← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 41

Sashe 10

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Qunquni yake,amma General yaji shi tsaf, Khaleefa bai aune ba bai san daga ina hannun ya biyo ba yaji wani makakken mari a kuncin shi na hagu,gabadaya parlourn sai da ya dauka, Aeeshaa da ta shigo dan komawa daki qamewa tayi, jikar tsohon soja kenan, hannun ta a rufe da bakin ta,cikin ta ne ya bada wata irin qara mai sauti, da sauri ta bar wajen,ta shige daki.

"KAII KHALEEFA kar kaga ina daga maka qafa, ina bin ka da lalama, dik wani qunci da baqin hali da rashin kunya tare da qin 'yan uwan ka da kk akan idona yake, rashin kunyar ka har ta kai ina magana kana man qunquni, kuma kana yi wato yanda zanji sabida baka da kunya ko? To ka sani daga yau sai yau, in na sake ganin rashin da'a a tare da kai ba a gabana ba ko a gaban waye sai na mummunan saba maka, tashi ka ban waje, kuma kar ka sake ka fita ko ina, gobe auren ka, mara mutunci kawai,"

Khaleefa wanda bakin shi yake a sake, dan mamaki, da tsoron ganin yanayi Baba General wanda tinda yake bai taba ganin bacin rai irin haka a fuskar shi ba, da saurin gaske ya zuba guiwowin shi a qasa yana bama Baba General hakuri,da kyar ya hakura dai da Hajja ta fito ta sake bashi hakuri sannan ya hakura.

Abu dayane a ran Khaleefa yanzu; fansar marin nan, akan Aeeshaa zata fada, tinda ta ga sanda aka mare shi, kuma a sanadin auren aka mare shi, dan haka ya ma matsu a daura masu auren............

*Mugu ta Allah ba taka ba to*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

Page 6:

A duqe take kan guiwowin ta, idon ta a rufe, bakin ta na rawa, hawaye face2 a fuskar ta, dik wanda ya gan ta zai zaci gamo tayi d fatalwa, ko aljanu, tsabar tsoron dake kan fuskar ta, babu wanda bai san iskanci ba, tabbas Khaleefa kura ce a cikin fatar rago, ba qaramin dan basaja bane, a zaton da take masa, tsabar nagartar shi da kirkin shine yasa baya son hayaniya, tsoron Allah ne yasa baya son kula matan da ba muharraman shi ba, sannan yana tsoron Allah ne akan kalaman shi kar ya fadi sabon Allah shi yake hana shi yawan magana, ashe yana boye mugayen halayen shi ne.

Gani tayi ya gogr hannun shi da tissue ya tako inda take, d sauri ta fara qoqarin tashi ta gudu, amma santsin qasan wajen da yanayin rigar da tasa mai santsi sai zamewa take, Allah2 take wani ya shigo saboda ihun da tai,amma shiru, matsalar irin gidajen nan masu manyan qofofi kenan,Maman su na can parlour, zai wahala taji tinda babban parlour ne, qara zata sake saki, kafin ta kwalla ya damqe mata baki.

Magana yake son yayi, amma bai ma san ta ina zai fara ba, cikin zare ido, da tsoratar da ita ya fara magana,

"Abinda kk gani ya tsaya a tsakanin mu,in kuma kina ganin ba zai tsaya a tsakanin mu ba sai kin fada ma wani,ni ba zan hana ki ba, tinda ba tare dake nake yawo ba, amma ki kuka da kan ki, dik abinda ya same ki, da mahaifiyar ki dda qannen ki, je ki zaki iya tafiya, ba zan iya dogon surutu ba,"

Tsoron shi ne mai tsanani a tare da ita, kuma shima ya fuskanci hakan, dan haka ya qara daure fuska, ya nuna mata bai damu ba, in taga zata iya risking rayuwar ahalin ta, cikin sauri ta qoqarta fita, da sauri ya bi bayan ta ya fixgo ta,

"Me ma ya kawo ki waje na, bayan kin gaishe ni ban amsa ba shine dan naci sai kin biyo ni,"

Bakin ta na rawa sosai ta furta,

"Baaabbbaa Geeegggeneral keee kiran ka,"

"Shit ! Me zan yiwa tsohon nan ne? Ya qaqaban auren da ban so, ya sani zullumi da zancen nake kwana nake tashi, kiran na meye yanzu kuma, me kk ji yana magana akai?"

"Baan san ni ba nima,"

"To goge idon ki, kuma ki nutsu, kafin ki jawon magana wajen tsohon can, dan na kula bai hada ki da kowa ba, "

Da saurin ta kuwa ta fara gyara fuskar ta, da dikkan wani abu da ke buqatar gyara a jikin ta, yaji dadin yanda take tsoron shi, hakan zai bashi damar yin abinda ya so kenan, da kyau.

Komawa ciki yayi, dan bai isa fita a haka ba, dole sai ya dan watsa ruwa, ita kuwa data fita a parlourn shi, bata ga kowa ba, ta godewa Allah, dan bata son wani ya tambaye ta me ya faru.

