← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 41

Sashe 2

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Barka da zuwa Yayanmu, saukar yaushe? Shine ko ka sanar dani,na maka kyakkyawar tarba da girkina me tsinka kunne ko?"

"Wowww, har yaushe kk girma? Yaushe2 ma daina daukan ki muna zuwa gidan Hajja dake? Yaushe2 ne na daina....."

"Yayaaa plsss ya isa haka, kana ganin wannan mara kunyar har ya fara dariya,"

"Dan Allah muje ciki, na gaji da tsaiwa, dan na kula in aka barku nan sai ku kwana hira,"

Hanya suka bama Umman nasu ta shige, sannan suma.suka shiga suna ci gaba da hira tare da murnar dawowar yayan nasu, wanda yake dan Yayan umman su ne, amma anan gidan ya tashi, hasalima shi ke kiran Umman nasu da suna Umma har sika tashi da hakan suma.

Kulle dakin ta tayi, ta sauya kayan ta, har zata fita, ta tsaya, gani nai ta koma ta dakko mayafi mara girma sosai, ta yafa, sannan ta fita, (dan ta tina cewar yanzu ba su kadai bane akwai wanda ba muharramin ta ba a gidan).

Kamar yanda ta saba, girki taje ta dora, ta koma suka ci gaba da hirar su,yana basu labarin karatun nashi daya je na koyon tuqa jirgin sama, Abdul dik sha'awar tuqa jirgi ta gama kashe shi, tambaya kan tambaya, ita kuwa Aeeshaa abun bai wani bata sha'awa wai tuqa jirgi, ita taso ace aikin asibiti yayi,ko dan sanda ko soja, dan su take son namiji ya zama yana yi, amma ba wani abu wai shi tuqa jirgi ba,

"Qanwata ya dai naji kin bata shiru?"

"Ammm ba komai, dama ina tinanin kamar abincin nan yayi bari naje na duba,"

"Yes dear pls go, yunwa nake ji sosai,"

Dariya sukai dika ta tashi, ya bi bayan ta da kallo, yana mamakin saurin girman da tayi, kamar ba yar shekara sha shida ba,komai na jikin ta sai dai masha'Allah.

Bayan sun kammala cin abinci har Umman nasu, ya masu tayin raka shi zuwa gidan Hajja dan acan gidan iyayen shi yake.

"Yehhhhh Yah Sabeer zani, na dade ban je ba dama"

"Nima zani,"

"Ina zaki? Ke qaramar yarinya ce? Ki zauna ga dakina nan jiya ko sharar yamma baki min ba, ga gidan nan kaca2 in muka je dake wa zai gyara?"

"Au Umma kema zaki?"

"Zani mana Ameena, nida gidan mu? Ku kuka je balle ni?"

Sauke kan ta tayi, ta miqe ta bar wajen dan tana buqatar zama ita daya, ta koka abinda ke ran ta, in aka mata abu in bata koka ba wani irin baqin ciki ke tokare mata zuciya,

"Allah ya kaiku lfy y dawo d ku lfy,ina gaida tsohuwa me ran qarfe, sai kun dawo,"

Sabeer baiji dadin hakan ba,ya so su tafi dika, kwata2 baya son abinda Umman nasu take ma Aeeshaa da sunan wai kunyar 'yar fari,wannan ai shirme ne da kuma rashin wayewa, dik da su da alaqa da fulani ai ba haka ita Maman ta ke mata ba, tinda ko shawara da ita maman ta keyi, amma ita taqi jan tata diyar a jiki, tashi yayi jiki ba laka, dan ya sauya kayan jikin shi su wuce.

Tana wanke2 ya same ta, ya jingina da qofar yana kallon yanda ta juya baya take sharbar majina saboda kukan da take,

"Kar ki damu, inshaa Allahu zan kai ki da kaina, ki daina kuka, in munje da yawama bazaki wani ji dadin zuwan ba, ki bari sanda Umma bataje ba sai na kaiki, ki sake sosai abinki kinji yar qanwata?"

