← Book details Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 41

Sashe 3

Kun Makaro Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Khadeeja ke fa ba zallar bafulatana bace, ki daina tauye mana rayuwar jin dadin mu,"

Takan bashi amsa da,

"Mu fulani ne, dan kuwa kakannina na uwa da uba fulani ne, dole na zama me kunya"

Sun samu albarkar aure, tare da qarin arziqi me yawa. Watarana yana wajen aiki aka wuce da shi asibiti, saboda matsanancin ciwon kai da yake fama da shi, likitoci sun dade suna masa gwaje, dan sai da suka dau kwanaki, suka gano yana dauke da ciwon cancer na bargo, Khadeeja tayi kuka sosai kamar zata mutu, gaba daya kunyar shi da nauyin su Hajja da take ji ranar babu, ga shayarwa tanayi, ga tashin hankalin rashin lafiyar mijin ta, ko abincin kirki bata ci, yarinya bata samun nono sosai, shekarar Ameena daya da yan watanni aka yaye ta, An shirya za ai masa aiki, a qasar India, suna shirin tafiya, Allah ya karbi rayuwar shi.

Tashin hankalin da Khadeeja ta shiga ba zai misaltu ba, sai da ya kai, an kwantar da ita a asibiti, na sati daya da kwana biyu, ta rame ta lalace kwata2 ko kyaun gani bata da shi, har Hajja ta dinga zargin ko wani cikin gare ta.

Bayan arba'in da rasuwar Salihu, Hajja suka yanke hukuncin ta koma gida, aikuwa sunga tashin hankalin da basu taba zatan zata yi ba, kuka ta dingayi, tana sambatun zasu raba ta da gidan mijin ta, mijin ta zai iya dawowa ko wanne lokaci ya ga bata nan, tafiya yayi ba mutuwa ba, da kyar aka lallaba ta, aka bar ta, dan gudun kar ta samu wani ciwon, a hankali2 ta fahimci cewar mijin ta fa ya rasu, ya barsu bari na har abada, dik da ta san hakan tafi son ta zauna nan, daga wannan lokacin halayen ta suka sauya, da Aeeshaa yar gata ce a wajen ta, amma yanzu kwata2 gani take in ta sa ta a rai itama wataran mutuwa zatai ta bar ta, dan haka take janye ta a ran ta da jikin ta,Sabeer shi ya ci gaba da zama da su, bayan rasuwar mijin goggon tashi, nan ya ci gaba da karatun shi kafin daga baya ya tafi qarin ilimi, sun shaqu sosai da Aeeshaa, ba kadan ba.

Suna shiga Khaleefa yana qoqarin fita,

"Lahhhh ga Yah Khaleefa Umma, Yah khaleefa !"

"Malama ki daina cika mana kunne kin san ba kula ki zai ba,"

Murguda baki Ameena tayi, dan ita mai son mutane ce.

Khaleefa ne ya leqo kan shi ta window, ya daga masu hannu, tare da motsa labban shi, babu wanda yasan me yake fada, Sabeer yaji haushin hakan sosai, dik da dama ba wani jituwa suke ba, amma a qalla yayi tafiya, domin zumuncin dake tsakanin su ma ai ya nuna kulawar shi.

Shima yaqen yayi masa ya daga hannu, ya sa kai a da mota, Khaleefa shima ficewa yayi abin shi.

"Wai fa Yah Khaleefa na nufin wannan daga hannun da yaqe haqoran harda ke a gaisuwar,"

"Na sani, muje ciki, matar shi nada aiki matuqa,"

Da murna Sabeer ya yi bangaren mahaifan shi, inda suka taru suna taya shi murnar kammala karatun shi da cikakkiyar nasara, Umman su Aeeshaa bangaren Hajja ta nufa.

Hira suke sosai, Hajja tayi gyaran murya, tare da kiran sunan Umma.