Tap din flowers ta nufa,ta kunna tana ta watsawa fuskar ta ruwa, tana koka me ta gani, wannan abu ba zai taba barin kan ta ya huta ba, bata san sanda zata daina hango wannan mummunan gamon ba,wataqila sai bayan ran ta, bai kula da ita ba sanda ya wuce, tana ganin shi ta manne jikin queen of the night dake shuke a kusa da wajen da take saye, har sai da ya wuce, qamshin turaren shi mai sanyi da dadi ta shaqa, dazu kafin suyi mummuna gamon nan, ta yaba da qamshin, amma yanzu qarni da wari yake mata, da sauri ta sake splashing ruwa a fuskar ta, ta shaqi iskar wajen, idon ta rufe, sai da taji hankalin ta ya kwanta sannan ta fara komawa ciki.

"Tinda gata ta zo kawai ku fara komai na shirye2n bikin, ni me zance, yarinyar da na ninka shekarun ta amma wai ita kuke son hada ni da ita, in ma nace bana so baji zakuyi ba, ko ra'yin ta na tabbata bakuji ba, shekara nawa a tsakani, tin tana aji biyar baku nemi ra'ayina ba sai yanzu da lokaci ya qure,"

"Bamu kira ka dan ka mana rashin kunya ba tijararre, tinda kai ba a fara abin arziqi da kai bai koma na tsiya ba, da kai da Aeeshaa dika mallakin mune, zamu iya zaba maku wanda muka so, ko sisin ka bamu buqata, zamu aura maka ita, za kuma akai ma ka ita gidan baban ka na kabuga, in kaga dama in an kaita kar kaje gidan, kace ba ka auren, tashi ka bar mana nan dan iskan yaro kawai,"

Hajja ke shafa hannun General a hankali, saboda yanda ta kula ranshi ya baci matuqa, cikin rashin kunya ya miqe zai fice, Aeeshaa da taji dik abinda ke faruwa ce ta shigo, idon ta na tsiyayar da hawaye, ta durqusa a gaban General da ke cikin matsanancin fushi.

"Baba General ka taimaka min kar ku auramin wannan fasiqin, kar ku hada aurena da shi yafi qarfina ba zan iya auren shi ba, dan Allah kar ku jefa rayuwata cikin halaka, na sani tin tasowa ta ba wanda ya damu dani, ba wanda yake jin me nake so, ko meye vana so, dik abinda aka so yankewa ake akaina, na tabbata in mahaifina na nan zai tsaya min, dan.....

Wani gigitaccen mari taji ya sauka a kuncin ta, tana juyawa ta ga Umman ta tsaye,

"Lallai wuyan ki yayi kaurin da har zaki sa iyayena a gaba kina aibata jikan su a gaban idon su, wato tarbiyyar da na maki kk son nuna masu ko? Sai ki bi mahaifin naki shi da ya fimu son ki ya tafi ya barki bai tafi da ke ba,mara mutunci, durqusa ki basu hakuri,har Khaleefa din,"

Khaleefa na jin haka ya sa kai ya fice, dan shi wannan drama ba da shi ba, sun dade basu aura masa itan ba, ko kuma sun dade ba su fasa bashi ita ba, dik dayane a wajen shi, bakin ta na rawa ta fara bawa kakannin nata hakurin abinda ta aikata, zuciyar ta kamar ta fito waje, ji take da ta san Yayan mahaifin ta a Katsin ina yake can zata gudu.

"Khadeeja bai kamata ki saurin dukan ta ba, ra'ayin ta take fada, amma Aeeshaa ina son ki gane, ita mace budurwa iyayen ta ke zaba mata mijin aure, bazawara ita ke da 'yancin zabar miji, dan haka ki hakuri da zabin General, inshaa Allahu ba za ki dana sani ba, maza jeki, ki yi alwala magrib tayi, Allah ya sanya maku albarka,ya kare dikkan abin qi,"

Cikin rangaji irin na mayen damuwa take takawa, zuwa dakin, Umman ta ta bita da kallon tausayawa a cikin zuciyar ta, ta sani bata kyauta ba,amma ba zata iya jayayya da mahaifan ta ba,ba su mata wannan tarbiyyar ba,dole ne diyar ta itama ta zama mai biyayya.

General ne ya tashi dan zuwa masjid, yau Khaleefa bai je ba, Sabeer kawai ya gani, ya kada kai, wato dan an masa fada shi yasa yayi fushi har da sallar ma,Allah ya shirya.

Har Umma ta tafi bata nemi ganin Aeeshaa ba, dama Aeeshan ta san za ai hakan, bata sa a ka ba, dan haka tana idar da sallah ta haye gado ta nade cikin bargo, saboda ciwon kan dake damun ta, Hajja ce ta shigo dauke da mug, ta hada mata shayi mai kauri, da kuma plate dauke da faten dankalin turawa, wanda ya sha kayan lambu, da kayan ciki.

"Tashi kici wannan ki sha magani sai ki kwanta, kin yi sallar isha'i ko?"

Daga kai tayi,sannan ta fara sauka,ta daukar wa kan ta alqawari bazata sake ma kowa musu ba har qarshen rayuwar ta,sai dai in abin da ya sabawa Allah ne, shi kadai ne ba zatai ba, ta kula rayuwar ta bata da amfani a cikin iyalin ta,abinda suke so shi suke mata, koda kuwa shine abu na qarshe da ta tsana a rayuwar ta, ba ruwan su.

Abinci ta fara ci, Hajja na kallon ta da tausayawa, bayan ta gama ta sha maganin ta koma zata kwanta, Hajja ta riqo ta, ta jingina ta da jikin ta.
Chapter 10 · 0% Book details