Sashe 30
Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Aeeshaa ki daina damun kan ki, kin sani a da mun shaqu, amma a yanzu ke matar aure ce, ko kinga ina wasa da su Bilqis ne? Dik da yayuna ne su dole akwai tsakani, su din ba muharramai na bane, su Hassana da Hussaina sune zan iya sakewa sosai, ina fatan yanzu kin gane dalili na? Ki daina dmun kan ki kinji qanwata?"
Daga kai tayi tana murmushin jin dadi, Yah Sabeer daban ne a cikin maza, ya san dokokin Allah, kuma yana kare su, ina ma haka Yah khaleefa yake, nan da nan ta tina shi, qirjin ta sai da ya buga dan faduwar gaba, tinowa tai da Hoton su da ta gani shi da Hadiza, Hadiza na nuna shi a matsayin mijin da zata aura a iG, suna cikin motar shi, ga ice cream gaban su, yana bata a baki sukai hoton.
Da sauri ta dauki Ameerah zasu fita, fuskar ta ba walwala sam
"Lafiya Ayshaa?"
"Ba komai Yah Sabeer"
Da Ammar ta hadu, ta wuce shi, Ammar shigo wa yayi yana kallon Sabeer da bacin rai,
"Wai kai yaushe zaka daina wannan halin kafiyar? Ance maka ka fada mata ko ka sassauta mata ku koma normal, ji yanda ka bata mata rai, yarinya kamila,"
"Nifa ba ni bane, kawai mun gama magana naga ta tashi kamar ta tina abu ta fita, mun gama magana mun fahimci juna, kawai naga ta hade fuska ta fita cikin sauri, na tambaya tace ba komai, me kk so nayi,"
Har Ammar zai magana Hassana ta shigo dauke da magani da abincin su, ajewa tai,ta masa sannu, Ammar kallon ta kawai yake, har sai da Sabeer ya taba shi,
"Ka fa kiyaye, yaya ta ce,"
"So? Ni ban girme ka ba? Ko dan ina abota da kai? Shin in ma sa'o'i muke da kai mace ai ba ta yi wa namiji kadan sai dai in bai balaga ba,"
"Da gaske kk yi kana son ta?"
"Kwarai d gaske in dai zata so ni, a shirye nake na aure ta, kana ganin a iri na gidan ku akwai mummuna ne ko mai mummunan hali?"
Shiru Sabeer yayi, shi dai iya sanin shi babu, amma yana zargin khaleefa bai da halin kirki, dik da ba zai nuna hannu akan wani laifin shi ba amma dai bai da halin kirki haka yake zargi,
"Gaskiya babu, a iya sani na,"
"Then zan saka kai kawai Alhaji,"
Tafawa sukai, Ammar na qara jin labarai akan Hassana.
***********************
Aeeshaa na komawa ta samu Hajja,ta kunna Data, dan ta nuna wa Hajja abinda ta gani, saboda qarin aure ba da sanin su ba babban abu ne,kumq Hadiza for that matter.
Hajja ke waya,
"K, aiko min da su gida kamar wancan, kuma ka ci gaba da sa masa ido,"
Kashe wayar tai ta kalli Aeeshaa cikin tausayawa.
"Hajja akwai abinda nake son na nuna maki game da Yah Khaleefa,"
"Bana buqata, sai yanzu? Yanzu kk ga damar ki sanar dani ko ki nuna min wani abu game da mijin ki? Tin yaushe nake bin kan ki akan hakan? Kin nuna min? Riqe abin ki, nima na riqe abinda na sani akan shi, har a dawo daga dik gidan uwar daya tafi"
"Tafiya Hajiya?"
Banza Hajja ta mata ta shige kitchen, tar da kwalla mata kira akan taje suyi aikin abinci.........
*Team Sabeer me kuke gani game da shirun Hajja akan wannan lamari?.... Team Khaleefa me mutumin ku ke aikatawa a ABJ n a bamu mu sha...😅*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼
*BY HAERMEEBRAERH*
Page 22:
"Hadiza ni fa ban gane maki ba kwana biyu, kwata2 kin rage walwala, sannan yanayin jikin ki ma kin sauya, anya Hadiza? Kar ki sa na dinga maki zargin da ba haka bane, abinda nake zargin ki da shi bai kamata ace kina tare da shi ba duba da ke din bazawara ce"
"Goggo ki fito fili kice ciki ne da ni, yes ciki ne da ni, kuma cikin Khaleefa ne mijin Amarya,"
"Ya Allah, Ya kareem, Ya mannan, innalillahi wa inna ilaihirraji'un, wayyo Allah na,ya Allah ka sa mafarki nake, mummuna kar ka tabbatar da wannan lamarin,"
Kuka Hadiza ta fashe da shi, sai yanzu abun ke bata takaici, ta bata wayon ta, d tarbiyyar da Goggo ke bata a kullum, albasa batai halin ruwa ba.