Cikin maida hankali kan mahaifiyar ta ta, ta aje cup din dake hannun ta, ta amsa,

"Khadeeja, na dade ina tattauna wannan maganar a zuciyata, amma bansan ya zaki dauke ta ba, shiyasa ban sanar da kowa ba, ina son muyi maganar dake da farko,"

"Hajja wannan wace magana ce mai mahimmanci haka?"

"Magana ce akan Aeeshaa, ina ganin tinda yanzu tana aji biyar na sakandire, ya kamata a tsayar mata da mijin aure, danni ban yarda da dogon karatun nan na boko ba aure ba, me kk gani?"

Kunya ce ta kama Umma, wai yau tayi girman da ake maganar aurar da diyar ta, ga wani kewar mijin ta daya kama zuciyar ta, kamar daga sama taji sunan da Hajja ta ambata, sannan wai fa shi take jiyo muryar Hajja tana cewa za a hada auren su da Aeeshaan ta...........

*Wadda ta canki sunan wanda za a aurama Aeeshaa zan bata biyay* 😆😆😆😝
💅🏼 *KUN MAKARO* 💅🏼

*BY HAERMEEBRAERH*

Page 3:

"Me kuke tattaunawa ne haka, Tinda na shigo nake jin muryar ki?"

Zama yayi tare da kallon Khadeeja wadda ta bude baki, kamar tana cikin rudani.

"Ina fada ma Nana Khadeeja ra'ayina ne game da maganar da muka tattauna, amma naga kamar hankalin tama baya tare dani,"

Da kyar ta tattaro murmushi ta saka a fuskar ta, ko ba komai Aeeshaa diyar ta ce, kaza na taka dan ta ba dan bata so ba, sai dan ta ladabtar da shi, anya zata iya yin shiru akan wannan hadin da Hajja ke so kuwa?

"Baba barka da yamma,"

"Barka dai 'yar baba, ya abokina da matan nan nawa masu yanga?"

Sunkunyar da kan ta qasa tai sosai, saboda ita din akwai kunya matuqa, amma in ta bangaren kasuwancin tane, ko da qawayen ta ba wannan maganar wai kunya.

"Suna lfy, munzo da su Abdul, Hajja qarama tana gida, kasan ta da aiki, ga son karatu, tace zata zo amma ba yau ba"

(Sannu Umma da gilla qarya😏)

"Allah sarki, gaskiya Aeeshaa tayo halayya irin ta ki uwar gida na, komai na dabi'un ta naki ne, Allah ya qara maku kyakkyawan hali ku yi koyi da Nana Aeeshaa,"

"Ameen,"

Suka amsa, waya Baba General ya dauka, ya hau kiraye2, sai dai kawai suji yana fadin,

"Assalamu alaikum,...... kazo da iyalan ka, ina neman ka......yauwa sai kun shigo,"

Miqewa Umma tayi dan zuwa wanke hannun ta, da tai ciye2,

"Ina zaki? Ai zaman kusan naki ne, dik da naga ba kizo da Aeeshaa ba amma maganar nada mahimmanci wajen Hajjan ku, ya kamata a yi ga yau,"

Wani abu ta hadiya mai daci, dan indai bata bata ji ba, wannan hadin bai mata ba sam.

"Hannu zan wanke kafin su iso,"

"To...to... je ki, ki dan taho min da abin sha,"

Hajja ce ta miqe da sauri tana bawa mijin nata hakurin rashin kawo masa abin sha da batai ba, nuna mata yayi babu komai, tayi zaman ta, ga Khadeeja nan, ai ba sai ta tashi ba.