Juyowa tai tare da qaqalo murmushin dole,

"Na gode yaya, amma ni bansan me yasa Umma bata son jerawa dani muje gidan Hajja ba, rabona ma da gidan har na manta, ko ina za a fita ba ta zuwa dani, kullum sai dai a barni a gida kamar me gadi, innai magana sai tace wa xa a bari a gidan in mun fita dika,"

Kuka ne ya kwace mata ta juya d sauri ta ci gaba da wanke2n ta.

Cikin nutsuwa yake takawa zuwa gare ta, jin shi tai daf da ita,

"Kar ki na saka damuwa a ran ki kina qaramar yarinyar ki, zaki jawa kan ki wani ciwon,komai dake faruwa dake yana da dalili, Umma kunyar 'yar fari kawai take nuna maki, ba wani abu bayan nan, a bayan idon ki bakiji yanda take yabon ki ba,"

Da sauri ta juya wani farin ciki ya bayyana a fuskar ta,

"Yah Sabeer da gaske tana yabona a bayan idona?"

Ya bude baki zai bata amsar qaryar da ya shimfida yaji kira daga waje, ana qoqarin shigowa,

"Sabeer in bazaka kaimu ba mu mu tafi ai munsan hanya, ka samu waje ka yi zaman ka daga bari ka sauya kaya,"

"Umma kiyi hakuri nayi wanka ne, yanzu na shigo ina ma wannan 'yar qauyen sallama"

"Muje,ke kuma ki tabbata kan mu dawo, kin yi komai, kar na dawo naga wajen nan kaca2"

"Umma ku dawo lfy, ina gaida Baba General, kice ya baki abun dadi ki kawo min,"

"Eh tinda akaina rashin kunya ta qare sai naje ina fada masa saqon ki, keni bana ciki da rashin ta ido,"

Dan dariya sukai mata, dan gaba daya ita kamar ba wayayyiya ba, kunyar dan fari tin yaushe aka daina?

Tayi qoqarin kammala komai da wuri,dan tana da kazar2 da saurin aiki,sai dai tana yi a nutse da kulawa, yanda dik saurin da takeyi tana aiki me kyau, nan da nan gidan ya dau qamshi da kyalli, wanka tayi ta kwanta dan hutawa, in Umman ta ta dawo bata san kuma wanne aikin ne a gaban ta ba.

********************

Babban gida ne, kusan nace dik unguwar yafi kowanne gida kyau da girma, daga farkon layin zuwa rabin layin gaba daya gidan General Muhammad Mustapha Dan Bauchi ne, tsohon soja ne, wanda ya halarci yaqi kala2, kuma ya samu babban muqami, da kyaututtukan girmamawa, yayi ritaya amma har yanzu mahukuntan qasar nan suna damawa da shi, yana da matar shi guda daya, mai suna Aeeshaa, wadda suke kira da Hajja, auren soyayya sukai, wanda har yanzu soyayyar nan a kullum ba dan tsufa ba sai mutum yace sabbin aure ne, yana matuqar girmama matar shi,bai hada ta da kowa ba, itama haka, akwai fahimtar juna mutuntawa da kauda kai a tsakanin su.

A shekarar farko da auren su ta samu ciki, inda wata tara na yi ta haifi yaron ta na miji, aka maida sunan mahaifin shi wato Muhammad, amma suna kiran shi da Basheer, sai Abubakar, sannan daga qarshe sukai auta da Khadeeja.

