← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 41

Sashe 26

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da tsoron ki zan ji, kar ki kawon raini dan kinga na nemi wani abu wajen ki, haqqina ne ba dan haka ba ke baki isa na tsaya ina maki magana ba ma,"

Kashe data tayi, ta kwanta, can ta tashi, ta kunna, still yana online, shiga contact din ta tayi, tana duba numbers da take da, tana cikin dubawa taga Hadiza ma na whatsapp ashe, murmushi tayi, tana shiga contact din hadizan sai ta ga tana online,murmushi ta sake yi,

"Ohh Hadixa ko dawa ake hira da tsohon daren nan?"

Sallama ta mata, Hadiza ta gani taqi amsawa, can ba a jima ba sai taga message daga Khaleefa, da sauri ta duba,

"Ke sauka online, in kuma da wani qaton kike hira sai naji,"

Baki bude cike da mamaki ta sauka, wai ita ke magana da wani qaton, to a ina?lallai Khaleefa ba dama, to ita da bata kula shi ba ya akai yasan tana online? Ko kuma duba wa yayi yagan ta? Oho dai yaje yaci kan shi ta sauka.

Addu'a tayi ta kwanta, bacci ne mai nauyi cike da mafarke2 kala2 na ban tsoro da kuma nishadi ya mamayi baccin ta.

Allah ya tabbatar mana d alkhairi kedai Aeeshaa.

***********************

Tinda Aeeshaa ta tafi khaleefa bai je gidan ba, yau cikin Aeesha ya shiga wata na tara kenan, iyakar shi yaje wajen Rebecca ko ya dau Hadiza su faki idon mutane su shige gidan su sheqe ayar su, ta fita,ko suje inda suka saba zuwa.

A hankali son kasancewar ta matar Khaleefa ke shigar ta, da kawai so take suna debema juna kewa, amma yanzu auren shi take son yi dan ta dandana daula itama.

Wani babban abin haushin kullum sai sunyi waya ko chatting da Aesshaa, taji lafiyar ta wai da babyn ta, tayi2 taji cikin Aeeshaa akan zaman su da mijin ta taqi sanar da ita komai, sai tayi ta tambayar ta khaleefa ya je kuwa? Aeeshaa kullum sai tace mata me yasa take tambaya, taqi dai bata takamaimai amsa.

*********************

"Kasan Allah yau in baka zo gidannan ba sai ka ci Uban ka, kar ka ga ina daga maka qafa kana kiramin aiki in ka dawo ka gaji, kuma kana waya da ita, na gaji da jin uzirirn ka,kazo yau dinnan, dan matar ka ta wuni naquda, anjima in mun daidaici abin yazo gadan2 zamu kai ta asibiti"

"Haihuwa kuma Hajja? Wace irin haihuwa? Ko dai bari?"

"A'uzubillahi min kulli sharrin dan uban ka, wanne irin bari? Ciki wata tara cif ana xancen haihuwa, dan ka ja mana mugun baki kk kiran bari; sai dai ka barar da abincin ranar ka shegen yaro mai mugun fata,ga babar ka nan tin safe take sintiri akan yarinyar nan, tinda uwar ta ta zama baqauyiya, taqi zuwa, in baka zo ba nan da minti 10 zaka isko mana a asibiti"

"Kuje na taho,'

Hajja ta kashe waya tana ta masifa,

"Dik iskancin dake kan ka ka gama, bari ta haihu lfy hankalina ya nutsu waje daya, ai na gano inda kk zuwa yanzu daga wajen aiki, ba wajen karuwa ba ko wajen magajiyar karuwai ne sai na sa an kulle ta an kulle gidan nata, 'yan iskaa marasa tsoron Allah, ba abin tausayi irin Baban ka da General, sun aminta da kai matuqa kana xan kana iskanci,ita ma sallamammiyar matar taka ba zata iya fada ba kamar wanda kaiwa asiri ka rufe mata baki, dik to zan iya daku dika, marasa mafadi kawai,"

(Dama alaqar su Hadiza aka hango tafi ba hashi ni fai😡)

Asibitin da take zuwa aka kai ta, likitan na ganin ta yaggguta sallamar wanda yake gani, ya miqata wajen daya Dr. Dan yana matuqar son taimakawa Aeeshaa.

