bai ishe shi ba, ganin ta yayi a tsaye a bakin qofar shiga dakin, sanye da rigar shi, ta riqe ludayin motsa miya, ba ko dogon wando, ta daurs gashin ta data qara a bayan kan ta, tana wani rausaya.

"Hadiza? Yaushe kk zo? Me kk yi haka? In wani ya shigo ya gan ki a haka fa?"

"Sai kace masu amaryar ka ce ni?"

Dan dariya yayi ta baki da hankali ya shige toilete, ita kuwa dadi ne ya kashe ta tayi tsalle ta fada gado, tana wurwurga qafa tana murna, ita a dole Khaleefa yaji dadi tace ita amaryar shi ce.

Bayan ya fito ta kammala shirya abinci, suka zauna suka ci,shidai kwata2 ba zai ce ba dadi ba, ba kuma zai yaba ba, sai jira take taji ya yaba, taji shiru, dake 'yar variki ce sai cewa tai,

"Gaba daya yau banji dadin abincin nan ba, banga maggi ba, haka nayi shi inajin shi yasa bai dadi ba sosai,"

Khaleefa a ran shi yace

'Gaskiya mana abu ba wani dadi haka, ai na zaci iyakar kwarewar ki kenan'

"Ayyaa aiko yn nan baki kula bane, ba laifi ai za a iya ci haka,"

Kada ido tayi

"Dan ma renon Goggo ce,kasan tsoffin da suna girki ba maggi kuma yayi dadi,"

"Haka ne kam, kamar yanda kk da dadin ba,"

Anzo wajen, nan da nan ta washe baki, sauri2 suka gama ci, ko kwashe plates ba ta san tai ba, sai shi ya fara kwashewa dan vaya son datti, yana shiga yaga kitchen kaca2 a aiki daya ta maida shi kamar an dade ana aiki ba gyara, ledojin maggi ya gani, kawai ya kada kai, maggi an tafka shi an gode Allah, ko a zaton ta maggi shije girki oho?

Gyara wajen ya fara tana taya shi, ita fa bata son aiki sam, haka suka kammala, a kitchen din ta dafe shi,nan da nan suka fara aikin na su na rashin mafadi,Khaleefa Aeeshaa kawai yake hangowa, inama zata zama romantic haka, ai da ita zai wannan lamari a kitchen, haka dai sukai ta sabawa Allah hankalin su kwance.

**********************

Ranar suna, yarinya an rada mata suna Khadeeja, suna kiran ta da Ameerah, Umma kam ta aje kunya a gefe, dan ba dan Adam din da zai dora idon shi ya kalli Ameerah ba ta kwanta mashi a rai ba, ba dan wai tsananin kyau ba, kawai haka Allah ya yi ta, har wanka Umma ke yi mata, sai dai a idon mutane ba ruwan ta da Aeeshaa balle wata Ameerah, da an ragu zata dauke ta tayi wajen su Sabeer ta mata wanka, ta gyara ta, taba Hassana ta maida ta ciki.

Yau su Hamdiyya, Bilqis,da Hussaina zasu koma gidajen su, bayan sun cika qanwar tasu da abubuwan gyara dan taimaka mata ta dawo kamar sabuwar amarya, sun gama shiri tsaf sun ma kowa sallama, zasu tafi Hajja ta fito dan yu masu sallama, Aeeshaa na dauke da Ameerah, sai daga masu hannu take kamar kar su tafi.

*********************

Dare ya yi, Khaleefa ya kasa samun nutsuwar dayake nema, Hajja ta hana Aeeshaa daukan wayar shi, ko a jikin ta, da ta samu hutu itama da jarabar shi,IG ta shiga tana kallon pictures, suna ta gani farkon kamar Hadiza, kuma an qarshen kamar wani yare daban, amma ga hoton Hadiza nan a jiki.

Dannawa tayi ta shiga, sai duba picture take, hotuna ne masu mugun kyau, kamar ba Hadizan data sani ba, kayan dake jikin ta kwata2 ma ita bata taba ganin ta da su ba, kaya ne masu tsada, daga jaka har tufafin da takalmi zuwa agogo, to ko dai kama ce ba Hadizan data sani bace, gidan. Ma da akai hotunan bata gane ko daya ba, dan ba gidan su bane, wani vedio da Hadizan tayi ta qawata shi da flowers dan kar a gane inda take ne ya tabbatar wa da Aeeshaa tabbas Hadiza ce, dan a parlourn ta akai vedion, sai hotuna da ta dauka a dai2 dinning table, kuma da alama wannan rigar ta Khaleefa ce ga hular shi nan akan Hadiza,tana wani karairaya, tana fadin ta kusan yin aure masoyan ta su sanya mata albarka, nan ba da jimawa ba zata turo masu hoton mijin da zata aura.

'Ikon Allah, amma wannan parlourn kamar nawa, kuma rigar Yah Khaleefa ce na ke gani, da hular shi, sai ta dan yafa mayafi'

Dubawa tayi taga post din ya kai kusan sati daya.

