← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 41

Sashe 22

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana kiran asuba Aeeshaa ta tashi domin gabatar da sallah, ji tai an qanqame ta, kamar za a kwace ta,daga kai tayi taga yanda ya dora kan shi daf da nata, hannayen shi na kan qirjin ta, haka ma qafafun shi suna maqale da nata.

Hade ran ta tayi, shi baida aiki sai hakan,a karon banza ba zai mata wannan riqon na so d tausayawa ba.

Janye hannayen shi tayi daga kan qirjin ta, aikuwa kamar yaron da aka kwacewa alawa, ya qara rarumar ta ya matse a jikin shi,

"Wasssshhh Allah na"

Bude ido yayi ya ga kwanciyar da yayi, da sauri ya sake ta yayi baya yana zaro idon shi, rufe jikin shi yayi ya tashi, ya sanyakayan shi ya bar dakin, da kallo tabi bayan shi, daga baya ta tashi ta je dan tai wanka tayi sallah.

Yau Khaleefa ko karyawa bai ba ya je wani babban shago da suke saida wayoyi, ya siyo ma Aeeshaa waya mai kyau, ya hado da yan abubuwan motsa baki, ya nufi gida, sanda yaje ta gama hada abn karyawa, ta saka doguwar riga baqa mai ratsin blue, ta daura mayafin, gwanin sha'awa, lips din ta sai walqiya yake, gashin ta ya kwanta a bayan ta ta cikin dankwalin, ga qamshi mai kwantar da hankali dake fita daga kowanne sassa na jikin ta, cikin ya matuqar amsar ta ya mata kyau sosai.

Ya na shiga ta tashi tana masa sannu da zuwa, yau ce rana ta farko da Khaleefa ya mata magana ba fada ba hantara ba zagi,

"Yauwa, kin gama abinci? Yuuunnwaaa nake ji,"

"Na gama, bismillah,"

Aje mata ledar kayan yayi ya wuce ya fara durawa tumbin shi abinci, yana ci yana kallon ta,ta aje kayan a gefe inda daya gama zai dauka ya wuce dakin shi.

"Ki duba mana,"

Kallon shi tayi kafin ta fara buda ledar farko, kayan marmarin da take so ne, murmushi ne ya subuce mata, dan ta samu abun karyawa, dama yunwa take ji ta kasa cin abincin.

Dayar ledar ta bude ta ci karo da waya mai mugun kyau da tsada, d sauri2 ta qarasa zaro ta tana washe baki, Khaleefa ma murmushin gefen baki yayi, ya qura mata ido, wayar shi ce tayi qara, yana dubawa yaga Hadiza ce ta ke kiran shi, bai dauka ba, amma zai so ya dauka din, da taji bai dauka ba ta turo masa message,

_Duba_ _whatsapp_ _dinka_ __love_

Da sauri kamar wanda aka mintsina ya tashi yana murmushi,

"Ki sata a caji kan ki fara amfani da ita,ban da kiran qawaye, kuma inna kama ki kina abinda bai dace ba daga ranar zan amshe ta,"

"Na gode Allah ya qara budi, Allah ya sanya ka farin ciki,"

Qarammm taji qarar qofa, juyawa tayi taga ya shige daki,

'Mai hali ai bafasawa'

Bude whatsapp din shi yayi ya ga hotunan Hadiza, ta sha gayu da qananan kaya dik qirjin ta a bayyane, riga ce shara2, yan mitsi2n n****wanta a waje a tsaitsaye, Khaleefa kiran ta yayi suka hau hirar su ta rashin da'a.

Ranar bai fita office da wuri ba.

Da rana Umma tazo da su Ameena, Ameena da Aeeshaa sunyi murnar ganin juna sosai, Abdul ba laifi harda gaisuwa.

Bayan sun gaisa da Umma, Umma ta debo kayayyakin datake tarawa ta ba Aeeshaa,

"Saura naji kin fada ma wani ni na kawo,"

Dariyar qasan maqoshi Aeeshaa tayi, kwana biyu Umma ta daina nuna matsananciyar kunyar nan, da alama anayi da wannan jikan ko da ita ba a yi da ita.

