← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 41

Sashe 34

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khaleefa ya san in gudu za ai tini zasu kama shi, takun shi d nasu ba daya bane, wani shago dake kusa ya fada, su John ba uniform.ne ba a jikin su, balle a gane sojoji ke biye da shi,mai shagon ne ya ga an fado masa ba zato ba tsammani, a rikice ya durgusa dan kare kan shi daga koma meye ya zo masa a bazata haka.

"Malam lfy? Zaka shi min waje kamar an jefo ka?"

"Ba gwanda wanda aka jefo ba, ina cikin matsala, wasu yan fashi ne suka biyo ni tin daga wajen gari har nan,rayuwa ta suke so, ka taimaka kayi ceton rai, kar su kama ni,"

"Shigo ta nan, shige ciki, bari na tsaya bakin shagona,dukiya ta nake ji,"

Da jarumta mai shago ya leqa, ya tsaya a bakin shago, ganin su John dik ya zare masa lakar jikin shi, komawa yayi kamar dan tsakon da ruwa ya mai duka, a bakin shagon suka tsaya suna tinanin inda za su gn shi, Auwal ne ya kama John yace,

"Muje kawai mu fada masu gaskiya,"

"Haka za ai,"

Komawar su mota suka sauya shawara, dan gano inda Khaleefa zai fara nufa.

Raba qafa sikai daya ya tafi gidan Khaleefa a adaidaita sahu, daya ya wice gidan Rebecca,suna jiran zuwan shi.

Khaleefa na fita yayi wa mai shago godiya, ya gita yana leqe, gidan Rebecca kuwa ya dau ki hanyar zuwa.

Rebecca na zaune ido ya mata zuru2, sakamakon warning din da ta sha.

"Sugar taimaka min nayi wanka, kiji me ya samen,"

"Wace sugar? Wanne wanka? Kuma a ina? Fitar min a gida ba zaka ja min masifa ba, dik connection danake da shi kafin a kawon dauki sun lahantan jiki, ba zan risking jikina ba kuwa ka fi kowa sanin hakan,so get out,"

"Me kk nufi ne,"

Daya daga cikin dakin ta ne ya bude, already John ya yi ma abokin shi waya ya sanar da shi inda Khaleefa yake, dan haka yana gab d isowa, Khaleefa na ganin John, wani kuka ya xo masa, ya san in ya kama shi kashin shi ya bushe,

"Wai ku nawa aka baku ne kuke azabtar dani haka? Sai kace tsohon barawo,"

"Kudin kula da cin ka da shan ka da kuma na haya da muka kama, sai wanda zamuci abinci, kana da matsala da hakan ne,"

"A'a ba wai matsala nake da ita ba, kun matsa min, kun takurawa rayuwa ta, dan Allah ku barni ko kwana daya nayi anan na harda ku maida ni,ko shekara zan,"

"Ba a bamu wannan umarnin barin ka zuwa gidan karuwai ba,wuce muje,"

"Yana ina?"

Yana qarasa shiga sukai ido hudu da Khaleefa da Auwal, Auwal ya debe shi da mari, sai da ya hantsila, ya qara kifa masa mari, Rebecca sai ihu take, sai da ya masa duka sosai sannan suka kama shi suka maida shi,

"Da ga yau ba zaka sake fita ba ko fitsari kk ji kayi a wajen, kai da sake fita sai dai kashi kashin ma sai mun amince da gaske shi kk ji za a bude ka, in banda abinka a lissafina sauran watanni biyu ka fita, lokacin za a haife maka shegen dan ka, ko 'yar ka, da an kwana biyu a daura maku aure, Ango🤣🤣🤣🤣"

Tinda Khaleefa yake basu taba masa magana har haka ba, balle su yi masa dariya, nan fa suka kafa tsokanar shi, shi dukan da suka masa ba shine ya sashi kuka ba, kiran shi ango da suke ne ya sashi kuka, dariya kuwa haka ya dinga shan ta a wajen su.

Kwana goma sha takwas Khaleefa ya qara a daure a wajen, Hajja ta sa a maida shi gida, a bangaren shi na da, no TV, no laptop, no phone, dik wani abu mai sa nishadi ba shi, daga redio da aka sama kawa kaset na karatun qur'ani ba komai a dakin, tin Khaleefa baya son sauraran karatun har ya fara hakura, watarana sai ya tashi da sha'awa yana son aikata tsiyar tashi ta biyawa kai buqata, sai yaji nauyi d kunyar yin hakan ga qur'ani na playing, haka yake hakura, lokacin sallah na yi Hajja da kan ta take zuwa ta sa shi gaba sai yayi ta, in ya kuskure a wani wajen in ya idar ta gyara masa, Hajja ke kai masa abinci, da dik wani abu daya ke buqata, ko sau daya ta hana shi ganin iyayen shi, ta hana su zuwa ko da da dare ne kuwa, dan da dare Auwal ko John ke zama bakin qofar shi.

Ba qaramin matakan tsaro da na gyara Hajja ta sawa Khaleefa ba, a ganin ta haqqin ta ne ta gyara shi, da ran ta da lfyr ta ba zata bar zuri'ar ta ta lalace ba, sai dai in bata numfashi, in iyayen da mijin ta ba zasu iya ba ita za ta iya, Allah bai tauye ta da komai ba, na lfy, da arziqi, bq zata qi bauta masa, kuma ba zata bari a zuri'ar ta a samu kafur kafur ba.