"Sannu Aeeshaa, abin yazo kenan, ku shiga da ita, ina mijin naki? Ko har yanzu yana kan bakan shi na zubda cikin,"

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, me nake ji haka?"

Da biyu yayi maganar, dan kamannin Aeeshaa da Khaleefa kamannin wannan dattijuwar, tabbas wata mata ce mai mahimmanci a rayuwar su, dole ya fadi hakan dan ta sa ma ma'auratan ido, Aeeshaa kuwa bata son sirrin gidan ta ya bayyana, kullum addu'a take Allah ya gyara mata lamarin ta, bata son asirin Khaleefa ya tonu, ko da ba mijin ta bane zata so ya shiryu ba tare da kowa ya san meke faruwa ba, amma likitan nan ya sa Hajja zata matsa sai ta san komai.

An shiga da Aeeshaa Hajja da Maman Khaleefa hankalin su ya kasu kashi biyu, dama baya son haihuwa? Amma Aeeshaa taqi fadawa kowa? Lallai wannan yarinya a gaishe ta, sai tinanin haihuwar ta.

Hajja ce ta dauki waya ta kira Umman su Aeeshaa,

"To bafulatanar daji, tana dakin haihuwa sai ki mata addu'a"

Kit ta kashe wayar ta, danta san indai Khadeeja ce bazata samu kyakkyawar amsa ba.

Hassana da ummeen sabeer na gida suna aikin tarbar baqo ko baquwa, farfesun naman rago Ummeen Sabeer ke dafawa, Hassana ta dora ruwan wanka a bangaren Hajja, sai addu'a take Allah ya sauki Aeeshaa lfy.

Likita ne ya fiton yana washe baki,

"Mama a bani goron albishir gaskiya,kafin na fadi kinyi Amarya,"

"Alhamdu lilLAAHi ai ka riga ka fada, ga wanda yayi amarya nan, mu kam diya ce muka sake samu,ga uban yarinya kuma anan,"

"Baba General ne ke wannan maganar daidi lokacin da yake qarasowa, bai taho ba sai da ya biya office,din Baban Khaleefa ya dakko shi sannan ya taho da khaleefan, in ka gan shi da Baban khaleefa sai ka rantse abokai ne,babu ruwan shi da daukan kai ma yaran shi, yana jan su ajiki sosai, komai tare sukeyi musaman na family.

Khaleefa ba mai gane yanayin shi, fuskar nan kamar kullum cike da munafushin murmushi.

Hajja wani kallo ta watsa masa na zamu gaura da kai ne.

Dakin da aka gyara mai jego da baby suka shiga, nan kowa ya dinga yabawa yana ganin qoqarin Aeeshaa na haifar wannan narkekiyar yarinyar.

Khaleefa na ramuve a gefe, ya rasa kallon mutuwar da Hajja take wurga masa.

Karambani ya kaishi daikar yarinya daga Hannun Baban shi bayan ya gama yi mata addu'a..............

*wayyooo cikina🤣🤣What do u think will happen guys?🤣*

*hummmmmmm wata sabuwa*

*Khaleefa w........ka daban yacin in baka tuba ba🙊🙊*💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

Page 19:

"In ka taba ta sai na sare hannayen ka da wannan silver din, dan uban ka ba barin ta kk son ayi ba? A zubar d cikin ko? Kar ta zo duniya, hummmm na maka murna a asibiti muke, da agida muke sai na maka dukan da zai tabbatar maka da sauran qarfina, shiyasa mutane ke cewa ni babar ka ce ba kaka ba, dan iska mara mutunci bar nan, ai ko ba kai za ta rayu, akwai uban ka akwai kakan ka, har suna dik zasu saka mata,ban taba sanin baka da mutunci har haka ba khaleef, ka fita nace ko? Ko kayi ajiya je anan din?"