(Uwar gida wannan ba dalili bane da zai sa miji ya dawo taqamar kina da yara ki make a gefe, qafa daya kan daya, kina kallo kina watsa inibi, da juice, ki sa yara su kaima baban su komai, ke bazaki je ba, in mijin kine ya aminta, saboda baya son wahalar ki, baya son kin gama aiki, ki wahala, ya amince yara sukai masa, kuma kka tabbatar har ranshi ne, shikenan, amma baki da dalili in ba shi ya aminta ba)

Daya bayan daya suka dinga shigowa, Abdul da Ameena kusa da Hajja suka zauna, amma daga baya Baba General yace su shiga ciki suyi wasa, sai da suka qara minti bakwai kafin mai sarauta Khaleefa ya shigo, yana wani babbata rai, ya samu gefe ya zauna shi kadai, da kyar ya bude baki yayi sallama ya gaida su, in badan sun kalli leben shi ba, ba mai gane me yake fada.

"To da farko dai zan yiwa Allah godiya daya bani zuri'a kyakkyawa,mai riqo da addini kamar ku, kuma ina maku godiya akan hadin kan ku da zumun cin ku, musamman kai Abubakar, ka riqe zumunci guda biyu, na farko na 'yan uwantaka, sannan na abokantaka, ka tsaya tsayin daka iyalin Salihu basu koka ba, kuma qanwar ka da take bazawara bata wulaqanta ba, Allah ya saka maka da alkhairi,"

"Ameen,"

Kowa ya amsa, banda mai muqami, (Khaleefa).

"Toh saboda wannan zumunci naku ya qara qarfi, hajja da ni mukai tinani, muka ga tinda Aeeshaa ta kusan kammala Secondaryn ta, me zai hana da ta gama a aurar da ita, tinda a wannan zamanin ba kowacce yarinya bace zaya fara makarantar gaba da Secondary ba ba tare da ta lalata rayuwar ta ba,"

Khaleefa ne ya dan ja guntun tsaki, dan za ayi maganar yarinyar nan me zai sa sai an wani kira su? Kawai dan a hana shi shan iska.

Sabeer kuwa wani farin ciki ne ya lullube shi, musamman da yaji an yabi mahaifin shi, kuma anyi zancen auren Aeeshaa, tabbas addu'ar shi ta shekara da shekaru zata amsu, musamman yau dinnan haka kawai yake sake jin ta sabuwa a zuciyar shi, tin da ya dora ido akan ta yaga yanda ta koma; yaji bai ma kan shi zaben tumun dare ba.

Hassana dake zaune, tana qunquni a ran ta, na ganin ita da ta girmi Aeeshaa nesa ba kusa ba ba wanda ya yi maganar aurar da ita da abin son ta, sai qaramar yarinya kamar Aeeshaa, ita Degree gare ta bangaren Accounting, amma Baba General ya hana ta aiki tace sai sanda tai aure tayi a gidan mijin ta, a yanzu ma bata da samari, ina ga ta fara aiki? Ai gudun ta zasu nayi suce tafi qarfin su.

"Kai Khaleefa nayi2 ka samar ma kan ka macen aure, amma girman kai ya hana ka, na san komai lokaci ne, na so ace na baka dama ka zabi wadda ta yi maka, dan kai auren soyayya irin nawa da kakar ku ka more aure, amma ka tsaya ruwan ido, kamar jira kk a kawo maka mace daga gidan sarkin makka,to mun yanke shawarar aura maka Aeeshaa dik sanda ta kammala makarantar ta,"

Su ukun a tare suka miqe tare sa furta,

"Whattt!!!!"

"Yes, Khaleefa nace zai auri Aeeshaa, meye naku a ciki da kai da ke?"👉👳🏻‍♀🧕🏻

Komawa Sabeer yayi, cikin tsananin takaici, da qunar rai, tare da karyewar zuciya mai tsanani, idon shi ya kada yayi jawur, jijiyoyin kan shi sun firfito.

Hassana kuwa kuka ta saka, amma qasa2, yanda Maman su kawai ke jin ta, sai zungurin ta take da qafa amma bata daina ba.

"Ina sauraron ku, wannan reaction din da kuka nuna min na meye? Baku goyon bayan hukuncin mune ko mi?"
Chapter 3 · 0% Book details