← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 41

Sashe 20

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan take Dr. Ya qara tabbatar d zargin shi, ba yau ya saba ganin maza na son a zubar da cikin halak ba, masu shegu su zubar masu na sunna su zubar sabida dalilin son zuciya.

"K madam muje damin scanning din, ba anan ake ba,ki kwantar d hankalin ki ba wani matsala, zai fita a hankali, ba zaki san ma yana fita ba saboda maganin da zan baki zai hana maki jin zafi,"

Wani daki suka je, likita yayi yayi Aeeshaa ta fada masa meke faruwa a tsakanin ta da mijin ta,amma sam taqi, wannan abina ya shafi iyalin su ne, ya yi aikn shi kawai tinda shima ba imanin gare shi ba.

"Look baiwar Allah, Aeeshaa kk ko? (Daga masa kai tayi) k, kinga na fahimci halin mijin ki, shi yasa na ke tambayar ki taimaka maki zan, dan inna bar shi ya kai ki wajen wasu, zubarwa zasuyi a banza,na sha ganin cases haka, so ki amince min zan taimaka maki,"

"Dan Allah ka tausaya min,ina son cikin nan, kar ka zubar min, bamu sn ma cikine dani ba sai da muka je gida yau, kakar mu ke fada, yanzu tana jiran result ne, dan Allah kar a zubar min da abinda ke ciki na😭😭😭"

"Ki daina kuka, inshaa Allah sai kin haifi abinda ke cikin ki,"

"Allah ya yarda, na gode,Allah ya saka maka da alkhairi,"

"Ameen, kwanta yanzu na duba na ga ni,"

Scaning akai mata, daga qarshe likita ya gano cikin ta ya kai wata hudu, amma ya yi takardar qarya, yace wata biyu ne.

Ko da ya sanar da Aeeshaa plan din shi, tayi murna sosai, sannan wannan maganin da yace tana zuwa ana saka mata antinatal care zata na zuwa, ya rubuta har da lokacin daya kamata tana zuwa, ya bata magungunan da zasu qara mata lfy da abinda ke cikin ta.

"Yallabai u ar good to go, amma akwai shawara sai ka jure, zaka dan dakata da yawan saduwa da ita, ya zamana lokaci zuwa lokaci ne, saboda mu samu maganin mu yayi aiki da wuri,"

"Ba damuwa na gode Doc, na gode sosai,"

"Akwai bayanai dake cikin wannan takardun dana rubuta zaka samu dik abinda kk nema,"

Aeeshaa kan ta a qasa, ta qi bari su hada ido da Khaleefa kar ya fahimci kwanciyar hankalin da ta samu.

*********************

Khaleefa ya fita sha'anin Aeeshaa kullum amma yana sata gaba ta sha magani, ko neman ta ya hakura,sai dai sanda jarabar shi ta motsa akan ta zai je dakin ta yayi ta romancyn din ta har sai ya biya buqatar shi, Rebecca kuwa kamar sallah dan.murnar samun khaleefa akai akai, ba damar ta tambayi dalili.

Da lokacin Antinatal yayi Aeeshaa zata dau adaidaita sahu ya kai ta asibiti, taga gama ta koma gida.

Umma tayi murna sosai d labarin cikin da Aeeshaa ke dauke da shi, amma ko da wasa bata sa maganar a labban ta ba balle wani ya ji, kayan yara unisex take siya a boye in taje sarin kayan ta.

Lokaci zuwa lokaci takan je gidan, tai kicin2, wai ita a dole kar a gane murna take zatai jika😢😂.

**********************

Ziyara ce ta musamman yau Maman Khaleefa zata kai ma su Aeeshaa, dan ta kwana biyu bata ga dan ta ba, sannan bata ji aike ba, yau so take taje taga meke hana shi zuwa, in ma dan Aeeshaa na da ciki ne ya daina bata kulawa zatai maganin su dika.............

*Allah ya kai hankalin Hajja kan ki Maman khaleefa kici.......🙊*
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

Page 15:

Aeeshaa na ta bacci Mama na ta kwada sallama, ko da a cikin mafarki bata ji sallamar nan ba, Mama dik ran ta ya baci, daki2 ta fara bi tana leqawa, ganin irin dukiyar da aka kashe a gidan ya qara bata haushi, yaran ta da akai ma aure ba wanda aka kashewa wannan dukiyar, (kamar Khaleefan ba dan ta bane) kwafa tayi, lokacin da ta isa dakin da Aeeshaa tai daidai take baccin ta cikin kwanciyar hankali, daga ita sai 'yar qaramar riga red mai hannun vest iya cinya, dik ta tattare sama, sai pant din ta red, ganin hakan bai sa Mama komawa baya tai sallama ko kwankwasawa ba har Aeeshan ta farka.

Qarasawa tai ta tashe ta, cikin magagin bacci ta ture hannun ta, ta gyara kwanciya ta ci gaba da bacci, a zuciye Mama ta daka mata duka, ai kuwa da sauri ta miqe,

"Dan Allah kayi hakuri, b.... Mama???"

"Eh ni ce, kn kwanta kina ta baccin asara in da barayi ne suka zo sai dai su yashe ku su wuce, ko ina sai da na shiga, da alama mai gidan wanka yake, dan naji motsi a wani daki dana leqa,ke kuma kina nan kina sharar bacci abin ki,"

Aeeshaa kunya dik ta gama lillibe ta, suruka ta shigo mata daki ga shi kayan jikin ta ba wasu masu arziqi bane, kuma da alama ita ko a jikin ta.