Kuka Aeeshaa take yi saboda a kwace take amma jiri take gani, jinin nan fa ya qi tsaiwa, Hajja ko a zaton ta korar da akao wa Khaleefa ne ya sata kuka,

"Kema taki uwar xanci in baki rifen baki ba,bari dik mu koma gida, in baki fadan asalin zaman ku ba ni da ke ne, mun tattara mun miqa ki muna ganin shi mutumin kirki ashe dik rufemu yayi"

"Hajja bata numbashi,"

"Subhanallahi kira likita da sauri,"

Likita ne ya shigo da azamar shi, Khaleefa ba wanda ya san sanda ya bar wajen.

Ana ta qoqarin bata taimakon gaggawa, likita ya sanar da su Hajja jini e bai tsaya ba,da sauri ta fita dan koma gida, driver ne ya maida ta, sai azalzalar shi take yayi sauri, Hajja akan Aeeshaa bata da sauqi, wannan karon ba zata yi wa kowa da wasa ba, tinda aka dano ta sai tai harbi zata huce.

Tana isa gida, Hassana da Ummeen su sukai ta mata barka, hankalin ta tashe take amsawa, gyada ta debo danya, ta wanke ta jiqa sannan ta zuba gishiri kamar cokali daya da kadan, barin ta tayi kamar minti sha biyar, ta jiqu bayan ya fara kamar barewa d kan shi, ruwan yayi jawur, sai ta tsiyaye ta saka a gora, da azama ta shirya ta koma asibitin.

Taje Aeeshaa ko motsawa bata yi, tana nan kwance, an smau jinin ya rage zuba, dan haka ta bawa likita maganin da ta kawo, tace a bawa Aeeshaa zai tsaida jinin, musu ya tsaya mata akan ta hakura zuwa wani lokacin.

"Ina da 'yancin da zan bata da kaina, amma na baka, in wani abu ya samu jikata sai nai qarar ka, ni da ka ganni nan cikakkiyar 'yar boko ce ba 'yar gargajiya ba, balle kace zan mata wani abun da zai cuce ta,yanda nake son ta ko uwar ta bana so haka, maza amshi ku san ya zakuyi ku dura mata ta shanye,"

Amsa likita yayi, ya shiga ciki suka sa mata Hajja na kallo, dan bata yarda ta barshi ba yaqi bata.

Suna nan zaune kamar awa daya, ta farka, tana jin yunwa, kowa sai murna yake,jini ya tsaya, ba wata matsala yanzu, sai satar kallo yarinyar take,

"Amshe ta ki riqe abin ki, ke kinfi kowa sanin ciwon nunawa yaro qiyayya, ke zaki bawa wani labari ma, amshe ta ki mata addu'a ki sa mata albarka, sannan ki tauna dabinon nan ki bata, a bata zamzam dinnan, Allah ya muku albarka, ya qara maki lfy ya yara mana ita da imani"

"Ameen Hajja na gode sosai, Allah ya ja mana da ranki,"

"Ameen Aeeshaa ta, maza bata kema ki ci abincin, hada mata shayi kai Muhammadu,"

Mugun kunya ne ya kama Aeeshaa da taga Baba da kan shi yana hada mata shayi cikin farin ciki da kuma son yin hakan.

Mama sai qoqarin amsa tayi take ya dakatar da ita,

"Basshi kawai ke zuba mata abinci, ai ba wani abu bane, diyata ce fa, ko kin manta ne?"

Murmushi sukai, ran Hajja yayi fari, a qalla Aeeshaa bata maraicin uba sai Uwa, gata kusa amma kamar itace ta mutu.

(Hajja bata da labri fa yanzu Umma tana zuwa wajen Aeesha a sace)

Waya ta dauka ta kira Khadeejan,
Chapter 26 · 0% Book details