Godiya tayi sosai, ta nuna ma Umman wayar ta sabuwa da aka siyo mata da safe.

Kar ba tayi ta kalla, ta kiqa mata,

"Allah ya tsare, aji tsoron Allah wajen amfani da waya, dan yanzu waya ta zama makamin kai da damar mutane wuta, an sauqaqa zina da dikkan wani mugun abu, yanzu har bokanci ana yi ta waya, dan haka ki ji tsoron Allah akan waya, dik abinda zaki kiyi kina tinawa yatsa daya in kin dora akan screen Allah yana ganin me kk danna, mala'iku na rubuta abinda kk aikata,"

"Inshaa Allahu Ummana zan kiyaye, na kuma gode,"

Tana son ta dakko masu abin tabawa tana tinani tasan halin Umma, tinda take ko ruwa bata taba sha a gidan ba, tashi tai a hakan dai bari ta kawo.

Fruits ta wanko ta kawo masu da juice, da snaks, Ameenaa da Abdul kuwa sun ci, amma Umma sai azalzalr su take akan suyi sauro su tafi, ko ta wuceta barsu,

"Umma ki barmu ana,"

"Abarki dai,"

"Ohhh Abdul Allah ya nunamin sanda zaka daina qina,"

Jikin su je yayi sanyi dika har Umman, a ran ta tana son aje kunyar nan amma abun yabi jikin ta, hakan ne ma yasa take zuwa akai2 kwana biyu, amma har yau Khaleefa bai san tana zuwa ba, Hajja ma a tinanin ta bata taba zuwa ba har yau, har fada ta mata, tai shiru,ita dai bazata ce mata taje ba.

"Kawo na sa maki whatsapp a wayar ki, na bude maki facebook,instagram, na sa maki snapchat"

"Nan kafi kauri,"

Abdul karba yayi ya saka mata through Xender, daga wayar Umman su, nan da naj ya bude ya koya mata yanda akeyi, Instagram ne yafi daukan hanakalin ta, da facebook, tinda Whatsapp bata da no kowa, Abdul ne ya sa mata no Umman su, data Hajja.

Tayi murna sosai,aje wayar tayi, ta bama Umman ta lokacin ta, Umman taji dadin hakan, amma sai ta ce bari su tafi, kafin wannan dan rainin wayon ya dawo, dik da ba wani jituwa ske ba amma Aeeshaa bata son Umman ta na fadan hakan.

***********************

Cikin Aeesshaa ya kai wata bakwai, ya shiga farko2n na takwas,Hajja ce ta zo da yamma liqis, cike da fara'a,dan so take ta wuce da Aeeshaa,

"Hajja na hada komai da kk ce, amma ai zamu jira ya dawo ko?"

"Ahhh dole ai, na dauke masa mata bai sani ba? Ke dai gama shiryawa kawai, ina nan ina jiran shi, na tambaye ki yafj sau shurin masaqi lafy kuke kince lfy kuke, ana zaune lafiya ace mace bata da lambarwayar miji waya tayi wata,tabbas akwai wata a qasa da ba a son na sani, kuma in Allah ya so sai na gano ko me ne, ai ita qarya fure take bata 'ya'ya"

"Kaiiii Hajja ba kyau mita,tsufa take sawa,"

"Uwaki, ni din da wace ce? Ai kowa ya ganni ya san dam tsohuwace ni,ko dan kinga ban takwarkwashe ba?"

Haka sukai ta hira suna kumawa, Hajja na sane taqi kiran shi so take taga yaushe zai dawo, ta san lokacin tashin shi yanzu yayi, me ya hana shi dawowa har anyi magrib yanzun.