Hijabin ta dake ninke a kan sallaya ta dauka ta saka, dogo ne har qasa, sannan ta fara tafiya tana nufin suje waje, amma baiwar Allahn nan ta samu bakin gado ta zauna, ganin haka yasa Aeeshaa durqusawa ta fara gaida ta, a ciki2 ta amsa,Aeeshaa mamaki take wannan ba halin ta bane data sani, ko kuwa dama ta boye ne kamar dan ta da ba kowa ya san asaln halayyar shi ba?

"Bari na hado maki abin sha Mama"

"Ki dafan harda dan farfesu, na dan ci nima, ni da gidan dana a ce wai abin sha kawai za a kawon,"

A zuciyar Aeeshaa dan ta ce zata kawo ruwa ba iya shi take nufi ba, dama dole zata hado da wani abun mana.

Amsawa tayi a ladabce ta wuce d sauri.

"Ke ! Uban wa ya sa kika shigar min daki? Ko wani abun kk so?"

Yana fadan hakan ya jata jikin shi,yana kai hannun shi qirjin ta,tare da matsawa da qarfi, qara ta dan sake saboda zafin data ji, nan da nan ya kai bakin shi cikin nata, yana qoqarin cire mata hijab Mama ta leqo,

"Ihun me nake ji? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, me zan gani? Auuu wato qarar tawa ce kenan, kirana kk na zo naga me kuke yi ko,wayyoo Allah na na shiga uku, wannan abun kunya har ina,"

Khaleefa ido tsilli2, yama rasa me zai ce, ganin Maman shi na neman tara masa maqota ya hau borin kunya yana masifa.

"Ke Mama dama wake zuwa gidan mutane ba sanar wa? Yanzu da na san kina nan zanyi hakan ne? Dan Allah ni ki daina mana kuka tinda ba haramun muka aikata ba,"

Cikin parlour ya qarasa shigewa ya zauna,tare da matse qafar shi, jarabar shi ta motsa iyakar motsawa, gashi ta tashi tazo ba sanarwa,gaskiya shi ba ai masa daidai ba.

Aeeshaa kan ta na qasa idanun ta cike da hawaye,

"Yanzu dan zan zo gidan dana sai na sanar? Kuna nan kuna cin mai kyau kuna shan mai kyau, ina can zaune ni daya,ko zuwa ziyara ta ka daina, mace tafi uwa ko?"

Cikin tsananin bacin rai ya miqe tsaye,

"Dan Allah mama meye haka? Tin rannan kk maganar muna cin dadi, ke wahala kk ci? Ki dube ki ki dube mu mu dake waye yfi kalar cin dadi, meye Baba baya baki? Meye a cikin gidan ki babu? Dan wanda na kawo ma iyalina shine abin magana? To kar ki manta fa bani na aurawa kaina ita ba, Baba General ya aje mana abinci kala2, wanda zamu kao shekara ko sama bamu cinye ba, iyaka ta na kawo na cefanen yau d gobe,komai an sauqaqa min, in kudi ne sai dai ki bama wani, baki son mu zauna lfy ne? In na fadawa Hajja kina zuwa gidannan me kk zaton zata ce? Ko kuma Baba General ko Babana? Mahaifiyar ta tinda akai auren nan ban taba ganin ta zo ba, shi yasa ashe Hajja bata son kowa yazo mana saboda irin wannak,"

Aeeshaa bata saba ganin da yana ma mahaifa irin wannan rashin kunyar ba, dan haka da sauri ta durqusa gaban shi ta kama qafar shi,

"Dan Allah Yah Khaleefa ka daina yi ma Mama irin wadannan kalaman, mahaifiya ba abin wasa bace, Allah na fushi da wanda iyayen shi ke fushi da shi, meye a ciki, dik abinda take so dan Allah ka mata, ku rabu lfy,"

Kauda kai yayi, ya san maganae ta gaskiya ne, amma kun san mutumin mu d girman head.

Janye qafar shi yayi ya wuce yana tsaki da surutai, daki ya shige ya buga qofar d qarfi wajen rufewa, sai da suka rufe idon su.

Aeeshaa kallon ta ta mayar wajen Mama wadda jikin ta yayi mugun sanyi, kamar wadda ruwa ya daka,.ba qaramin kunyata ta Khaleefa yayi ba, ba abinda ya fi damun ta yanzu.in bata lallaba shi ba ya fada ma Hajja ai ta shiga uku, zama tai tayi kalar tausayi.

"Ohhh ni yanzu in yaran nan.ya fada ma Kakannin shi ai na shiga uku,"

Aeeshaa ce ta je ta dora dumamen farfesun naman zabbi data yi ta kasa ci, ta sa a fridge,ta fara daukar mata mata juice ta kai mata kan ya dumama ta kai mata.

"Mama ki kwantar da hankalin ki, na san Yah Khaleefa barazana ce kawai, amma ba zai fada va, ki sha wannan bari na kawo maki farfesun in yayi, ina zuwa,"

Wani kallo ta watsawa Aeeshaan, dan a ganin ta ita ce tajawo danta ya juya mata baya, tinda irin haka bai taba shiga tsakanin ta da dan ba,tsakanin su girmamawa ce, tinda a da yana mata ihsani sosai, amma tinda yayi aure ya rage.

"Dalla rufemin baki, farfesu? To da shi na karya a gidana, ke da uwar ki kun mallaken da ko? Dan ihsanin dayake min ya daina, to bari kiji,in baku janye asire2n da kuke yi wa dana ba matakin da zan dauka akan ku ba qarami bane,yanzu diba, irin dankunnen dake kunnen ki, na tabbata sai da ya saka kudi mai yawa sannan ya sai maki su, ni fa? Irin wannan babbar kyautar bata taba hadani da dana ba, daga zuwan ki kin kankane ko ina,da sakel an bawa mai kaza kai,"
Chapter 20 · 0% Book details