← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 41

Sashe 11

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"My dear, ki sanar dani me ke ranki game da Yayan ki, in baki son shi ko kina da dalilin da yasa kk kira shi fasiqi ki sanar dani, ni na fara sha'awar hada ku, saboda ke ta gari ce, shi kuma halin shi bamu da tabbas akan shi, muna saka ran, ko me yake aikatawa mara kyau, zaki zama sanadin shiryuwar shi, wannan dalilin yasa na sanar da General ra'ayina da tinani na, amma a yau in kk ce baki so,ga dalili kwakkwara, xan warware maganar nan, kin dai fi kowa sanin dik abinda nake so, shi General ke so,so tell me, i am here for u my dear,"

Hajja na magana tana tinani, tabbas tinda suka ce suna saka ran ta sauya shi, is either suna da masaniyar mugayen halayen shi,ko kuma suna zargin yana da mugayen halayen ne, dan haka is of no use ta tsaya masu bayani, dan haka kawai ta amince, Allah ya bata ikon zama da shi da amana, kar ta cutar da shi, kar ya cutar da ita, kuma zata miqawa Allah zabin rayuwar ta, dik abinda yake alkhairi Allah ya mata, ya kare ta daga sharri.

"Kinyi shiru baki ce kmai ba,"

"Na amince da zabin ku, Allah ya shige maba gaba,"

Rungume ta Hajja tayi sannan ta mata kiss a goshi,

"Allah ya miki albarka,"

Nan ta dinga vata labarin zuwan su England, da su America, da sauran qasashen waje, da irin qauyancin da tai kan ta waye, ta saba,just to cheer her up, tin Aeeshaa bata dariya har ta fara, sai da ta kula tana jin bacci ta miqe tace ta gudu wajen dan tsohon mijin ta.

Tana fita,Aeeshaa ta shiga sabon shafin tinanin yanda rayuwar aure zata kasance mata da Yah khaleefa.

*********************

Da safe Sabeer yaji labarin amincewar Aeeshaa, hankalin shi ya qara tashi, lallai yana son maso wani, tinda ta amince shi me ya rage masa ya zauna anan, da hanzari ya wuce office, yana neman transfer ko kudu ne a hankada shi, inda ba zai sake ganin ta ba sai ya so.

Aeeshaa ta so su hadu da shi, dan ta koka masa dik abinda ke zuciyar ta, ko hakuri ya bata ai ta samu sauqi, he is no were to be found.

*******************

Hajja da kan ta take saka driver ya kai su gwammaja, shagon DUBAI, inda suke saida kayan da ke maida tsohuwa yarinya, islamic chemist ne, suna saida kayayyaki na gyaran jiki,sabulai kala2, na slimming, mai na slimming, na stretch mark, kayan mata masu kyau da inganci, zuma mai kyau, turarukan wuta,hummm abun sai wanda yaje shagon kawai, ga sauqin kudi, dan suna saida kaya ne akan farashin sari.

Aeeshaa kunya ta dinga ji, amma Hajja ko a jikin ta, haka ta dinga yi ma Ibraheem da Haruna bayanin aurar da jikar ta zatai, tana son a hada mata kayan mata masu kyau, da zasu gyara ta, nan kuwa suka dinga hada mata, sai da suka tabbatar sun saka komai, suka buga lissafi, suka basu kaya suka tafi.

A zaton Aeeshaa kayan nan da ta gani za ai ta dirka mata tasha, sai taga Hajja ta adana su,ta boye.

"Kk zaro ido kamar an wurga mage sama, ba wai baki zan yanzu ba, sai an kai ki naga kamun ludayin mijin naki zan fara baki su, yanzu gyara zamu fara namu na gargajiya, natural gyara wanda ba zai lalata maki budurci ba,sai dai ya qara inganta shi, dan ba komai ake yi wa budurwa ba da sunan gyara.

Kan Aeeshaa na qasa dan kunya, ga ajiyar zuciyar kwanciyar hankalin da ya shige ta, data ji ba ita za a dirkawa wannan kayayyakin ba yanzu.

Aikin girki suka fara, hajja na son ta sake koyar da ita abincin gargajiya masu gina jiki, tinda ba laifi ta iya na zamani sosai, dan wasu ma Hajja agunta take gani.

Daga girki kuma sai Hajja ta daina barin ta cin kowanne abinci, sai mai gina jiki, da zai qara mata ni'ima,kamar ganyayyaki. Farfesun da yaji kayan qamshi,shayin da yasha kayan qamshi da minannas kadan, sannan tana mata kwadon zogale, da alayyahu, tare da tumatur mai yawa, da albasa.

Gashi kusan koda yaushe tana markade mata cucumber da carrot, tana hadawa da sugar, zuma da dan gishiri kadan ta sa ta shafe mata jikin ta da shi, bayan ta gama ta jiqa lalle ta tace ruwan ta sa ta wanke jikin ta da ruwan, tin Aeeshaa bata so, ita kan ta sai taji tana so, fatar ta ta sauya, kyaun da tai ko ba kwalliya in ka kalle ta sai ka qara.

Cikin wata daya, Aeesha ta sauya, harda girma sai da ta qara,ga shi ta cika sosai hips da da dik inda ya kamata ajikin ta sai da dik su ka ciko, saboda hadin ganyayyakin da ake bata, kunya take ji ta zauna ba Hijab, dan haka kullum cikin doguwar riga da Hijab take.