Abinci Aeeshaa tayi mai sauqi suka ci, ta aje ma Khaleefa ma, tana nan zaune suna taba hira da Hajja Hadiza ta shigo, ta sha kwalliya kamar mai zuwa gasae kyau,

"Amarya ina ta kiran wayar ki baki daga ba, dama naji mai gidan na nan ko baya nan dan na shigo, kar mu hadu ya hau fadan nan nashi,"

Aeeshaa sai kyafta mata ido take kwata2 bata kula da Hajja ba sai da ta zagayo ta zauna,

"Yi hakuri Ina wuni,ban kula ba,"

Hajja haka nan taji Hadiza bata mata ba, dan haka cikin daure fuska ta amsa da

"Lfy ke kuma wace ce kk tambayar me gida na nan ko baya nan?"

Kamar an gama sanin sirrin ta haka Hadiza taji,cike da daburcewa ta amsa,

"Maaammmmaqota muke, suna na Hadiza,"

"Ohhhh, to fita zamuyi yanzu,"

"Ok to sai anjima, Amarya sai munyi waya,"

"To na gode ki gaida Goggo,"

Bayan ta tafi, Hajja tace

"Wannan kullum take zuwa?"

"Eh, da farko Yah khaleefa baya son kowa ya shigo, daga baya kuma ya bar ta tana zuwa, in bata zo bama.zai ce na kira ta tayani zama, na kula bai son na zauna ni daya ne,"

"Ummm"

"Tsakanin ki da Allah yaushe yaie dawowa gida?"

Jimmm tayi kafin ta amsa,

"Gaskiya wataran yana kai 1 ko biyu ma, kin san yanayin aikin shine hakan,"

Hajja kada kai kawai tayi akwai matsala, aikin shi bai kaiwa haka, tabbas wani wajen yake zuwa, amma zata gyara komai, in ma matsalar daga wajen Aeeshan ne zata gyara, in daga wajen shi ne zata gyra inshaa Allahu.

"Tashi mu tafi,"

"Hajja baya nan fa,"

"Nace muje, uban daya sa shi a dade shi zai sa ya dawo yaga baki nan,"

Driver ne ya shiga yayi ta diban kaya yana kaiwa mota, Hajja ta danna wayar khaleefa,

"In ka dawo daga yawon naka mun wuce gida da ita,"

Ta kashe wayar ta, Khaleefa kira yayi tayi bata dauka ba, ashe sanda Hadiza ta shigo, tana fita suka hadu,ya dauke ta suka wuce wajen da suke haduwa,

"Muje gida,"

"Habaa yanzu fa muka zo, kasan ina tsananin buqatar ka,plss ko minti sha biyar mu dan yi sai mu tafi"

Bai ko gama jin me zata ce ba y fara tuqa motar zuwa gida.

Hajja na tayi ma Aeeshaa fada dan ta kula so take ya dawo kan su wuce, ita Aeeshaa tana ganin haramun ne ta tafi ba tare da izinij shi ba, shiyasa take jan lokaci, a dole haka suka tafi ba tare daya isko su ba.

Sanda Khaleefa suka iso bakin layin su, ya tsaya Hadiza ta bude motar ta fita ranta bace,da sauri ya ja motar ya nufi gida,yana zuwa ya ga ba kowa, sun wuce kenan gaskiya Hajja na masa abinda taso, ranshi bace ya fita rufe gate,Hadiza ya hango bata qarasa shiga gida ba, wani tinani ne ya fado masa a ran shi.........
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

Daki ya wuce tare da rufe qofar shi, dik da ya san bata shigo masa daki sai ta nemi izini.

Hadiza na shiga gida ta zauna ta gilla qarya, wai na canji shiyasa ba a bata kudin ba.

Tana zaune wayar ta tayi qara, waya ce da zata kai dubu talatin da 'yan kai, Goggo tayi fadan tayi lallashin akan ta sanar da ita inda take samun kudi amma sam taqi,in fita zatai Goggo ta hana ta sai ta fita, dan gani take ai yanzu ta girma, tinda zawarci take,bata ga dalilin da zai sa a kulle ta a gidan ba.
Chapter 22 · 0% Book details