Shiru dai tayi tana nazari, can zuciyar ta ta dinga saqa mata

'In ma Hadiza shi zata aura ko a jikina sun dace, suje su qarata, balle ma ta san ba shi Hadiza ke nufi va'

Dubawa tayi taga yana online, taso ta masa magana amma sai taqi, kawai sai ta saka hoton Ameerah a status, da Dp, sai ta rubuta, (Allah ya albarkaci rayuwar ki my baby Khadeeja, AKA Ameerah)

Yana hawa, Khaleefa shi ya fara gani, murmushu tayi, tace

"Kai da Hajja taurin kan ku daya, tinda ta kore ka kaqi dawowa, itama taqi neman ka,na tabbata ko sunan yarinyar baka sani ba,ta kuma hana kowa ya neme ka, ni dai ina gida ina hutawa ta abuna, ko a jikina,"

"Sunan ta kenan? Allah ya raya maki ita,gata kyakkyawa kuwa,"

"Ameen na gd,"

"Turon hoton ta,"

"No"

"Why?"

"Saboda tawa ce ni kadai,"

"Ohhhh"

"Yehhhhh"

Sauka tai online,ranta bai mata dadi ba, wai kenan yana nufin har yanzu bai amshe ta a matsayin diyar dayake so ba, ita kadai ta mallake ta, ba komai, ta ji ta yarda, muje zuwa, zako kaga rashin M, dan kuwa komai Hajja ta yanke kan ka kai ka sani.

Shi kuwa sai maimaita kallon hoton Yarinyar yake, sabods ba laifi ta masa kyau,

Sake hawa Aeeshaa tayi, tayi ta saka hotunan su na suna, wanda tayi kyau sosai, ai da wani bacin rai Khaleefa ya mata audi,

"Kina hauka kk saka hotunan ki haka? Gaba daya qirjin ki ya fito, dalla malama ki cire kafin ran ki ya baci,"

"Kar ka damu muna da Omon wanke wa koda baka siyo ka kawo mana ba,"

'Wayyooo ina yiwa mijina rashin kunya, na shiga uku'

"Baki da mutunci dama, ni kk fadawa baqar magana haka, ki jira gobe kiga abinda zan maki,"

"Allah ya kaimu, xan so ganin me zaka iya aikatawa ina gaban Hajja gatana,😂😜😜"

Abun ma dariya ya koma bata, haka sukai ta Chatting da audio yana mata masifa tana kunna shi tana bashi haushi, daya kula bata masa rai kawai take son tayi sai ya sauka onlinem

"Xaman yarinyar nan a gidan hajja ya zo qarshe, Hajja ke koya mata dik wani walaqancin da zatamin, yarinya mai nutsuwa da kamun kai, komai na aikata sai dai ta ban hakuri, ita ce ke fadi in fada yau, inaaa koya mata akai, Allah ya kaimu gobe,"

"Ahhh Ummu ameerah baki bacci ba?"

"Auntyyy🙈 eh ban yi ba,"

"Yah diyata?"

"Tana lfy, ya nawa babyn? Hope kuna lfy?"

"Lfy qlou, bari gobe zan bada no ki wajen wata qawata Haermeebraerh ta samin ke a group din ta, zaki qara samun wayewa akan zaman aure inshaa Allahu, na san baki wani group dan qauyancin ki yawa ne da shi Aeeshaa,"

"Hhhhhhh aiko Adda Bilqis na gode sosai,sai d safe, ki kwana lfy,ina gaida yarona,"

"Allah ya kaimu, ki shafan kan babyna,"

Sallama sukai, a cikin daren Bilqis ta turawa Haermeebraerh no Aeeshaa, cikin sa'a kuwa tana online, nan da nan tayi adding din ta.

Aeeshaa tai sallama ta gabatr da kan ta, nan mutanen dake kusa suka amsa mata daga nan ta yi shiru ta nutsu tana kallon yanda ake shan hira a gidan, tin daga nan ta fara gane halayen mutane kala2 a duniya, kowa da irin halin shi, ita a rayuwar ta banda iyalin ta bata taba intermingling da wasu mutanen ba.

Washegari kuwa da ta tashi da sassafe ta duba sai taga hira har ta kasa bi, saboda yawa,

'To su kwana suke hira ne? Bari zan tambayi Adda Bilqis naji mutanen nan akwai surutu'

('Yan group din Haermeebrah basu surutun banza malamar su komai aka ce mai amfani ne😚🙄ba laifi wasu har gudu suke wai hira tayi yawa🤣🤣🤣🤣)

********************

Wasa2 Aeeshaa tayi wata biyu kenan a gida, amma Khaleefa zuwan shi uku, Hajja na kora shi,daga baya yace ba zai sake zuwa ba, dama yana zuwa ne dan Baban shi dake masa fada akan yazo ya bada hakuri banda haka sho me zai kawo shi, Hajja na nan tana qara bincike akan shi.

Wata ranar asabar da Aeeshaa ba zata taba mantawa da ita ba, da safe, ta hau IG, kawai tana duba picture, sai ta shiga inda taga hotunan Hadiza kwanaki, tana shiga tai ta kallon rubutu da hotunan flower masu kyau, tana kalaman soyayya, sai da ta duba pictures wajen guda biyar sannan tayi gamo da hoton daya birkita mata lissafi,hankalin ta ya tashi, tana maimaita kallon hoton dan tabbatar da anya gaskiya ne Hajja ta banko qofa cikin rudani itama, dauke da wasu takardu masu kama da hotuna a hannun ta................

*Annnnngamuuuu bammmmm* 👏🏼👏🏼
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

Page 20:
Chapter 27 · 0% Book details