Khaleefa ya samu nutsuwar zuciya, har ya samu damar roqon Hajja a maida masa Aeeshaa a bar maganar Khaleefa, randa ya yi maganar Aeeshaa sai da ya gwammace uwar shi bata haife shi ba, dan yasha maruka ba su qirguwa, sannan Hajja ta sa John ya nada masa mugun duka, sai da ya dinga shiga ruwan zafi, kiran sunan Aeeshaa ya za masa bala'i da masifa, to ya zai yi da kewar ta da ta ke kama shi, ga son ganin abinda suka haifa dake dawainiya da shi, shi ko sau daya a bashi dama ya sa su a idon shi.

(U dey play with fire Khaleefa)

***********************

Wata shaquwa ce mabayayyaniya a tsakanin Aeeshaa da Umma, Ameena da Abdul, Abdul har baya son zuwa ko ina saboda Ameerah, soyayyar Ameerah ce ta sa ya fara kula Aeeshaa,har yake sakin jiki da ita, daga hirar Ameerah suka koma hira a tsakanin su, yakan fada masa damuwar shi ta bashi shawara akai.

Umma ta dage wajen maida Aeeshaa yar gayu, makarantar da ake koyar da kwalliya da girke2 ta saka ta, kwalliyar zamani Aeeshaa ta maida hankali akai wajen koya sai cakes da snaks data qara gwanancewa, abinci wataran har itama tana taya koyar da shi a wajen, saboda bata da matsala a wannan bangaren.

Tare da Umma yanzu take zuwa sarin kaya, manyan shaguna, musamman shagon Alhaji Shehu Dan Kwarai, dake kantin kwari, shago ne da ake saida kayyaki ko wanne iri kk so, akan farashi mai sauqi, kuma kaya ne masu quality matuqa, kowa yaga Aeeshaa ta saka kaya sai ya sake kallo, gani ake specila order ake mata.

Sun saba sosai da mutanen shagon saboda karamci da karbar mutane cikin girmamawa da sakin fuska.

Watarana Aeeshaa da kan ta take zuwa shagon, dan yanzu ta waye tana iya fita ita daya ba tare da an raka ta ba, sai dai wataran ta kan dauki Ameena saboda ta riqe mata Ameerah.

Yah Sabeer kusan tarewa yayi a gidan, ko da yaushe yana dauke da Ameerah, tayi sabo da shi sosai, dan in zai tafi ma sai ya mata wayo yake guduwa.

Umma tayi2 da shi akan ya sanar da Aeeshaa abinda ke ran shi, ya kasa, Ammar yace in ya wuce yau bai fada ma Aeeshaa abinda ke ran shi ba, shi zai sanar da ita, Sabeer ya yi roqon duniya Ammar ya rantse ya qara.

Dan haka yau ba shi da option din daya wuce ya sanar da ita, manyan kaya ya saka, wanda suka matuqar karbar shi, ga gemun shi daya tara wanda yake shan gyara a koda yaushe, ba mai ganin Sabeer a maza bai sake waige ba, balle mata, qamshi kawai ke tashi a jikin shi, sallama yayi ma su Ammar da Hassana wanda suka zama kamar gam, saboda liquwa ma junan su, Baba General ya ba shi Umarnin ganin ta, iyayen shi sun zo sunyi magana da Baba General din da manyan gidan, sunga Hassana kuma sun yaba da halin ta dana iyalin ta, sun aminta zasu hada zuri'a da su, yanzu suna jiran a masu izini su zo maganar aure.

"Sabeer kayi wa yarinyar nan a hankali, irin wannan gayu haka?"

"Ke dai baki rabo da ja na, da bana gayu kuke nufi?"

"Kana yi amma na yau kai kan ka kasan daban ne,"

Murmushi yayi ya fice, da Hajja ya hadu, zata je wajen Khaleefa, yau ya tashi da surutun wai ana masa abu kamar qaramin yaro, bayan shine babba a gidan, za a sa qannen shi su raina shi.

"Sai ina kuma?"

"Zanje wajen Aeesh...... ammma wajennnn Ummana,"

"Hummm Sabeer kenan, ka gaida min Aeeshaa da Khadeejan da kuma sauran yaran, Allah ya tsare ya bada sa'a,"

Yaji dadin addu'ar ta sosai, dik da yaji kunya yana ganin ta gano shi ma.

Hajja zuciyar ta fari qal, domin tin da ta sa Khaleefa ya saki Aeeshaa burin ta ace Sabeer ya aure ta, amma bata son ta fada dan bata san ya zai dauki abun ba, kar a kuma irin na Khaleefa, so sai ta bada qarfin ta wajen yin addu'a akan lamarin, in alkhairi ne Allah ya hada zuqatan su, in ba alkhairi Allah ya ba su masu alkhairi a rayuwar su.

Aeeshaa na zaune tana bawa Ameerah Nono bacci ya dauke ta, Sabeer ne yayi sallama, ya dade a bakin qofa ba wanda ya amsa, Umma ta tafi wajen kasuwancin ta, yara na makaranta, Ameerah na jin maganar shi ta fara takawa zata fita, tana ta murna.

Sabeer ne ya shiga dan jin Ameerah dake tahowa,yana shiga yayi arba da Aeeshaa dake zaune tana bacci n*** daya a bude, da sauri ya juya yana hadiye yawu, tare da zazzaro ido, bakn qofa ya je ya hau kwankwasawa, bude ido tai a hankali bata ga Ameerah ba, gyara rigar ta tayi, ta fita dan dubawa tare da kwalawa Ameerah kira, dariyar ta taji a waje, ta leqa da gudu2, ganin Sabeer dauke da ita ne yasa ta dafe qirji tana dariya.

Sabeer ba abinda yake hangowa sai hoton ta tana bacci da zu, hakan ya sa masa tsoro da wani irin faduwar gaba, wanda yake jin kamar ba zai iya fada mata ba.............
Chapter 34 · 0% Book details