Sabeer dai har yanzu basu hadu da Aeeshaa ba, ta hango shi yana fita da mota daga gidan, ya koma aiki can Ibadan, yayi kyau, yayi qiba, ya aje saje, sai daga masa hannu take, amma bai tsaya ba, ya ganta ko bai gan ta ba, daga shi sai Allah suka san hakan.

Cikin bacin rai, da rashin jin dadi ta juya zata koma ciki, aikuwa sai a kan qafar shi, da guiwar hannun ta ta naushe shi a ciki, bata ko sani ba, 'yar qara ya saki, ya dafe wajen,da sauri ta kai hannun ta kan nashi, tana taba cikin tare da furta,

"Wayyoo Allah na, dan Allah kayi hakuri, Yah khaleefa ban sani bane, dan Allah kar ka dake ni, na tuba, ba zan sake tafiya ina waige ba,"

Sake baki yayi yana kallon cikin idon ta, wanda ya ciko da hawaye,yayi wani irin kyau, ga hannun ta mai laushi data dora akan nashi, (ba dole hannu yayi laushi ba tana shafa man kwakwa, da alayyadi, tare da man ridi, wanda hajja ta zubawa madarar turare mai dadin qamshi)

Labbam ta yabi da kallo, ganin irin kallon da yake mata ne yasa tai sauri janyewa, ta dirirce, bai da niyyar motsawa ko bata amsa, da gudu ta nufi cikin gida, Hassana da komai ya faru akan idon ta kasancewar tana qasan bishiyar mangwaro dake gidan ce ta saki tsaki, ta juyar da kan ta ta sake qanqame wayar ta, a ganin ta da gayya ma sukai hakan dan ranta ya baci, Khaleefa ji yayi kamar an zare masa laka.

"Allah ka gaggauto da ranar bikin nan kusa".............

*Kuna cikin 'Yan Ameen ko kuwa? Nidai nace.........🙊😆*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

Page 9:

Qarfe tara da wasu mintuna Hamdiyya ta zo da mijin ta, wanda a ranar yake son su koma, cike da murna da farin ciki suke ta gudanar d harkokin bikin, wanda su kadai suke farin cikin su, amarya da ango zuqatan su kamar ana dana masu wuta suke ji.

Can gidan Umman Aeeshaa ita da qawayen ta suna na su bikin,amma nunawa take ita kam ba wani hidimar biki da zatai, Hajja kuwa na riqe da jin takaicin ta ,ta dau alwashin itama sai ta dandana mata taji yanda Aeeshaa ke ji, Allah ya kaimu a gama bikin lfy, ai in fillanci take ji ta fita zama bafulatana tinda ita ta haife ta.

Qarfe 11 daidai aka daura auren Khaleefa da Aeeshaa akan sadaki dubu hamsin, aure ne daya halarci manyan masu hannu d shuni daga kan manyan 'yan siyasa zuwa 'yan kasuwa.

Kowa ka gani cikin farin ciki yake amm bnda Ango,shi ko dan yaqen nan ma yaqi yi,Sabeer ke ta gaisawa da mutane sai ka rantse shine angon ma, amma cikin zuciyar shi shi kadai yasan me yake ji, ba bu wanda ya kula ya zame ya bar wajen, mota ya fada ya kife kan shi ya na sauke numfashi mai nauyi da zafi, shikenan, shikenan Khaleefa ke da sa'a ba shi ba, Khaleefa ya fishi sa'a a rayuwa, ina xai saka kan shi yau, Aeeshaa ta zama mallakin wani, numfashin shi ne ya fara barazanar dauke masa, da sauri ya kunna motar ya bude window ya tada ta a guje, ya bar wajen, iska na ratsa shi amma ji yake kamar a cikin rana yake.

Bai tsaya a ko ina ba sai gidan Umma, yana zuwa ya shige dakin shi, ya kulle,kuka mai sauti ya sake, bai damu ba kowa ye xai ji shi ba zai iya riqe wannan baqin cikin ba, kuka yake kamar wani qaramin yaro yana birgima a gadon shi, hannun shi riqe da saitin zuciyar shi, ji yake kamar zata fashe dan kumburin da yaji qirjin shi ya yi, ga wani maqaqin dauri a wuyan shi ya qi shigewa yaqi ficewa.

Kwankwasa qofar akai, hakan bai sa ya daina kukan ba, da qarfi take kwankwasawa, dan taga wucewar shi, cikin kukan da yake son ya danne ya miqe yana layi ya bude qofar, juya baya yayi, xai koma, ta dora hannun ta akan kafadar shi

"Haba yaron Umma? Komai yayi zafi maganin shi addu'a ga Allah ya yaye ma bawa, ina hankalin ka ya tafi zaka manta da Allah a wannan yanayin da kk ciki, ba yanda zanyi ne da ban bari an yi wannan auren ba,"

Da sauri ya katse ta, cikin daga mata hannu, idon shi sun yi jawur saboda kuka.

"Umma baki taba min laifi ba a duniya domin ke uwata ce, amma a wannan karon bana ganin laifin kowa sai naki, ke ce silar yi ma Aeeshaa auren dole, da kin ja ta a jiki ba ki nuna mata tsana da wai itan 'yar fari bace da ta zayyana maki me take so, meye bata so, sannan da kin cire kunya sanda akai hadin nan,d kin tsaya mata kin ce bai maki ba, da kin kwatar ma diyar ki 'yancin ta da aka danne mata.....

Da qarfi ya tafi zai fadi sakamakon marin daya ziyarci fuskar shi ba tare da zato ko tsammani ba.

Cikin kokawa Umma ke magana.
Chapter 11 · 0% Book details