Goggo ce a harzuqe ta nufe ta,
"Kukan me zaki? Ashe dik tarbiyyar danake baki a banza? Dama tin da naga fitar ki ta yi yawa addu'a ta Allah ya kiyaye mu kar ki dakkon magana, ashe ba zaki riqe maraicin ki ba da zawarcin ki har Allah ya kawo maki miji na gari, bayan kin san yanzu 'yan matan ma ba mijin suka samu ba, kowacce mace ta qanqame mijin ta bata son kishiya, koda kuwa mijin mai ra'ayin qara aure ne kin ban kunya, da ke da dikkan zawarawa masu aikata zina suna fakewa da zawarci suna aikara zina,tir da halin ki, tir da ke,"
Goggo fada kawai take ji take kamar ta rufe ta da duka, ba dan ta kai zuciya nesa ba da har ciwo sai ta jiwa Hadizan mummunam ciwo kuwa, dan a rayuwar duniya ba abinda ta tsana irin zina, ga shi Allah ya jarabci zuri'ar ta da ita, wannan mummunan labari in ya yadu a dangin su daga na uba har nata ai sun shiga uku, qara nesanta za ai da su, kuma ga mutan unguwa za su shiga bakin su, ohhh Hadiza ta dakko mata magana.
"Goggo dan Allah ki zauna kiji,ki daina daga hankalin ki, abinda ya faru ya faru,"
Dik daurewar Goggo sai da ta zabga mata magigicin mari wanda ya sa ta daina ganin haske na wasu mintina.
"Hadiza kar ki kaini maqura na maki abinda bana fata,dan uwar ki har kina da abin fada? Har ni zaki kalla cike kar na daga hankali na? Kin dagan shi tsaye ya zan ya kwanta yanzu, baki son na damu kk dau matakin wulaqanta ni, bani da buri wanda ya wuce na sama mana abinda zamu kai bakin mu, amma ke burin ki bai wice na ki watsar min da mutumci na ba ko? Allah ya shirya ki Hadiza?"
Hadiza ce ta fara magana cikin kuka sosai,
"Dan Allah Goggo ki hakuri, ki yafe min,inshaa Allahu wannan abun daya faru ba zi rusa komai ba indai kin ban hadin kai, so nake na aure shi, kinga shikenan mun samu surukin da zai dauke mana wahalhalin da muke ciki ko?"
"Ke yanzu kina ganin har kina da darajar da wani zai aura kuma? Me kk tanada da zaki ba namiji? Na farko dai na hana ki shafe2n mayukan nan na zamani kin kafe, fari banaki ba kowa ya gani ya san ba naki bane,dik yanda mai shafa mai ya so boyewa kar a gane wallahi sai an gane, kin zubda mutuncin mi a wajen mutane dan zasu gan ki baki waye ba, ke din ba ki da tarbiyya,ke mai sabon Allah ce kin sauya halittar da ya maki, kin raina Allah wa'iyazu billah, kina nuna masa bai iya halitta ba, ke ce kk iya, subhanallah,Hadiza baki iya girki ba, nayi2 ki koya kin qi, Hadiza baki da tsafta, da girman ki komai sai na maki in ban ba gidannan ya ruve dan qazanta ko?Hadiza ibada bata dame ki ba dik da damun ki da nake na saki gaba dan ki yi amma inaaa, Hadiza kwata2 ke ba yariyar kirki bace, kan wani ya fadamin na sani d kaina"
"Goggo.....kiiikiiii....yaaafeeminnn, inshaa Allahu na daina dikkan abinda kk ce, na tuba Goggo, daga yau na daina aikata dik abinda Allah yace, bana son na shiga wuta goggo, wayyooo Allah na, Allah ka yafe min, ya Allah kai me gafara ne kana son masu tuba Allah ka yafe min,"
Hadiza fa da gaske take kukan nan, kamar zata shide, gane cewa da gaske tame neman gafarar Allah da ta ta ne yasa ta rungume ta,tana lallashin ta, tar da kwantar mata da hankali.
"Goggo yanzu zubar da cikin za ai? Wata biyu ne da kwanaki, na je asibiti an tabbatar min da hakan,"
"Sam ba zamu zubar ba,yanda kk dakko sai kin haife shi,ina tausaya wa wannan mata yanda zata ji cin amanar da kk aikata mata,"
"Goggo na fiki tausaya mata yanzu, a da ina ganin itace babbar maqiyyiya ta,amma yanzu na fuskanci ni ce maqoyyiyar ta,kuma na cuci kaina,dan yanzu haka shi baya nan, ya tafi shaqatawa da wata karuwar shi,"
"Karuwar shi?"
Goggo ta fada cikin zaro ido da dafe qirji.
"Eh Goggo,kuma naji yace gidan su ma neman shi ake, Gogge ya kamata mu sanar da iyayen Shi zancen cikin, kar a zo daga baya suce basu san zancen ba,"
"Dan Allah kyale ni for now na ji da baqin cikin dake zuciya ta, na gaza a matsayina na uwa, na gaza, na gaza wajen baki tarbiyya da kula da dikkan abinda kk so, na gaza matuqa,"
Kuka Goggo take sosai, qirjin ta har dagawa yake, saboda tana ganin laifin ta ne hadiza ta lalace.