Basheer shine babba, wanda yanzu haka suna tare a gida daya da mahaifan nashi, a bangare daban, yana da mata guda daya, yar garin Kano ce, mai suna Huwaila, mace ce mai mutunci da mutunta kowa, sai dai akwai ta da son abin duniya da son girma, gata kwata2 ba zaka taba mata kyauta ko wani abun alkhairi ba tace maka na gode, amma tsakanin ta da mijin ta sai son barka,kullum a cikin yabawa kyakkyawan halin ta yake, son abin duniyar ta kadai ke hada su, in yayi magana takan kashe bakin shi da cewa,

"Haba Abban Khaleefa, komai na siya ko na saka ai domin ka ne,"

Ta hakan yake dauke kai akan yawan bani2n ta. Suna da yara uku, Khaleefa wanda ya ci sunan kakan shi, (Muhammad Basheer Muhammad) sai Hamdiyya, da Bilqis. Matan sunyi aure dika, Khaleefa shi bai aure ba, har yanzu saboda girman kai, da ganin ba wanda ta isa ya kai kan shi wajen ta, ma'aikaci ne a filin jirgin sama dake nan a garin kano.

Sai Abubakar wanda yake shine mahaifin Sabeer, mahaifiyar shi 'yar uwa ce ga Hajja, dan haka aure zumunci ne suma, suna da yara Uku suma, Hassana,da Hussaina,Sannan Sabeer, Hussaina a tare aka aurar da ita dasu Balqis, yanzu ya rage sauran ita kadai a matan gidan.

Khadeeja itace autan Hajja, kuma itace mahaifiyar su Aeeshaa, ita kadai ce tayiwa Hajja takwara, wannan dalilin ne yasa Hajja ta hana a boye sunan Aeeshaa, Aeeshaa na da qanne kamar yanda kujaji sunan su a baya, Abdul Hakeem da Ameena.

Mahaifin Aeeshaa mai suna Salihu Adam, maraya ne, dan garin Katsina ne, yana da Yayan shi da ya rage masa, mai suna Isma'el Adam Katsina, yana can zaune tare da iyalan shi.

Neman aiki ne ya kawo Salihu garin Kano, makaranta daya suka gama da Abubakar Mahaifin Sabeer anan Kano, dan haka yace ya zo gidan su ya zauna har ya samu aiki, ya samu aikin banki, da taimakawar General, kuma yana samun albashi mai tsoka, dan haka General ya bashi shawara akan yayi aure, matasan yanzu suna samun kudi ba aure musiba ne, cike dajin kunya ya sosa kan shi, ya duqar da kai qasa, Hajja dake gefe tana shan kayan marmari, tace,

"Au ashe fa General baka da labari,"

"Na me fa?"

"Salihu Khadeeja yake so, dan na sha kama su suna hira, kullum ina son sanar da kai to ba ka zama sosai, sai na manta, yau dai Allah ya nufa kayi maganar a gabana, na san da ba zai fada maka ba,"

"Ahhh afff tooo... masha Allah, wannan abun ai yayi, yayi kyau hakan, na kuma ji dadi, Allah ya sanya albarka a ciki, yanzu abinda za ai shine, ya kamata kaje Katsina ka sanar da magabatan ka, kaga shikenan sai a zo a sha biki ko?"

Cike da jin nauyin su ya musu godiya sannan ya sanar da su rasuwar mahaifan shi, ta hanyar hadarin mota, ya sanar dasu yayan shi ne ya rage masa, da baffanin shi da kawunan shi.

Sun masa ta'aziyya, sannan suka shaida masa zasuje Katsinan tare, basu son a bata lokaci tinda suna son juna Hajja ta shaida hakan.

Cikin qanqanin lokaci akai auren su, Generak yayi2 su zauna tare da shi, kamar sauran yaran shi, Salihu yaqi, dan shi mutum ne mai zuciyar nema, da kuma son ya tsaya da qafar shi, mace dik son da take maka, taga iyayen ta na maka wani abu, komai qanqantar shi to ta samu kafar rainaka, haka ba dan Hajja taso ba suka samu gida a unguwar dake kusa da tasu, ya siya suka zauna.

Khadeeja na matuqar son mijin ta, amma kunya tana matuqar damun ta, kullum yayi ta tsokanar ta yace,
Chapter 2 · 0% Book details